Kano: Abdullahi Rogo Ya Maka Jafar Jafar a Kotu saboda Labarin 'Satar Naira Biliyan 6'
- Wata kotu a Kano ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan Jafar Jafar, mawallafin jaridar Daily Nigerian
- Daraktan kula da harkokin gidan Gwamnatin Kano, Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo, ne ya kai ƙarar kan zargin bata masa suna
- Kotu ta umarci ’yan sanda su binciki rahotannin da wannan jarida ta wallafa a ranakun 22 da kuma 25 ga watan Agusta, 2025
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wata babbar kotun majistare a Kano ta ba da umarnin cewa a gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen batanci da ke kan mawallafin Daily Nigerian, Jafar Jafar.
Wannan umarni ya fito daga kotu ta 15 da ke Nomansland, karkashin jagorancin Alkalin kotu, Malam Abdulaziz M. Habib da ke Kano.

Source: Facebook
Wannan na kunshe a cikin sakon Darakta Janar kan yaɗa labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin Gwamnan Kano ya tafi kotu
Da fari, Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo, Daraktan kula da harkokin gidan gwamnatin Kano ne ya kai Ja'afar da wani Audu Umar gaban kotu.
Yana zargin sun ci mutuncinsa da wallafe-wallafen da suka yi, inda ya ce suna ƙoƙarin bata masa suna.
Hon. Rogo ya ce kiransa 'ɓarawon hadimin Gwamna' da su ka yi, ya yi matuƙar taɓa mutuncinsa.
Ya shigar da ƙarar bisa dokar Shari’ar Laifuffuka ta Kano ta shekarar 2019, tare da sashe na 114, 164 da 393 na dokar Penal Code.
Ya nemi a gurfanar da Jafar da Umar bisa wallafe-wallafe na ranakun 22 da 25 ga watan Agusta, 2025.
Rahoton da ya fusata hadimin gwamnan Kano
Ƙarar ta ambaci rahoton da Daily Nigerian ta wallafa a ranar 25 ga Agusta da ke cewa gwamnatin Kano ta kare 'barawon hadiminta.”

Source: Facebook
Haka kuma, wani rahoto da aka wallafa a ranar 22 ga Agusta da taken: “Takardun kotu sun nuna yadda ICPC da EFCC suka gano Naira biliyan 6.5 a hannun Daraktan kula da harkokin gwamnan Kano.
Amma Rogo ya ƙaryata dukkanin rahotannin, inda ya ce an fitar da su da mugun nufi don taɓa mutuncinsa a idon duniya.
Saboda haka, ya shigar da tuhuma guda biyu a kan Jafar Jafar da abokin aikinsa, wadda ta shafi batanci da kuma tayar da hankalin jama’a — laifuffuka da dokar Penal Code ta Kano ta ayyana da hukunci.
Kara ta biyu kan Jafar Jafar a kotun Kano
A gefe guda kuma, an shigar da wata ƙara ta biyu a kotun Kano, inda ake neman diyya kan batancin da ake zargin Daily Nigerian ta aikata wa Abdullahi Rogo.
Mahukunta sun bayyana cewa zarge-zargen da ake ta yadawa kan Daraktan “ƙagaggun labarai ne” da masu adawa da gwamnati ke kirkira domin su lalata martabarsa.
Kotun ta kuma umarci ’yan sanda su binciki Jafar Jafar da yadda ya yi watsi da ƙa’idar aikin jarida ta hanyar kiran wani mutum “ɓarawo” alhali bincike daga hukumomin ICPC da EFCC bai kammala ba.
Bayanai sun fito kan hadimin gwamnan Kano
A baya, kun ji cewa gwamnatin Kano ta ƙaryata zargin cewa hadimin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya wawushe kudi har Naira biliyan 6.5 daga asusun jihar. Ta bayyana cewa duk wasu fitar kudi na gwamnati ana aiwatar da su ne bisa tsarin kasafin kuɗi da dokokin gwamnati kamar yadda doka ta bayar da dama.
Wannan na zuwa a matsayin martani a kan wani rahoto da ke alakanta Daraktan kula da harkokin gidan gwamnatin da ajiye zunzurutun kuɗin a asusun bankinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


