Abu Ya Girma: Ana Zargin Sanata Ya Yi Barazanar 'Kashe' Gwamnan Kaduna

Abu Ya Girma: Ana Zargin Sanata Ya Yi Barazanar 'Kashe' Gwamnan Kaduna

  • Rundunar yan sanda ta gayyaci Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Lawal Adamu Usman bisa zargin yi wa Gwamna Uba Sani barazana
  • Hakan ya biyo bayan korafin da Gwamna Uba Sani ya shigar gaban yan sanda, yana zargin sanatan da yunkurin tayar da tarzoma a Kaduna
  • Kwamishinan yan sanda ya gayyaci Sanatan wanda aka fi sani da Mista LA domin amsa tambayoyi ranar 1 ga watan Satumba, 2025

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Rigima ta kara kamari tsakanin gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani da Sanatan Kaduna da Tsakiya, Lawal Adamu Usman.

Gwamna Uba Sani ya zargi Sanata Adamu da yi masa barazana ga rayuwa da karya, wadanda yake ganin za su iya tayar da zaune tsaye a jihar Kaduna.

Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani.
Hoton gwamna Kaduna, Malam Uba Sani a fadar gwamnati Hoto: Uba Sani
Source: Twitter

Jaridar Tribune Nigeria ta ce hakan ya sa ‘yan sanda suka gayyaci Sanata Lawal Adamu Usman kan zargin barazanar kisa da ƙarya da Gwamna Uba Sani ya yi masa.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Sanata ya maka gwamnan Kaduna a kotun duniya, yana so a cafke Uba Sani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sanda sun gayyaci Sanata Lawal Adamu

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta aika wasikar gayyata ga Sanatan, inda ta bukaci ya bayyana a hedkwatarta domin amsa tambayoyi kan wadannan zarge-zarge.

Wannan gayyata dai kamar yadda wasikar ta bayyana, ta biyo bayan korafin da Gwamna Uba Sani ya shigar ta hannun ma'aikatar shari'a ta jihar Kaduna.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, ya sanya wa wasikar hannu, bayan samun ƙorafi daga gwamnan a hukumance.

A cewar wasiƙar, ana sa ran Sanata Lawal Adamu zai bayyana a gaban kwamishinan ‘yan sanda a hedkwatar rundunar ranar Litinin, 1 ga Satumba, domin ya yi bayani kan zargin da ake masa.

Gwamna Uba Sani na zargin Sanata da barazana

Gwamna Uba Sani ya zargi sanatan da yin magana marar tushe wacce za ta iya tayar da tarzoma tare da lalata zaman lafiya da tsaron jihar Kaduna, Guardian ta rahoto labarin.

Wani ɓangare na wasiƙar gayyatar ya ce:

Kara karanta wannan

Duniya labari: Tsohon shugaban hukumar Kwastam kuma Sardaunan Adamawa ya rasu

“Game da batun barazanar kisa, ƙarya da kuma zarge-zargen da suka yi illa ga mai girma Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna.
"Wannan na sanar da kai cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta karɓi ƙorafi daga mai girma gwamnan Kaduna, ta hannun ma’aikatar shari’a ta jihar, kan waɗannan laifuffuka da aka lissafo a sama.
"Muna roƙonka da ka bayyana a gaban kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna a ranar Litinin, 1 ga Satumba, domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen. Muna fatan za ka ba da haɗin kai a wannan lamari, mun gode.”
Sanata Lawal Adamu mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya.
Hoton sanatan Kaduna ta Tsakiya, Lawal Adamu Usman a ofishinsa da ke Abuja Hoto: @imrammuhdz
Source: Twitter

Gwamnan Kaduna ya yi sauye-sauye

A baya, mun kawo maku cewa Gwamna Uba Sani ya yi sauye-sauyen wurin aiki tsakanin mambobin Majalisar zartarwa ta jihar Kano domin inganta ayyukan gwamnati.

Sanata Uba Sani ya sauya wa kwamishinan shari’a, Sule Shuaibu (SAN), mukami zuwa kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, yayin da James Kanyip ya zama sabon Antoni Janar na Kaduna.

Gwamnan ya nuna kwarin gwiwa cewa duka mutanen biyu da aka sauya wa wurin aiki za su yi amfani da gogewarsu a ma'aikatun da aka kai su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262