Dakarun Sojoji Sun Toshe Kofofin Tsira ga 'Yan Ta'addan Boko Haram, an Kashe Miyagu
- Dakarun sojojin Najeriya na ci gaba da kara kaimi wajen kai hare-hare kan 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP a jihar Borno
- Jami'an tsaron sun kai wasu hare-hare kan 'yan ta'addan da nufin kakkabe su domin kawo karshen ayyukan ta'addancin da suke yi
- Hare-haren sun yi nasara, inda aka kashe 'yan ta'adda tare da kwato bindigogi da alburusai a hannunsu bayan an gwabza fada
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Dakarun sojoji na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), tare da haɗin gwiwar ’yan CJTF da sauran jami’an tsaro, sun hallaka ’yan ta’addan Boko Haram/ISWAP a jihar Borno.
Dakarun sojojin sun hallaka 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP guda 12, a wasu jerin hare-hare da suka kai a jihar Borno.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun sha wuta hannun sojojin sama, sun sako mutanen da suka sace a Zamfara
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun kai hare-hare kan 'yan Boko Haram
Majiyoyi sun bayyana cewa hare-haren sun gudana ne daga ranar 29 zuwa 30 ga watan Agusta 2025 a kauyuka da dama, ciki har da Tamsu Ngamdu, Dalakaleri, Gaza da kuma Loskori Kura.
A cewar majiyoyin, dakarun sun yi arangama da ’yan ta’addan ne a kauyen Loskori Kura, inda aka samu musayar wuta mai zafi wacce ta kai ga hallaka ’yan ta’adda 12.
"An kwato bindigogin AK-47 guda shida, jigida guda takwas cike da harsasai, tare da wasu nau’o’in magunguna da dama."
"An kuma lura cewa wasu daga cikin ’yan ta’addan suna karɓar magani ne saboda raunukan da suka samu a wani gumurzu da dakarun a ranar da ta gabata."
- Wata majiya
Majiyoyin sun kara da cewa samamen ya raunana karfin yan ta'addan a yankin baki ɗaya, inda ya katse musu damar tafiya da kuma samun kayan agaji.
A ’yan watannin nan, rundunar sojojin Najeriya ta kara kaimi wajen kai hare-haren kasa da na sama a Arewa maso Gabas, musamman a sansanonin ’yan ta’adda dake cikin dajin Sambisa, Tafkin Chadi da kuma tsaunukan Mandara.

Source: Original
Karanta wasu labaran kan sojoji
- An kwashi gawar 'yan bindiga a buhu bayan sojoji sun kashe 'yan ta'adda 50
- 'Yan bindiga sun sha wuta hannun sojojin sama, sun sako mutanen da suka sace a Zamfara
- Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'addan Lakurawa, an kashe miyagu
- 'Yakin ba na sojoji kadai ba ne,' Janar Buratai ya kawo dabarar murkushe 'yan ta'adda
- Dakarun sojoji sun hallaka kwamandojin Boko Haram da 'yan ta'adda 11
Sojoji sun dakile harin 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile harin 'yan bindiga a jihar Zamfara.
Sojojin na rundunar Operation Fansan Yanma sun ragargaji 'yan bindiga bayan sun yi yunkurin farmakarsu a kan titin hanyar Gusau zuwa Tsafe.
Jami'an tsaron sun samu nasarar kwato babura a hannun 'yan ta'addan bayan sun kore su zuwa cikin daji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
