Harin Masallaci: Gwamna Radda Ya Ziyarci Kauyen Mantau, Ya Dauki Alkawura
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya kadu kan mummunan harin da 'yan bindiga suka kai a karamar hukuma Malumfashi
- Malam Dikko Umaru Radda PhD ya ziyarci kauyen domin yin ta'aziyya tare da jajantawa iyalan wadanda lamarin ya ritsa da su
- A yayin ziyarar gani da ido da ya kai kauyen, Gwamna Radda ya dauki alkawura domin saukaka radadin da mutanen yankin suke ciki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya kai ziyarar ta’aziyya zuwa kauyen Mantau a karamar hukumar Malumfashi.
Gwamna Radda ya ziyarci kauyen bayan da ’yan bindiga suka kashe masallata 32 lokacin da suke Sallah a masallaci.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamna, Ibrahim Kaulaha Mohammed, ya sanya a shafinsa na Facebook, ranar Laraba, 27 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Harin 'yan bindiga ya sosa zuciyar gwamna Radda
Gwamna Radda a yayin ziyarar tasa ya sanar da bayar da tallafin gaggawa na N500,000 ga kowane gida da lamarin ya shafa.
Ya nuna takaici matuka kan mummunan harin tare da kira ga al’umma da su haɗa kai wajen yaki da rashin tsaro.
"Abin da na gani abin taɓa zuciya ne, marayu, gidaje da aka kona, da iyalai cikin tashin hankali. Mun tambaye su bukatunsu, na kuma tabbatar musu cewa gwamnati za ta magance waɗannan matsaloli ɗaya bayan ɗaya."
- Gwamna Dikko Radda
Me Gwamna Radda ya ce kan harin Mantau
Ya bayyana cewa an kai harin ne a matsayin ramuwar gayya bayan mazauna ƙauyen sun kori ’yan bindigan a baya, inda suka kashe guda bakwai tare da kwace makamai.
A cewarsa, an kashe mutane 32, mutum 20 a cikin masallaci da mutum 12 a wajen masallacin.
Sannan gwamnan ya ce an kona gidaje 20 tare da yin garkuwa da mutane 76, duk da dakarun sojojin saman Najeriya sun kubutar da su washegari.

Kara karanta wannan
"Na hakura": Gwamna Bala ya bayyana dalilin jingine burin yin takarar shugaban kasa
Gwamna Radda ya dauki alkawura
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Gwamna Radda ya umarci ma’aikatar ayyuka da ta tafi ta kimanta hanyar Mantau tare da tsara shirin gina sabuwar makaranta da asibiti.
Ya kara da yin alkawarin gyaran masallacin da aka lalata, sake gina gidajen da aka kona da kuma bayar da tallafi ga iyalan waɗanda suka rasu.

Source: Facebook
Gwamna Radda ya sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
"Za mu ci gaba da kare rayuka da dukiya. Tsaro al’amari ne na rayuwar ɗan adam, ba na siyasa ba. Da goyon bayan jama’armu, In Sha Allah, za mu yi nasara."
- Gwamna Dikko Radda
Gwamna Radda ya magantu kan rashin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ta addabi jihar.
Gwamna Radda ya nuna takaicinsa kan yadda ake samun sakaci a wasu lokutan daga bangaren jami'an tsaro idan aka tashi kawo hare-hare.
Ya koka kan cewa a matsayinsu na gwamnoni, wasu abubuwan sun fi karfinsu domin ba su da iko a kan sojoji ko 'yan sanda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
