'Dalilin da Ya Sa PDP Ke Son Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Kirista saɓanin APC'

'Dalilin da Ya Sa PDP Ke Son Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Kirista saɓanin APC'

  • Gwamna Bala Mohammed ya ce PDP ta koyi darasi daga kuskuren APC a 2023, inda jam’iyyar ta tsayar da tikitin Musulmi da Musulmi
  • Sanata Bala ya bayyana cewa PDP ta tura tikitin takarar shugaban kasa zuwa Kudancin Najeriya domin tabbatar da samun adalci
  • A cewarsa, hakan zai bai wa jam’iyyar damar hada kan Kiristoci daga Kudu da Musulmi daga Arewa domin samun goyon baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya yi karin haske game da zaben 2027 da matakan da jam'iyyar PDP ta dauka.

Gwamnan ya bayyana cewa jam'iyyar PDP tana son bambanta kanta da kuskuren da APC mai mulki ta yi a zaben 2023.

Gwamna Bala ya fadi dalilin kai tikitin takarar shugaban kasa zuwa Kudu
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi yayin taron siyasa. Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed.
Source: Twitter

Dalilin PDP na kai tikiti Kudancin Najeriya

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana haka ne a daren yau Alhamis 28 ga watan Agustan 2025 yayin hira da Channels TV.

Kara karanta wannan

"PDP na buƙatar ɗan takara Kirista daga Kudu,' Gwamna Bala ya yi magana kan 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin hirar, gwamnan ya bayyana dalilin jam'iyyar na kai tikitin takarar shugaban kasa zuwa Kudancin Najeriya.

Ya ce sun tura tikitin ne don tabbatar da cewa Kirista dan Kudu ne ya zama dan takarar shugaban kasa.

Ya ce:

"Abin da nake son na fada, ba mu fitar da ko kuma zabi wani dan takara da muke son tsayarwa ba a zaben 2027.
"Ya kamata a sani PDP ta kowa ce, kofa a bude take ga kowane dan Kudu domin tsayawa takara.
"Kamar yadda na fada, ba mu son yin kuskure irin na APC, muna son Kirista daga Kudancin Najeriya ya tsaya mana takara.
Gwamna Bala ya fadi dalilin kai tikitin shugaban kasa Kudu
Gwamna Bala Mohammed ya yi magana kan nasarar PDP a 2027. Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed.
Source: Twitter

Jam'iyyar PDP na tsoron sake kuskuren APC

Gwamna Bala Mohammed ya ce abin da suke so shi ne Kirista dan Kudu ya karbi takara domin daukar Musulmi mataimaki daga Arewa.

"Saboda ya jagoranci mafi yawan Kiristoci da suke Kudu domin su zo Arewa a zabi Musulmi don ya zama mataimakinsa."

Kara karanta wannan

Harin masallaci: Gwamna Radda ya ziyarci kauyen Mantau, ya dauki alkawura

- Cewar gwamnan

Ya ce suna gudun yin kuskure irin na jam'iyyar APC a zaben 2023 da ta yi amfani da tikitin Musulmi da Musulmi wanda ya jawo maganganu daga ko ina a fadin kasar.

Ya kara da cewa:

"Saboda gudun yadda APC suka yi a 2023 wanda ya kawo tikitin Musulmi da Musulmi ba tare da duba ra'ayin mutane ba.
Har yanzu ba mu kai wannan mataki ba da ba a rika duba wasu batutuwa a gudanar da lamuran siyasa ba."

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa shi bai da burin sai ya zama mataimakin shugaban kasa saboda babban abin da suka sanya a gaba shi ne nasarar PDP.

'Dalilin fasa takarar shugaban kasa' - Bala Mohammed

Mun ba mu labarin cewa Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi karin haske kan jingine burninsa na yin takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa burinsa na zama shugaban kasa bai kai girman hadin kan Najeriya ba da ci gabanta.

Gwamnan ya nuna cewa yana goyon bayan matakin jam'iyyar PDP na kai tikitin takarar shugaban kasa zuwa yankin Kudu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.