‘Na Shirya Rungumar Zaman Lafiya’: Bello Turji Ya Dauki Alkawari, Ya Fadi Sharrin da Ake Yi Masa

‘Na Shirya Rungumar Zaman Lafiya’: Bello Turji Ya Dauki Alkawari, Ya Fadi Sharrin da Ake Yi Masa

  • Bello Turji ya yi magana kan rashin tsaro da cewa ta’addanci na ci gaba da faruwa a Arewacin Najeriya, ya ce zaman lafiya yana da muhimmanci fiye da komai
  • A cikin hirarsa, Turji ya ce ba shi ne matsalar ba, amma idan aka nemi sulhu da shi, zai dakatar da hare-hare da aka yi
  • Turji ya nemi gwamnati ta tabbatar da adalci ga kowa, yana mai cewa zubar da jini ba ya taimakawa wajen kawo zaman lafiya a Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Shinkafi, Zamfara - Shahararren dan ta'adda, Bello Turji ya yi magana kan ta'addanci da ke ci gaba da faruwa a yankin Arewacin Najeriya.

'Dan ta'addan ya ce abin takaici ne yadda ake wasa da rayukan mutane, ya ce zaman lafiya ya fi komai a rayuwa.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Ɗan Najeriya ya maka gwamna sukutum a kotu, ya faɗi ƙuncin da ya jefa shi

Bello Turji ya yi magana kan sulhu da gwamnati
Dan ta'adda Bello Turji da hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

Turji ya magantu kan sulhu da gwamnati

Bello Turji ya bayyana haka ne yayin hira da jaridar DCL Hausa a yau Asabar 30 ga watan Agustan 2025 wanda ta wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin hirar, Bello Turji ya ce ko kadan ba shi ne matsalar ba amma idan yana nan zai iya dakatar da wasu game da hari idan ana maganar sulhu.

“Yanzu da ake ganin kamar ni ne na zama wa mutane karfen kafa, ba su san ko sun kashe akwai wasu da za su taso ba.
“Akwai turuza 30 da za su taso, yanzu akwai turuza 40 duk in na yi musu magana kuma za su saurare ni amma idan ba ni sai an bi su daidai.
“Ba mu da wata kasa da za mu kafa ko kungiyar addini, idan za a yi wa Fulani adalci wadanda ake kashe wa a Zamfara bai kamata ma mutum ya fito ya ce ba a cuci Fulanin Zamfara ba.

Kara karanta wannan

Yayin da Assadus Sunnah ke kiran sulhu, Hatsabibin ɗan bindiga ya kuma sakin mutane 142

Turji ya ce a shirye yake domin yin sulhu
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Turji ya koka kan sharrin da ake masa

A maganar ajiye makamai, Turji ya ce ba wai suna wannan rigima ba ne don addini ko kuma kokarin kafa wata kasa inda ya ce suna maraba da zaman lafiya.

Ya kara da cewa:

“Mu na neman zaman lafiya idan Allah ya sa saboda zaman lafiya shi ne komai, zubar da jini da ake yi duka mu yan Najeriya ne ba da sunan addini da kafa wata kasa ba mu ke yi ba.
“Idan gwamnati za ta yi wa kowa adalci, amma tsare-tsarensu ne yake da wahala ana tufka ana warwarewa, ba mu gane abin da suke nufi ba.
“Babu wani sulhu da wani zai ce ya yi da ni da gwamnati, misali a Shinkafi na ke, amma rashin fahimta na dan Najeriya sai a kashe mutum a Anka sai ace Bello Turji.“

'Dan sa-kai ya kalubalanci Bello Turji

Kun ji cewa wani ɗan sa-kai ya fito a bidiyo yana kalubalantar fitaccen ɗan ta’adda da ya addabi Arewa maso Yamma, watau Bello Turji.

Kara karanta wannan

'Allah cire ni a gadon sarauta': Sarki a Najeriya ya ƙaryata zargin yana shan wiwi

Matashin ya bayyana cewa idan gwamnati ta ba shi goyon baya, zai iya kamo Bello Turji cikin awanni 12 kacal.

Ya zargi Bello Turji da samun taimako daga wasu 'yan ta'adda, wanda ke kara masa karfi, amma ya ce jami’an tsaro sun fi ƙarfinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.