Yayin da Assadus Sunnah Ke Kiran Sulhu, Hatsabibin Ɗan Bindiga Ya kuma Sakin Mutane 142
- Yayin da ake cigaba da zama domin samun zaman lafiya game da hare-haren yan bindiga, an sako wasu mutane da ke tsare
- Rahotanni daga Zamfara sun tabbatar da cewa hatsabibin dan bindigan ya sake sakin mutane da ya sace akalla guda 142
- An ce an sako mutanen ne ba tare da wani sharadi ba, inda aka dauke su daga kauyuka daban-daban kafin a kai su asibiti
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Alamu na kara bayyana game da zaman sulhu da ake yi a wasu jihohin Arewa a Najeriya.
Malamin addinin musuluncin nan, Musa Yusuf Assadus Sunnah shi ne kan gaba wurin tabbatar da sulhu ya inganta.

Source: Original
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa akalla an saki mutane 142 da ‘yan bindiga suka sace a karamar hukumar Kaura Namoda.

Kara karanta wannan
Kaduna: An ɓarke da murna bayan mutuwar hatsabibin ɗan daba da ya addabi bayin Allah
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ake maganganu kan sulhu da 'yan bindiga
Hakan ya biyo bayan fara tattaunawa da yan bindiga a jihar Zamfara da ya jawo sakin mutanen wadanda suka samu ‘yanci.
Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah shi ke kan gaba don ganin an tattauna da yan bindiga tare da samun zaman lafiya a yankin.
Wasu malamai sun goya masa baya kan wannan aikin alheri daga cikinsu akwai Sheikh Muhammad Adam Albaniy Gombe.
Sai dai wannan aiki da Assadus Sunnah ya dauko ya fi shan suka fiye da yabon da yake samu duba da al'umma da wadannan yan bindiga ke kashewa.

Source: Facebook
'Dan bindiga, Dan Sadiya ya sake mutane 142
An gano cewa an sako mutanen ba tare da wani sharadi ba daga hannun fitaccen dan bindiga Muhammadu Dan Sadiyya a ranar Laraba.
An bayyana cewa an dauke wadanda aka sace daga kauyukan Gidan Gardawa, Kyambarawa, Maguru, Kurya Madaro, Kagara, Yankaba, Madira da Dogon Daji a yankin Kaura Namoda.
“Mutum 142 sun samu ‘yanci a ranar 27 ga watan Agusta da misalin karfe 8:30 na safe."
- Cewar wata majiya
An ce an garzaya da wadanda aka sako zuwa Asibitin Kaura Namoda, inda aka duba lafiyarsu, aka yi musu bayani sannan aka hadasu da iyalansu.
Mene matakin ke nufi a bangaren gwamnati?
Sakin ya kasance wani bangare na dabarun gwamnatin tarayya na amfani da sulhu wajen kawo karshen rikici da tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso Yamma.
Manufar gwamnati ita ce tabbatar da cewa duk wanda aka yi garkuwa da shi daga sassan Najeriya daban-daban ya samu ‘yanci cikin koshin lafiya.
An kara bayyana cewa wannan mataki yana nuna alamar ci gaba wajen tabbatar da zaman lafiya da kawo karshen satar mutane a jihar Zamfara da kewayenta.
'Yan bindiga sun sace mutum 100 a Zamfara
Mun ba ku labarin cewa wasu yan bindiga sun kai hari kauyuka biyu a ƙaramar hukumar Bukkuyum, jihar Zamfara inda suka kashe mutum biyu.
Majiyoyi sun ce aƙalla mutane 100 ciki har da mata da yara aka sace tare da kwashe dabbobi daga kauyukan Gamdum Mallam da Ruwan Rana.
An ce yan bindigar sun rabu kashi biyu, wani ɓangare na yin garkuwa yayin da dayan ya tare hanya yana harbin jama’a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
