Kaduna: An Ɓarke da Murna bayan Mutuwar Hatsabibin Ɗan Daba da Ya Addabi Bayin Allah
- Mutane da dama suna ta murna bayan tabbatar da mutuwar wani rikakken dan daba a Kaduna da ke Arewacin Najeriya
- Rahotanni daga Kaduna sun tabbatar da mutuwar sanannen ɗan daba abin da ya jawo martani daban-daban a yankin
- Wasu mazauna unguwar sun nuna farin ciki da mutuwarsa saboda zargin cin zarafi, yayin da wasu suka yi jimamin mutuwar tasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Rahotanni daga jihar Kaduna sun tabbatar da mutuwar sanannen ɗan daba wanda ya addabi al'umma da dama.
Majiyoyi sun bayyana cewa al'ummar yankin da dan daban ya fito sun nuna farin ciki kan lamarin da ya faru.

Source: Facebook
Rahoton Zagazola Makama ya ce dan daba, Abubakar Sadiq wanda aka fi sani da Habu Dan Damisa ya yi bankwana da duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda 'yan daba ke addabar jihohin Arewa
Hakan na zuwa ne yayin da jihohin Arewacin Najeriya ke fama da hare-haren yan daba wanda ke jawo rasa rayuka da dukiyoyi.
Kaduna ma ba a bar ta a baya ba, yan daba na cin karensu babu babbaka a wasu yankunan jihar.
'Yan daba sun kashe soja a Kaduna
Ko a kwanakin baya, wasu miyagun matasa sun jawo asarar ran babban jami’in sojan ruwa Commodore M. Buba a lokacin da suke kici-kicin kwace masa waya.
An tabbatar da cewa M. Buba ya tsaya domin gyara tayar motarsa da ta samu matsala a Kawo ta jihar Kaduna a lokacin da lamarin ya afku.
An ga wasu matasa sun bi ta kan jami'in suna kokarin kwace masa masa da sauran kayan da take tafe da shi, amma rikici ya kaure a tsakaninsu.

Source: Original
Wasu sun yi murna bayan mutuwar 'dan daban
Mutuwar matashin, ɗan unguwar Tudun Wada a Kaduna, ta faru ne ranar Laraba 27 ga watan Agustan 2025 da muke ciki.
An tabbatar da cewa mutuwar ta jawo martani daban-daban tsakanin mazauna yankin.
Yayin da wasu mazauna suka nuna farin ciki, suna murnar labarin rasuwarsa, wasu kuma sun nuna tausayin da kukan rashin rashin da aka yi.
“An zarge shi da cin zarafi a unguwa tare da zargin kashe mutane da dama.
"Amma abin kawai shi ne mu ce Allah ya gafarta wa mamatanmu kuma ya shiryar da zuriyarmu."
- Cewar wani mazaunin yankin
Rahoton ya tabbatar cewa Dan Damisa ya kasance matashin da aka fi tsoro a yankin.
Hakan ya jawo murna daga wasu ɓangarori saboda ya gudanar da rayuwarsa cikin tayarwa al'umma hankali.
'Yan sanda sun hallaka 'dan daba a Kano
A baya, mun ba ku labarin cewa rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta kawo ƙarshen ayyukan ta'addancin wani tantirin ɗan daba da ake kira Baba Beru.
Ƴan sandan sun hallaka Baba Beru ne bayan ya yi yunƙurin farmakarsu da wuƙa lokacin da suke je kama shi a jihar Kano.
Baba Beru dai ya gamu da ajalinsa ne a ranar Talata, 22 ga watan Afirilun 2025 a unguwar Gwammaja da ke birnin Kano.
Asali: Legit.ng

