'Yan Sanda Sun Yi Ram da Fasto a Kudu bayan an Gano Sun Hada Baki don 'Sace Matarsa'

'Yan Sanda Sun Yi Ram da Fasto a Kudu bayan an Gano Sun Hada Baki don 'Sace Matarsa'

  • 'Yan sanda a Ondo sun kama wani fasto da matarsa bisa zargin kitsa labarin cewa an yi garkuwa da su domin kwadayin kudin fansa
  • Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Olushola Ayanlade ya bayyana cewa matar ta ɓoye kanta a ɗaki yayin da mai gidanta ya sanar da labarin 'sace ta'
  • Bayan an gano gaskiya, matar ta amsa laifin, ta kuma bayyana cewa ta yi hakan ne don don ta samu kudin biyan bashin da ya yi mata katutu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoRundunar ‘yan Sandan Jihar Ondo ta kama wata mata mai shekaru 42 da haihuwa, Misis Sanmori Taiwo, tare da mijinta, Fasto Sanmori Joshua mai shekaru 62.

Sun shuga hannu ne bisa zargin kitsa labarin cewa an yi mata garkuwa Sanmori da niyyar karɓar Naira miliyan 10 daga danginta da ke ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

PDP ta koka, ta zargi EFCC da garkame manyan 'ya 'yanta 2 a Kaduna

An kama ma'aurataya a Ondo
Babban sufeton 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa DSP Olushola Ayanlade, Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ne ya bayyana a cikin sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Sanda sun kama Fasto da matarsa

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Taiwo ta ɓoye kanta ne a cikin ɗaki yayin da mijinta ya sanar da danginta cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ita.

Rundunar ta ce:

“Wani daga cikin ‘yan uwanta, Mista Fasegha O. Joseph, ya yi shakkun batun, inda ya rubuta ƙorafi zuwa ga Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Adebowale Lawal, wanda ya umarci Rundunar Sashin Yaƙi da Garkuwa da Mutane (SAKS) ta bibiyi lamarin."

Ya ce jami’an SAKS tare da taimakon ‘yan sandan sashen Enu-owa, sun mamaye gidan ma’auratan, inda aka same ta a cikin gida.

Dalilin ma'auratan na shirga karyar garkuwa

Bayan an yi mata tambayoyi, matar ta amsa cewa ita da mijinta ne suka kitsa lamarin domin samun kuɗin fansa daga ‘yan uwanta na ƙetare.

Kara karanta wannan

'Lokaci ya yi da za a dauki mataki,' ACF ta shiga takaicin yadda ake zubar da jinin 'yan Arewa

Taswirar jihar Ondo
Taswirar jihar Ondo Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rundunar 'yan sandan ta ce:

“Bayan zurfafa bincike a ofishin rundunar, Misis Taiwo ta amsa cewa ita ce ta shirya labarin sace ta domin ta samu kuɗin fansa daga danginta a ƙasashen waje. Ta kuma bayyana cewa dalilinta shi ne ta biya bashin da ya yi mata katutu da wasu bukatun da ke gabanta."

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa ma’auratan na nan a tsare kuma za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.

Ma'aurata sun yi karyar an yi garkuwa da su

A baya, mun wallafa cewa rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke wasu ma’aurata bisa zargin kitsa labarin yin garkuwa da kansu domin karɓar kudin fansa har naira miliyan biyar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana haka, gargadi al’ummar ƙasar da su guji aikata irin wannan mummunan abu tare da tayar da hankula.

Kara karanta wannan

Kano: Jami'an NDLEA sun cafke matashi da tramadol 7,000 daga Legas

Rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa an gano ma’auratan sun tsara wannan makirci ne domin tara Naira miliyan uku don sayenmal gida a Badagry da ke jihar Legas.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng