Hausawan da aka Ruguzawa Kasuwa a Legas Sun Fadi Halin da Suka Shiga

Hausawan da aka Ruguzawa Kasuwa a Legas Sun Fadi Halin da Suka Shiga

  • Sake rusa wani ɓangare na kasuwar Alaba Rago a Legas ya jefa dubban ’yan kasuwa cikin halin kunci da rashin mafaka
  • ’Yan kasuwa sun ce an rushe shaguna fiye da 3,000 da masallatai 40 tare da asarar da ta haura Naira biliyan 20.
  • Sun zargi gwamnatin Legas da karya alkawuran da ta yi musu a lokacin zaɓe da kuma rusa musu kasuwa ba bisa doka ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Kasuwar Alaba Rago da aka kafa tun a 1970,ta shahara wajen harkar abinci, dabbobi da karafa a unguwar Ojo, jihar Legas.

Ita ce kasuwar da aka sani da “kasuwar da ba ta barci” saboda yawan harkokin kasuwanci da ke gudana kullum.

Wani yanki na kasuwar Alaba Rago da aka rusa
Wani yanki na kasuwar Alaba Rago da aka rusa. Hoto: Imrana Muhammad
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa a ranar Asabar, 16 ga watan Agusta, 2025, jami’an gwamnatin jihar Legas sun sake mamaye kasuwar tare da rushe manyan sassanta.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari Kano da dare, sun sace mata bayan kashe rai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin da ya ci gaba har zuwa Laraba, 20 ga watan Agusta wanda ya bar dubban ’yan kasuwa cikin kunci da halin rayuwa marar tabbas.

Tarihin kafa kasuwar Alaba Rago

Tsohon ɗan kasuwa da ya fara kasuwanci a wurin tun daga shekarar 1979, Alhaji Hamidu Musa ya ce lokacin da aka ba su wurin, daji ne kawai ba tare da wani cigaba ba.

Ya ce:

“Mun tarar da macizai da namun daji amma muka yi ƙoƙarin gina kasuwa. Abin da muka kafa cikin shekaru 50, gwamnati ta rusa a cikin sa’o’i kaɗan.”

A cewarsa, shaguna uku da ya ke da su a kasuwar, wanda ke amfani da su wajen kula da kansa da ’ya’yansa 16, duk sun salwanta su a rusau din.

Koken Hausawa a kasuwar Legas

Wani mai sayar da hatsi, Alhaji Muhammed Rabiu ya jaddada cewa an ba su kasuwar bisa doka, kuma suna biyan haraji ga gwamnati.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Yadda N8,000 ta jawo asarar rai a kasuwar Legas

Ya ce:

“Shekaru 50 kenan ba tare da gwamnati ta taɓa gina mana ko da ɗaki guda ba, sai yanzu da ta rusa mana komai cikin rana ɗaya,”

Wani ɗan kasuwa, Alhaji Mohammed, ya ce duk da cewa gwamnati ta ba su sanarwar rushewa na watanni shida, amma sai ga shi an zo cikin kasa da wata ɗaya.

Ya bayyana cewa:

“Sun rusa shaguna, masallatai, majami’u da ofisoshi, sun bar mu a waje muna yin kasuwanci a fili,”
Gwamnan jihar Legas na magana a wajen wani taro
Gwamnan jihar Legas na magana a wajen wani taro. Hoto: Lagos State Governor
Source: Twitter

Halin da ake ciki bayan rusa kasuwar

Rahoton ya nuna cewa yanzu haka ’yan kasuwa suna gudanar da kasuwanci a fili a kan gine ginen da suka rushe.

Alhaji Ibrahim, wanda ya shafe shekaru 45 a kasuwar, ya ce sama da shaguna 3,000 da masallatai 40 aka rusa, abin da ya jawo asarar da ba za a iya misaltawa ba.

Nura Dan Marayan Zaki ya kara da cewa jami’an tsaro sun shigo da bindigogi da borkonon tsohuwa yayin rusau din, lamarin da ya haddasa firgici da asarar kaya.

Kara karanta wannan

Katsina: Za a rika ba limamai, masu sharar masallatan Izala da Darika kudin wata

Haka kuma wata mata mai sayar da doya, Hajiya Asema, ta ce shekaru 28 kenan tana kasuwanci a wurin, inda take ciyar da ’ya’yanta da biyan kudin makarantarsu.

Legas: Kwankwaso ya gana da Hausawa

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da 'yan kasuwar Alaba Rago da aka yi wa rusau.

Hakan na zuwa ne bayan mutanen Arewa sun yi korafi game da rusa kasuwar da suka ce ya jawo musu hasara sosai.

Rahotanni sun nuna cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi alkawarin cewa zai yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin an samu mafita.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng