Borno: Mayakan Boko Haram Sun Yi wa Matafiya Kwantan Bauna, Sun Bude wa Motarsu Wuta

Borno: Mayakan Boko Haram Sun Yi wa Matafiya Kwantan Bauna, Sun Bude wa Motarsu Wuta

  • Mayakan Boko Haram sun yi wa wata mota kirar bas dirar mikiya a hanyar Maiduguri zuwa Banki da ke jihar Borno
  • Lamarin ya dimauta jama'a, ganin cewa matafiya na tsaka da tafiya a lokacin da mayakan na Boko Haram su ka kai farmaki
  • Rahotanni sun bayyana cewa sojoji sun bazama zuwa yankin domin kai agajin gaggawa ga mutanen da hadarin ya afka masu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Rahotanni sun tabbatar da cewa mayakan Boko Haram sun yi wa wata motar bas dirar mikiya a ranar Alhamis, a kan hanyar Maiduguri zuwa Banki.

Lamarin ya faru ne da misalin 2:30 na rana a kauyen Wudila a jihar Borno, wanda zuwa yanzu aka tabbatar da cewa yankin ya riga ya zama kufai.

Kara karanta wannan

Reno Omokri: Tinubu ya kawo tsaro a Abuja zuwa Kaduna da ke fama da 'yan ta'adda

Boko Haram ta kai hari Borno
Sojojin Najeriya a wani rangadi Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa wata majiyar tsaro ta shaida cewa maharan sun bude wuta a kan motar Toyota Hiace mai lamba ASU-255-XA.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Boko Haram sun kai hari Borno

Rahoton ta bayyana cewa direban motar, Mustapha Adam, mai shekara 50 daga Wajare a Banki, ya ji rauni a bayansa sakamakon harbin 'yan Boko Haram.

Sauran fasinjojin da suka samu rauni sun haɗa da Musa Mohammed, mai shekara 41 daga Taradal Banki, wanda aka harba a hannunsa na hagu.

Sai kuma Mohammed Bukar Gaji, mai shekara 61 daga Wajare, wanda ya karye hannu bayan ya fado daga cikin motar.

Taswirar jihar Borno
Taswirar jihar Borno Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sai kuma Modu Usman, mai shekara 35 daga Amchide a Kamaru, wanda aka harba a wuyansa; da Mohammed Adam, mai shekara 32 daga Bama, wanda ya samu raunuka a ƙirjinsa.

Sojoji sun kai dauki Borno

Sojojin Operation hadin kai sun isa wurin bayan samun kiran gaggawa domin ceto mutanen da abin ya rutsa da su. Sai dai kafin isowarsu, maharan sun tsere daga yankin.

Kara karanta wannan

Yadda gini ya rikito kan maƙwabta a Zariya, an kwashi gawarwaki 4 nan take

Daga bisani, an kwashe duk waɗanda suka jikkata zuwa asibitin FHI 360 da ke Banki yayin da majiyoyi sun tabbatar da cewa uku daga cikinsu an duba su, kuma an sallame su.

Haka zalika, an ƙara tura sojoji domin ƙarfafa tsaro a hanyar Maiduguri–Banki don kare fasinjoji daga hare-haren ’yan ta’adda a nan gaba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa hukumomin tsaro, sun tabbatar da cewa babu wanda ya mutu a harin kuma ba a rasa kaya ko dukiya ba.

Sojoji sun hallaka kwamandojin tsaro

A baya, mun wallafa cewa a ranar Asabar, 23 ga watan Agusta, 2025, rundunar Operation Hadin Kai ta sojojin Najeriya ta samu babbar nasara a jihar Borno a yakinta da Boko Haram.

Rahotanni sun bayyana cewa an hallaka manyan kwamandoji biyu na kungiyar Boko Haram da kuma wasu yan ta’adda 11 yayin da su ke kokarin kai hari a karamar hukumar Gwoza.

Sojojin sun dakile hare-haren ne bayan wani bawan Allah inda har an kwato babura da makamai masu tarin yawa daga hannun ‘yan ta’addan a yunkurin dakile ta'addanci a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng