Bidiyon Gwamna a Arewa Ya Durkusa da Guiwowinsa a gaban Tinubu Ya Jawo Magana
- An yada bidiyon Gwamna Mohammed Umaru Bago ya durƙusa gaban Shugaba Bola Tinubu wanda ya jawo maganganu a kafoffin sadarwa
- Ziyarar Gwamna Bago ta faru ne a Brazil lokacin da Shugaban ke ziyara a kasashen da suka hada da Japan domi kawo ci gaba
- Wasu sun bayyana cewa dangantakar Bago da Tinubu ta fi ta siyasa, suna kallon hakan a matsayin haɗin guiwar tattalin arziki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Brazil - Wasu yan Najeriya sun yi ta ce-ce-ku-ce bayan ganin wani faifan bidiyon Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Niger da Bola Tinubu.
Bidiyon Tinubu da Gwamna Mohammed Umaru Bago ya jawo maganganu bayan ganin gwamnan ya durƙusa gaban shugaban kasa a Brazil.

Source: Twitter
Gwamna Bago ya durkusa a gaban Tinubu
Hakan na cikin wani faifan bidiyon da mai amfani da kafar sadarwa ta X, Zayyan A Sale ya wallafa a manhajar a jiya Alhamis 28 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A bidiyon, an gano gwamnan na Niger ya durƙusawa Shugaba Tinubu domin gaisuwa yayin ziyarar aiki da shugaban kasar ya kai Brazil.
Hakan ya biyo bayan ziyarar aiki na mako biyu da Tinubu ya kai kasashen da suka hada da Japan da kuma Brazil.
Gwamna Bago ya kasance tare da Tinubu a wannan ziyara inda aka kulla yarjejeniya da gwamnatin Brazil da wasu kamfanoni masu zaman kansu.

Source: Twitter
Martanin wasu kan bidiyon Bago da Tinubu
Bidiyon da hotunan gwamnan da shugaban kasar sun bazu a shafukan sada zumunta, inda suka jawo martani daga ‘yan Najeriya da dama.
Mutane da dama sun bayyana cewa Tinubu na gina Najeriya da matasa yayin da wasu ke yabon dangantakar Bago da shugaban.
Femi Peters ya ce:
"Dangantakar Bago da Tinubu ta wuce siyasa, ana haɗin guiwar tattalin arzikin jihar Neja da Legas.
"Legas ta sayi filaye kadada dubu dari biyu a Neja domin noman shinkafa da ake sarrafawa a Imota, Legas."
Fidel Otuyal ya ce:
"Tinubu makarantar shugabanci ce, yana gina matasa don gobe. Bago yana ƙirƙirar dangantakar siyasa ta ƙasa."
Cupher ya ce:
"Ina ganin shi ne shugaban 'NIGER FOODS'. Shi da Bago tamkar 5 da 6 ne da Tinubu, suna da kusanci a harkokin noma."
Michael Akinsuyi ya bayyana:
"Soyayyar gwamna Bago ga Shugaba Tinubu ta daban ce. Na kalli hirarsa inda ya kira Tinubu ubansa."
Oluwaseun Olatunde ya ce:
"Zuciyata na gaya min Bago na iya zama shugaban kasa nan gaba, kamar yadda Tinubu ya fito da Fashola."
Gwamna Bago ya taka rawa a taron APC
Kun ji cewa Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Niger ya taka rawa a taron da aka yi a Minna yana murna da wakar yabo ga Bola Tinubu.
Jam’iyyar APC ta jihar ta ayyana Bola Tinubu a matsayin tilon ɗan takararta a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
'Yan Najeriya sun bayyana damuwa, suna cewa gwamnoni sun fi mayar da hankali kan siyasa fiye da matsalolin rayuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

