Siyasar Sanatan APC da Ministan Tinubu na Fuskantar Matsala, an Bukaci Su Ja Baya
- Wata ƙungiyar matasa mai suna 'Youth for Kebbi Renewal Project' za ta razana Sanata Adamu Aleiro da Atiku Bagudu game da zaben 2027
- Ƙungiyar ta ce manyan siyasar sun yi aiki tsawon shekaru amma har yanzu jama’ar Kebbi ta Tsakiya na fama da rashin ci gaban da ake bukata
- Ta roƙi Aleiro da Bagudu su zama masu ba da shawara, su miƙa tutar jagoranci ga sababbin matasa domin sake fasalin siyasar jihar ta Kebbi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ƙungiyar 'Youth for Kebbi Renewal Project' ta taso Sanata Adamu Aleiro da Atiku Bagudu a gaba kan zaben 2027.
Kungiyar ta roki manyan yan siyasar su janye daga takarar majalisar dattawa ta 2027 domin ba wasu dama su jarraba sa'arsu.

Source: Twitter
An bukaci Bagudu, Aliero su ja da baya
Shugaban ƙungiyar, Auwal Ahmed Isah, cikin wata sanarwa a Alhamis 28 ga watan Agustan 2025, kamar yadda Daily Nigerin ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Auwal Ahmed Isah ya ce wannan kira ya fito ne bayan tattaunawa ta natsuwa da kuma muryar jama’a.
Ya bayyana cewa, wannan kira ba raini ba ne amma tsari ne da ya fito daga tunani domin ganin an kawo gyara a siyasar jihar Kebbi.
Sanarwar ta ce:
"Sanata Adamu Aliero ya mulki jihar a kusan kowane mataki, tsohon gwamna ne kuma tsohon minista yayin da yanzu yake rike da mukamin Sanata a karo na uku.
Haka kuma Bagudu ba shi da wani bambanci, daga mulki a matsayin gwamna zuwa Sanata yanzu kuma ministan kasafi da tsare-tsare."

Source: Facebook
Kebbi: An bukaci sauyin siyasa da ba matasa dama
Ƙungiyar ta jaddada cewa shekaru da dama a mulki ya kamata su koma jagorancin matasa, ba wai mamaye mulki na dindindin ba.
Ta ce mamaye mulki kullum na hana sababbin ra’ayoyi da samar yanayi na fifita gata fiye da ainihin hidimar jama’a a siyasa.
Duk da gogewa da dattawan suka samu, ta ce Kebbi ta Tsakiya na fama da rashin ci gaba a ilimi, lafiya da ayyukan samar da ruwa da aikin yi.
Kungiyar ta yi nuni da cewa babu wani gagarumin aikin majalisa da ya bambanta tasirin wa’adin da ya gabata da wanda ya biyo bayansa.
Ta kara da cewa yanzu ne sabon gwamna, Dr. Nasiru Idris Kauran Gwandu, ke fara kawo sauyi a matsayin jagora ga jama’a, sun ƙara da cewa siyasa ba gado ba ne.
Ƙungiyar ta jaddada cewa dimokuraɗiyya na dorewa idan aka sabunta shugabanci, aka ba matsa dama, ba ta hanyar maimaita tsofaffin shugabanni ba.
Ta ce Najeriya ƙasa ce mai matasa da suka fi kashi 70 amma har yanzu tsofaffin ‘yan siyasa na ci gaba da zama a gadon mulki.
Badugu ya fadi yawan albashinsa na minista
Kun ji cewa yayin da 'yan Najeriya ke yawan korafi kan albashi da alawus na mukarraban gwamnati, Minista ya fayyace gaskiya.
Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya bayyana cewa kwata-kwata albashinsa bai kai ko miliyan daya ba.
Yayin da ya yake maganar alawus, Bagudu ya ce bai san wani takamaimai alawus da Minista ke samu ba ban da albashi.
Asali: Legit.ng

