'Yan Bindiga Sun Kai Hare Hare a Zamfara, Sun Sace Mutum 100 a Jihar
- 'Yan bindiga sun kai hari kauyuka biyu a ƙaramar hukumar Bukkuyum, jihar Zamfara inda suka kashe mutum biyu
- Aƙalla mutane 100 ciki har da mata da yara aka sace tare da kwashe dabbobi daga kauyukan Gamdum Mallam da Ruwan Rana
- ‘Yan bindigar sun raba kashi biyu, wani ɓangare na yin garkuwa yayin da dayan ya kafa shingen hanya yana harbin jama’a
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - 'Yan bindiga dauke da makamai sun kutsa kauyuka biyu na ƙaramar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kashe rayuka tare da yin garkuwa da mutane fiye da mutum 100 a cikin makon da ya gabata.

Source: Original
The Cable ta rahoto cewa shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun shiga kauyukan ne a kan babura, suna harbe-harbe ba kakkautawa suna tsoratar da jama’a.
Lamarin ya girgiza mazauna yankin, inda suka shiga fargaba da jin tsaro, suna koka wa kan cewa gwamnati ba ta ɗauki mataki da wuri ba wajen kawo ƙarshen hare-hare a jihar.
An sace mutum 100 a Zamfara
Mai unguwar Gamdum Malam, Muhammadu ya bayyana cewa mata da yara da dama aka yi garkuwa da su a lokacin harin sun kai 100.
Rahoton Reuters ya ce ya ƙara da cewa:
“'Yan bindiga sun kashe da dama sannan suka sace mutane da yawa, ciki har da mata da yara, kafin su tafi da su cikin dajin Makakari.”
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun rabu kashi biyu a lokacin farmakin da suka kai.
Wani ɓangare ya mamaye kauyukan don yin garkuwa da jama’a da dabbobi, yayin da wani ɓangaren ya kafa shingen hanya a Adafka, inda suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi.

Source: Facebook
Fargabar mazauna yankunan a Zamfara
Wani daga cikin mazauna Gamdum Malam, Huzaifa Isa ya shaida cewa lamarin ya jefa jama’a cikin yanayin tsoro da kuncin rayuwa.
A cewarsa:
“Ɗaya bangaren 'yan ta'addan na yin garkuwa da mutane da dabbobi, yayin da wani ɓangare ya kafa shinge a ƙofar Adafka. Mun zama kamar bayi a ƙasarmu, kamar babu gwamnati.”
Wannan furuci ya nuna yadda al’umma ke jin cewa suna rayuwa cikin tsaro, lamarin da ya sanya da dama ke ƙaura daga garuruwansu don tsira da rayukansu.
'Dan majalisar dokokin Zamfara ya magantu
'Dan majalisar dokoki mai wakiltar mazabar Bukkuyum ta Kudu a majalisar jihar Zamfara, Hamisu Faru ya tabbatar da sace mutane fiye da 100 a hare-haren.
Ya ce:
“Aƙalla mutum 100 aka yi garkuwa da su tun safiyar Asabar. '
Yan bindigar sun kai hari Nasarawa Burkullum, sannan suka tsallaka ruwa zuwa Ruwan Rana inda suka sace karin mutane 46.”
An kama dan daba Linga a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Kano ta kama wani dan daba da ake kira Linga.
Rahotanni sun nuna cewa Linga na amfani da kafafen sada zumunta wajen yada bidiyonsa dauke da makamai.
Binciken 'yan sanda ya tabbatar da cewa an same shi da makamai tare da wani abokinsa, kuma yana shigar da matasa harkar daba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


