"Akwai Maza a gabanka," Ɗan Bijilanti Ya Fadi Dalilin da Ya sa Bello Turji Ya Gagari Hukuma

"Akwai Maza a gabanka," Ɗan Bijilanti Ya Fadi Dalilin da Ya sa Bello Turji Ya Gagari Hukuma

  • Wani ɗan bijilanti ya fito a bidiyo yana kalubalantar fitaccen ɗan ta’adda da ya addabi Arewa maso Yamma, watau Bello Turji
  • 'Dan bijilantin ya bayyana cewa idan gwamnati ta ba shi goyon baya, zai iya kamo Bello Turji cikin awanni 12 kacal
  • Ya zargi Bello Turji da samun taimako daga wasu 'yan ta'adda, wanda ke kara masa karfi, amma ya ce jami’an tsaro sun fi ƙarfinsa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto – Wani ɗan bijilanti da bai bayyana sunansa ba ya bayyana a wani bidiyo da ya wallafa kalubale ga shahararren ɗan ta’adda, Bello Turji.

Bidiyon mai tsawon minti 1 da dakika 43 ya nuna 'dan bijilantin na yi wa Bello Turji raddi da kalamai masu tsauri.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da fasto bayan an gano sun hada baki don 'sace' matarsa

An samu wani dan bijilanti da ya ce zai iya kara wa da dan bindiga, Bello Turji
Hatsabibin dan bindiga, Bello Turji yana zaune sanye da kayan 'yan sanda, da kuma lokacin da yake tatauna wa da dan jarida. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Dan bijilanti ya ƙalubalanci Belo Turji

Mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya da kuma yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ne ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin jawabansa, dan bijilantin ya yi ikirarin cewa Bello Turji matsoraci ne da ke raɓewa a cikin daji yana gudanar da ayyukan ta'addancinsa.

Ya ce:

"Akwai wani sakarai makaryaci wanda ake kira Bello Turji. Bello Turji, a saboda da kai na birni na koma jeji. Idan ka san kai namiji ne, ni shirye na ke na bayar da rayuwa ta. Bello Turji, ni sai na yi maganinka idan ka isa ka faɗa mani inda ka ke."

Ya ƙara da cewa ba ya jin tsoron Bello Turji kuma idan gwamnati ta ba shi hadin kai, cikin awanni 12 zai iya kamo ɗan ta'addan.

Wani dan bijilanti ya ce zai iya kamo Bello Turji a cikin sa'o'i 24 kacal
Wasu gungun 'yan bijilanti yayin da suka fito bakin aiki. Hoto: @DanKatsina50
Source: Facebook

Zargin ɗan bijilanti a kan Bello Turji

Ɗan bijilantin ya yi ikirarin cewa Bello Turji yana samun taimako daga wasu wajen gudanar da ayyukan ta’addancin sa.

Kara karanta wannan

'Lokaci ya yi da za a dauki mataki,' ACF ta shiga takaicin yadda ake zubar da jinin 'yan Arewa

Ya ce amma a karan kansa, Bello Turji ba shi da wani kataɓus da zai sa ya gagari dan bijilanti ballantana a kai ga sojoji da sauran jami'an tsaro.

A cewar 'dan bijilantin, taimakon da ya ke samu ne babban dalilin da ya sa ya gagara, inda har yake iya cin karensa babu babbaka ba tare da ya shiga hannu ba.

'Dan bijilantin, ya kara da cewa:

"Ka daina cika baki, idan ka isa namiji ka faɗa mani inda ka ke."

Ɗan bijilantin ya kuma kira Bello Turji da “mace” da “matsoraci” wanda bai isa ya shiga birni kai tsaye ba.

Yaran Bello Turji sun yi ta'addanci

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ’yan bindiga masu biyayya ga shahararren shugaban ta’addanci, Bello Turji, sun tafka barna.

An samu rahoton ruwa sun kai hare-hare a kauyuka daban-daban daga ranar Laraba 14 zuwa Juma’a 16 ga watan Agustan 2025.

Munanan hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane da dama ciki har da wani soja da ɗan sa-kai yayin da daruruwan mutane su ka shiga rudani.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng