A Karo na 3, Jirgi Ya Gamu da Hatsari Mai Muni a Jihar Sokoto, Mutane da Dama Sun Mutu
- Ana fargabar mutane da yawa sun mutu da wani jirgin ruwa ya kife a yankin karamar hukumar Shagari ta jihar Sakkwato
- Gwamnatin jihar Sakkwato ta tabbatar da aukuwar lamarin, tana mai cewa wannan ne hatsari na uku mai muni da ya auku cikin wata guda
- Bayanai sun nuna cewa jirgin na dauke da maza, mata da yara lokacin da ya nutse, har yanzu ana ci gaba da kokarin ceto mutane
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto - Jihar Sokoto ta sake shiga cikin jimami bayan an sake samun hatsarin jirgin ruwa karo na uku a wata daya, yau ranar Alhamis a ƙaramar hukumar Shagari.
Rahotanni sun tabbatar da cewa jirgin ruwan, wanda ke cike da fasinjoji har ya wuce kima, ya nutse a ruwa lamarin da ya jawo asarar rayuka da kuma bacewar wasu.

Kara karanta wannan
An gudu ba a tsira ba': Sarki ya faɗi yadda mutane 13 suka mutu a kogi a tsarewa yan bindiga

Source: Original
Mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara kan hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA), Aminu Liman Bodinga, ya tabbatar da faruwar hatsarin, rahoton Daily Trust.
Gwamnatin Sakkwato ta tabbatar da hatsarin
Hadimin gwamnan ya bayyana shi a matsayin mummunan hatsari na uku da ya faru a jihar Sakkwato cikin wata guda kacal.
Bodinga ya ce SEMA tare da haɗin gwiwar hukumar agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) da hukumar kula da hanyoyin ruwa ta ƙasa (NIWA) sun tura jami’an ceto zuwa wurin domin tsamo wadanda lamarin ya rutsa da su.
“Har yanzu ana ci gaba da ciro waɗanda suka tsira, haka kuma ana kara gano gawarwakin wadanda suka rasa ransu," in ji shi.
Yadda jirgin ruwan ya debo mutane a Sokoto
Wasu shaidu sun ce jirgin da ya yi hatsarin ya dauko maza, mata da yara fiye da ƙima kafin kifewarsa a tsakiyar ruwa, cewar rahoton Channels tv.
Wasu daga cikinsu da suka iya ruwa sun yi iyo zuwa bakin gaba, amma sauran ba a san inda suka shiga ba, kuma akwai fargabar cewa yawan mutanen da suka mutu zai ƙaru.
Shugabannin da masana sun sha gargadi cewa irin waɗannan haɗurran na faruwa ne saboda rashin bin ƙa’idojin tsaro, ciki har da rashin amfani da rigar ruwa.

Source: Getty Images
Wane mataki gwamnatin Sakkwato ta dauka?
Sai dai duk da yawan maimaituwar irin waɗannan hadurra, gwamnati ba ta dauki wani mataki ba wajen shawo kan matsalar ko ƙara tsaurara doka.
Mutanen ƙauyukan da ke zaune a bakin koguna, waɗanda hanyoyin ruwa su ne tushen rayuwarsu ta yau da kullum, na rayuwa cikin fargaba da bakin ciki.
A halin yanzu dai al'ummar ƙaramar hukumar Shagari da garuruwan makwabta na jiran labarin samun ’yan uwansu da suka ɓace a ruwa sakamakon hatsarin.
Wani dan Sakkwato, Babangida Musa ya yi kira ga mahukunta da su dauki tsauraran matakai don dakile karuwar hadurran jiragen ruwa.
Matashin ya koka kan rayukan da ake rasawa a hadurran jiragen ruwa yayin da yake zantawa da wakilin Legit Hausa, ya ce akwai garuruwan da zirga-zirga ta ruwa ya zama dole.
"Muna da ruwa a nan, ya kamata gwamnati ta matsawa mutane su rika bin doka tun da akwai yankunan da dole sai ka bi ta cikin kogi.
"Maganar gaskiya laifinmu ya fi yawa, ana cikawa wadannan jiragen lodi, ba abin dokar sa rigar kariya da sauran dokoki, ya kamata mu gyara sai Allah ya tsare mu," in ji shi.
Hatsarin jirgi ya rutsa da manoma a Borno
A baya, kun ji cewa mutane da dama sun mutu a yayin da jirgin ruwa da ya dauko manoma akalla 20 ya gamu da hatsari a jihar Borno ranar Litinin.
An ruwaito cewa manoma sun hau jirgin ne domin ketare ruwa zuwa gonakinsa amma taaitsayi ya rutsa da su, jami'ai sun yi nasarar ceto mutum 17 a raye.
Wannan lamari na zuwa ne yayin da wasu rahotanni ke nuna cewa ambliyar ruwa ta yi barna sosai a wasu sassan jihar Borno da ke Arewa maso Gabas.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

