Barau Ya Yi Koyi da Kwankwasiyya, Zai Aurar da Bayin Allah kuma Ya Hada Masu da Jari

Barau Ya Yi Koyi da Kwankwasiyya, Zai Aurar da Bayin Allah kuma Ya Hada Masu da Jari

  • Matasa 440 za su samu gata yayin da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya shirya aurar da su a Kano
  • Sanata Barau Jibrin zai dauki nauyin dukkanin hidimar da za a yi, kama daga kayan daki, sadaki, da kuma jari don dogaro da kai
  • Wani makusancin sanatan, Alhaji Fahad Ogan Boye ya bukaci 'yan Najeriya su dage da yi wa Shugaba Bola Tinubu da Barau addu'a

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, zai dauki nauyin aurar da matasa 440 ’yan asalin Kano daga kananan hukumomi 44 na jihar.

Baya ga daukar nauyin auren daga farko har karshe, Sanata Barau zai ba ma’auratan jari domin su samu abin dogaro da kansu, yayin da suke tare.

Sanata Barau Jibrin zai aurar da matasa 440 a Kano
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin yana jawabi a ziyarar da 'yan siyasar Danbatta suka kai masa a Abuja. Hoto: @barauijibrin
Source: Twitter

Barau Jibril zai aurar da mata 440

Kara karanta wannan

Daga Kudu zuwa Arewa: Yadda matatar Dangote take sauya tattalin arzikin Najeriya

Wannan bayani ya fito ne daga bakin makusancin Sanata Barau, Alhaji Fahad Ogan Boye, wanda aka fi sani da Ogan Boyen Sanata Barau Maliya, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da yake zantawa da 'yan jarida a Kano, Ogan Boye ya ce wannan shiri wani bangare ne na jajircewar Sanata Barau wajen tallafawa talakawa da inganta rayuwarsu.

Ogan Boye ya bayyana cewa za a rika kiran wadanda za su amfana da wannan shirin da suna, ‘Yan Gatan Sanata Barau Maliya.'

A cewar Ogan Boye, shirin auren gatan zai karfafa darajar addinin Musulunci da kuma zaburar da matasa wajen zama masu iya dogaro da kansu.

Ya kara da cewa wannan shiri ba zai tsaya ga jam’iyyar siyasa ko akidar kowa ba, domin duk wani matashi daga kowace karamar hukuma zai iya amfana.

Sanata Barau a matsayin jagora

Ogan Boye ya bayyana Sanata Barau a matsayin gwarzon da ke tsayawa wajen kare darajar Musulunci da tallafawa jama’a, yana mai cewa ya zama haske ga al’ummar Kano da Arewacin Najeriya baki daya.

Ya ce:

“Sanata Barau, wanda ya kasance jigo na dimokuradiyya da jakadan zaman lafiya da hadin kai, ya fito da wannan sabon shiri na daukar nauyin auren fiye da mutane 400 a Kano, inda zai biya komai daga farko har karshe.

Kara karanta wannan

Harin masallaci: Gwamna Radda ya ziyarci kauyen Mantau, ya dauki alkawura

"Bugu da kari, zai ba ma’auratan jari domin dogaro da kansu. Wannan ba karamin abu ba ne daga mataimakin shugaban majalisar dattawa.”
An roki 'yan Najeriya su taya Sanata Barau Jibrin da Shugaba Bola Tinubu da addu'a don samar da shugabanci mai nagarta.
Sanata Barau Jibrin ya samu gagarumar tarba a gangamin karbar 'yan adawa zuwa APC a Kano. Hoto: @barauijibrin
Source: Twitter

'A taya Tinubu, Barau da addu'a' - Ogan Boye

A karshe, Ogan Boye ya yi kira ga al’ummar Kano da sauran ’yan Najeriya da su ci gaba da mara wa Sanata Barau baya, ta hanyar yi masa addu’a.

Ya kuma yi kira da a rika yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu addu’a, yana mai cewa:

“Shugaba na kokari, kuma mun gamsu manufofinsa suna kan hanyar kai Najeriya ga tudun-mun-tsira. Dole mu tallafa wa shugabanninmu da addu’a domin samun zaman lafiya da cigaba a kasa.”

Abba ya ware biliyoyi don auren gata

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Abba Yusuf na Kano ya ware biliyoyin kuɗi domin shirya bikin auren gata ga matasan jihar a 2025.

Kudin da gwamnatin jihar ta ware domin gudanar da bukukuwan auren sun kai Naira biliyan 2.5, kuma za a zakulo matasan daga ƙananan hukumoi 44 na jihar.

Gwamnati ta ce wannan zai ƙarfafa shugabanci, kare haƙƙin bil’adama, da ƙarfafa adalci domin ci gaban al’umma mai dorewa da kuma kyautata rayuwar jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com