Dakarun Sojoji Sun Samu Nasara bayan Fafatawa da 'Yan Bindiga a Zamfara
- Dakarun sojojin Najeriya na ci gaba da kokari wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma a jihar Zamfara
- Sojojin na rundunar Fansan Yamma sun fuskanci hari daga wajen 'yan bindiga yayin da suke tsaka da gudanar da aikin sintiri a jihar Zamfara
- Jami'an tsaron sun nuna bajinta, inda suka dauki dogon lokaci suna artabu da miyagun 'yan bindigan wadanda suka kawo musu farmaki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Fansan Yamma, sun samu nasarar dakile harin 'yan bindiga a jihar Zamfara.
Dakarun sojojin sun samu nasarar fatattakar 'yan bindiga bayan sun kai hari a kan hanyar Tsafe-Funtua da ke jihar Zamfara.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun fafata da 'yan bindiga a Zamfara

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun sha wuta hannun sojojin sama, sun sako mutanen da suka sace a Zamfara
Rahotanni sun nuna cewa arangamar ta faru ne kusan ƙarfe 9:30 na safe a ranar Laraba, 27 ga watan Agusta, lokacin da jam'an sojoji ke sintiri a kusa da Marabar Kyaware.
Jami'an sojojin na cikin gudanar da sintirinsu, sai gungun ’yan bindiga dauke da makamai suka farmake su.
Lamarin ya jawo musayar wuta mai zafi wadda ta ɗauki sama da awa guda ana fafata tsakanin bangororin biyu.
Bayan an dauki lokaci ana artabu, sojojin sun tilastawa ’yan bindigan janyewa, inda ake tunann da dama daga cikinsu sun jikkata da harbin bindiga.
Hakazalika, dakarun sojojin sun kwato babura guda hudu da 'yan bindigan suka gudu suka bar su bayan da aka yi gumurzu mai zafi.
An samu asarar rai sakamakon artabun
Sai dai, wani abin bakin ciki shi ne, harsashi ya samu wani matashi dan gudun hijira mazaunin kauyen Magazu, mai suna Aliyu Muhammad, wanda aka fi sani da Rege, ɗan shekaru 27, a kirjinsa inda ya rasu nan take.
Majiyoyi sun bayyana cewa an mika gawar tasa ga iyalansa domin yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
An gano abin fashewa bayan artabun
Haka kuma, majiyoyi sun bayyana cewa an gano wani abin fashewa a wajen, wanda daga bisani aka tabbatar makamin harba bama-bamai ne na sojoji.

Source: Original
Sashen kula da bam na rundunar 'yan sanda daga Gusau sun yi nasarar tarwatsa shi ba tare da ya jawo wata illa ba.
A halin yanzu, an kara tsaurara sintirin hadin gwiwar jami’an tsaro a kan hanyar Tsafe–Funtua, domin kauce wa sake faruwar irin wannan hari.
Dakarun sojoji na kokari
Shafiu Halliru ya yaba da kokarin da jami'an tsaro suke yi wajen samar da tsaro a kan hanyar Funtua-Gusau.
Ya bayyana cewa sojojin da aka sanya a hanyar na taimakawa sosai wajen samar da tsaro.
"Gaskiya suna kokari sosai. Muna yi musu fatan Allah ya ci gaba da ba su nasara a aikin da suke yi."
- Shafi'u Halliru
'Yan bindiga sun sace mutane a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyuka guda biyu na karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara.
'Yan bindigan sun kashe mutane da dama tare da yin awon gaba da sama da mutum 100, yayin hare-haren da suka kai.
Miyagun 'yan bindigan dai sun kutsa cikin kauyukan ne a kan babura imda suka rika harbi ba kakkautawa kan mai uwa da wabi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

