Hatsari Ya Rutsa da Ayarin Mataimakin Kakakin Majalisa, An Rasa Rayukan Yan Uwa
- Ayarin mataimakin kakakin Majalisar Dokokin jihar Abia, Austin Okezie Meregini ya gamu da hatsari a hanyar dawowa daga Fatakwal
- Rahotanni sun nuna cewa motar ayarin ta yi taho da mu gama da motar wasu mutum biyu 'yan uwan juna, duka sun mutu
- An tabbatar da cewa mutane biyu yan gida daya sun dawo ne daga kasahen waje domin yiwa mahaifiyarsu jana'iza kafin faruwar hatsarin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Abia - Mutane biyu sun mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da ayarin motocin Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Abia, Austin Okezie Meregini.
Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya faru ne a kan titin Enugu–Umuahia–Aba–Fatakwal, a yankin Obehia, inda wasu daga cikin hadiman mataimakin kakakin suka jikkata sosai.

Source: Facebook
'Yan gida daya sun mutu a hatsarin

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kutsa cikin gida, sun sace malamin addini kuma ma'aikacin asibiti
The Nation ta ce wadanda suka mutu a wurin hadarin sune Ifeanyi Maduako (45) da kuma Onyedi Obasi (35), ‘yan gida daya da suka fito daga karamar hukumar Ehime Mbano ta jihar Imo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce yan uwan sun zo gida ne domin jana’izar mahaifiyarsu, bayan haka kuma suna shirin komawa kasashen da suke zaune kafin wannan mummunan hadari ya faru.
Wata majiya ta ce:
“Sun dawo ne daga kasashen waje domin yi wa mahaifiyarsu jana’iza. Daya daga Gambia ya dawo, dayan kuma daga kasar Palasdinawa.
"Sun kammala jana’izar kenan, a hanyar komawa wuraren da suke zaune, sai wannan abin bakin ciki ya afku.”
An kara da cewa daya daga cikin mamatan ya bar ɗa guda, yayin da dayan kuma ya bar ‘ya’ya biyu.
Me ya jawo wannan hatsarin mota?
Babu cikakken bayani kan ainihin sanadin hatsarin, sai dai bayanai sun nuna cewa motar ayarin kakakin Majalisar jihar Abia ta yi taho-mu-gama da motar mamatan.
Rahotanni sun cewa gudun da motocin ke yi ya wuce kima, abin da ya haddasa hadarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen biyu yan gida daya.
Dukkanin motocin biyu da abin ya shafa an garzaya da su zuwa ofishin ‘yan sanda na Obehie, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan
Borno: Mayakan boko haram sun yi wa matafiya kwantan bauna, sun bude wa motarsu wuta
Sai dai har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto, Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Abia da kuma Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) ba su fitar da wata sanarwa ba.

Source: Original
Mataimakin kakakin Majalisa ya yi magana
A nasa bangaren, Mataimakin Kakakin Majalisar ya musanta cewa yana cikin ayarin motocin a lokacin da hatsarin ya afku.
Ya bayyana cewa tawagar tasa na kan hanyar dawowa ne daga wani aiki a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas lokacin da hatsarin ya faru.
Hatsarin mota ya kashe mutane 12 a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa an samu asarar rayuka a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kauyen Samawa, karamar hukumar Garun Malam da ke jihar Kano.
Hukumar FRSC ta ce matsala da motar ta samu ya jawo wani bangare na burkinta ya fice, lamarin da ya haddasa mummunan hadarin da ya salwantar da rayukan mutum 12.
A cewarsta, jimillar mutane 19 ne ke cikin motar a lokacin hadarin, inda mutane 12 suka mutu, biyar suka ji rauni, yayin da biyu suka tsira ba tare da rauni ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng