Malaman Musulunci da Kirista Sun 'Karyata' Ikirarin da Tinubu Ya Yi a Kasar Brazil

Malaman Musulunci da Kirista Sun 'Karyata' Ikirarin da Tinubu Ya Yi a Kasar Brazil

  • Shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gyare-gyaren gwamnatinsa sun kawar da rashawa a Najeriya
  • Malaman addini sun karyata ikirarin, suna cewa rashawa ta tsananta a gwamnati da sauran bangarori
  • Sun yi kira da gwamnati ta dauki matakan gaskiya wajen yaki da cin hanci maimakon amfani da kalaman siyasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Maganar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a kasar Brazil cewa gwamnatinsa ta kawar da cin hanci da rashawa a Najeriya ta jawo ce-ce-ku-ce a cikin gida.

A cewar shugaban, an tsaftace tsarin tattalin arzikin kasa, an bude hanyoyin zuba jari, tare da tabbatar da gaskiya.

Wasu malaman addini da shugaba Bola Tinubu
Wasu malaman addini da shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga|MURIC|Philip Hayab John
Source: Facebook

Sai dai shugabannin addinai daga sassa daban-daban na Najeriya sun yi watsi da wannan magana a wata hira da suka yi da jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi gaskiyar abin da ke kai shi kasashen waje bayan dawowa daga Brazil

Martanin malaman addini ga Tinubu

1. “Babu sauyi a harkar cin hanci” Opelema

Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a jihar Bayelsa, Joseph Opelema, ya ce babu wani sauyi da aka samu a fannin cin hanci a kasar.

Ya bayyana cewa kowane sashe na rayuwar kasa na ci gaba da nuna hujjojin cin hanci, inda ya nuna misali da jami’an tsaro da ke karbar rashawa a bainar jama’a.

2. “Maganar siyasa ce kawai,” Sheikh Bello

Sheikh AbdulGaniy Bello daga Ikorodu ya bayyana cewa ikirarin shugaban kasa kalma ce ta siyasa, wadda ba ta da alaka da gaskiyar da ake fuskanta a kasa.

A cewarsa, shugaban na sane da yadda cin hanci ya yi tsanani, amma ya yi wannan bayani ne domin jan hankalin masu saka jari daga Brazil.

3. “Ikrarinsa ma ya nuna matsalar,” John

Rabaran Effiong John daga jihar Akwa Ibom ya ce ikirarin shugaban kasa cewa Najeriya ta kawar da cin hanci shi kansa hujjar cin hanci ne.

Kara karanta wannan

Kudin fansa: 'Yan bindiga sun dauke mutum 4700, an ji biliyoyin da aka rasa a shekara 1

Ya nuna misali da ministoci da aka zarga suna karkatar da kudin gwamnati da kuma jami’an ‘yan sanda da aka gano suna rabon kudin da suka kwashi daga hanya.

4. “Akwai matsala a mukarrabasa,” Hayab

Shugaban CAN na Arewa da FCT, John Hayab, ya ce ko da yake kudin shiga sun karu bayan cire tallafin man fetur, babu wata hujja cewa ana amfani da su cikin gaskiya.

Fasto Hayab ya bayyana cewa cin hanci har yanzu yana nan ko a cikin mukarraban shugaban kasa.

5. “Cin hanci ya mamaye ko ina,” Akintola

Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya ce cin hanci ya zarce bangaren 'yan siyasa ya shiga rayuwar yau da kullum.

Ya kawo misali da malamai makaranta da ke karbar rashawa, da masu sana’a da ke yaudarar abokan hulda.

Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola
Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola. Hoto. Muslim Right Concern
Source: Facebook

6. "Ikrarinsa ba gaskiya ba ne,” Udu-Etim

Rabaran Olu Martins daga jihar Edo ya ce kalaman shugaban kasa sun yi nisa da magana ta gaskiya.

Hakazalika, Bishof Paul Udu-Etim daga jihar Cross River ya ce ba a taba ganin cin hanci ya tsananta irin na wannan lokacin ba, musamman a bangaren shari’a da ‘yan sanda.

Kara karanta wannan

Gwamna ya kara albashi, wasu ma'aikata za su samu rabin miliyan a wata

7. Manufar jan hankalin ne” – Sheikh Uthman

Sheikh Rasaq Uthman, babban limamin Ansar-ud-Deen na reshen Ipaja, ya ce manufar shugaban kasa ita ce jan hankalin masu saka jari.

Sai dai ya bayyana cewa hakan bai shafe gaskiyar da ‘yan kasa ke fuskanta ba, inda ya yi kira da a dauki matakai masu tsauri wajen yaki da cin hanci.

Legit ta tattauna da malamin musulunci

Wani malamin makaranta, Hamza Adamu ya bayyanawa Legit cewa har yanzu akwai cin hanci da rashawa da sauran badakala a Najeriya.

"Sai dai ma a ce rashawa ta karu, ana sayar da ayyuka, ana rashin adalci da dukkan abubuwan da ba su kamata ba.

Dalilin zuwan shugaba Tinubu Brazil

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dalilin da ke sanya shi zauwa kasashen waje.

Bola Tinubu ya bayyana cewa yana tafiye tafiye zuwa kasashe ne domin dawo da martabar kasar a idon duniya.

Shugaban ya tabbatar da cewa tun a shekarar 2023 da aka zabe shi aka daura masa nauyin dawo da martabar Najeriya kuma ya dukufa da aikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng