Karfin Hali: Ɗan Najeriya Ya Maka Gwamna Sukutum a Kotu, Ya Faɗi Ƙuncin da Ya Jefa Shi

Karfin Hali: Ɗan Najeriya Ya Maka Gwamna Sukutum a Kotu, Ya Faɗi Ƙuncin da Ya Jefa Shi

  • Wani bawan Allah 'dan Najeriya ya nuna karfin hali bayan maka gwamna a kotu wanda ya jawo maganganu a kafofin sadarwa
  • Lauya Festus Ogun ya shigar da kara kan Gwamna Babajide Sanwo-Olu saboda ya toshe shi a manhajar X da aka fi sani da Twitter
  • Ogun ya ce ya sha wahala saboda matakin, amma bai nemi diyyar kudi ba domin ka da a dauke shi a matsayin mai neman riba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Wani fitaccen lauya kuma mai tsokaci a harkokin jama’a ya maka gwamna guda a kotu.

Festus Ogun, ya shigar da kara kan Gwamnan Lagos, Babajide Sanwo-Olu saboda ya toshe shi a manhajar X wanda bai yi masa dadi ba.

Lauya ya maka gwamnan Lagos a kotu
Gwamna Babajide Sanwo-Olu da lauya, Festus Ogun. Hoto: Festus Ogun/Sanwo-Olu.
Source: Twitter

Menene dalilin maka gwamna a kotu?

Ogun ya sanar da daukar matakin shari’ar a ranar 29 ga watan Agustan 2025 ta shafinsa na X, abin da ya jawo ce-ce-ku-ce a yanar gizo.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Babbar mota ta murkushe Musulmi yana sauri zuwa masallacin Juma'a, an yi rikici

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin rubutun da ya yi a X, Ogun ya ce:

“Na shigar da kara kan Sanwo-Olu saboda toshe ni a X, na roki kotu ta tilasta ya bude ni daga toshewar da ya yi.”

Ya kara da cewa ya sha wahala sosai saboda lamarin, amma bai bukaci diyyar kudi ba domin ka da a dauke shi mai neman riba.

Wasu na ganin matakin nasa ya yi daidai saboda kare ’yanci, yayin da wasu ke tambayar muhimmancin irin wannan kara a kotu.

Wace bukata lauyan ya nema daga kotu?

A cikin karar, Ogun ya nemi kotu ta tilasta gwamnan ya bude shi sannan ya rubuta takardar neman afuwa a bainar jama’a.

Ya bayyana cewa toshe shi daga ganin sakonnin gwamna a dandalin jama’a ya tauye masa hakkin shiga tattaunawa da sa ido kan gwamnati.

Wannan shari’ar na daga cikin sababbin rikice-rikicen doka da suka shafi amfani da kafafen sada zumunta tsakanin manyan mutane da al’umma a duniya.

Kara karanta wannan

Borno: Mayakan boko haram sun yi wa matafiya kwantan bauna, sun bude wa motarsu wuta

Kotunan Najeriya ba su da tabbacin matakai a irin wannan shari’a, amma wannan karar na iya gwada iyakar ’yanci irin haka a kundin tsarin mulki.

An maka Gwamna Sanwo-Olu a kotu
Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu. Hoto: Babajide Sanwo-Olu.
Source: UGC

Wane martani Gwamna Sanwo-Olu ya yi?

Har yanzu Gwamna Sanwo-Olu bai fitar da wata sanarwa kai tsaye kan shigar da karar da Ogun ya yi kansa ba.

Sanwo-Olu shi ne gwamnan jihar na 15, an haife shi a 1965, kuma ya kammala digiri da digiri na biyu (MBA) daga jami’ar Lagos.

A baya-bayan nan, gwamnan ya bai wa dalibar LASU mai suna Isioma Sybil Nwosu kyautar Naira miliyan 10 bayan ta kammala da digiri sakamako mafi kyau.

Toshe mutum a dandalin X

Abin da ake zargin gwamnan ya yi na toshe wannan mutumi ba zai hana shi ganin bayanansa a X ba, sai dai ba zai samu damar ba shi amsa ba.

A baya idan aka toshe mutum a dandalin X, bai da damar ganin abin da ake yi a shafin. Legit Hausa ta fahimci cewa Elon Musk ya canza wannan.

Matashi ya yi barazanar kashe gwamnan Osun

Kara karanta wannan

Katsina: Za a rika ba limamai, masu sharar masallatan Izala da Darika kudin wata

Kun ji cewa an gurfanar da Rasaq Gafar a kotun Iyaganku bisa zargin barazanar kashe Gwamnan Osun, Ademola Adeleke.

Lauyan gwamnati ya ce Gafar ya aikata laifin ne a ranar 12 ga Yulin 2025, wanda ya sabawa dokar Oyo ta 2000 sashi 249(D) da 323.

Kotun ta bayar da belin Gafar kan N2.5m, amma saboda bai iya cika sharudda ba, aka tura shi gidan yari zuwa watan Nuwamba, 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.