Yadda Uwargidan Gwamnan Borno Ta Gwangwaje Mai Shara da Kyaututtuka bayan Mayar da N4.8m
- Wata mai shara a Asibitin Koyarwa na Maiduguri, Faiza Abdulkadir, da ta mayar da Naira miliyan 4.8 da aka tura mata a kuskure ta ja hankali
- Uwargidan Gwamnan Jihar Borno, Dr. Falmata Babagana Zulum, ta karrama ta da kyautar kudi da kuma tallafi daban-daban
- Faiza, da ke samun albashin N30,000 a wata tana kula da ‘ya’yanta biyar da mahaifiyarta, ta ce tsoron Allah ne ya sa ta mayar da kuɗin
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Uwargidan Jihar Borno, Dr. Falmata Babagana Zulum, ta ba da kyautar N1m ga Faiza Abdulkadir, bayan ta nuna bajinta wajen mayar da kudin da ba nata ba.
An yi kuskuren tura Naira miliyan 4.8 asusun bankin Fa'iza, kuma rahotanni sun tabbatar da yadda ta rika zarya zuwa banki domin a mayar da kudin ga mai shi.

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa Fa'iza, wadda ke samun albashin N30,000 kacal a wata, tana kula da ‘ya’yanta biyar da kuma mahaifiyartada ta tsufa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai dakin Gwamnan Borno ta gwangwaje Fa'iza
Legit.ng ta wallafa cewa a wani biki na musamman da aka shirya domin ta, Uwargidan gwamnan Borno, Dr. Falmata Babagana Zulum ta jinjina mata.
Ta bayyana cewa Faiza ta zama abar koyi ga mata da maza baki ɗaya a jihar wajen jajircewa don tabbatar da gaskiya da rikon amana.
Ta ce:
“Ina farin ciki da cewa wannan mata daga Borno ta nuna irin gaskiya da tsoron Allah da ake nema. Na ba ta Naira miliyan 1 domin taimaka mata da iyalinta. Ina kira a ɗauke ta matsayin abin koyi."
Haka kuma, Kwamishinar Mata ta Jihar Borno, Hajiya Zuwaira Gambo, ta bayyana cewa gwamnati za ta ba Faiza kayan koyon sana’o’i da kayan abinci domin ƙarin tallafi.

Kara karanta wannan
Kudin fansa: 'Yan bindiga sun dauke mutum 4700, an ji biliyoyin da aka rasa a shekara 1
Borno: Faiza ta bayyana dalilin mayar da N4.8m
Faiza, ‘yar asalin unguwar Gwange a Maiduguri, ta shaida wa Legit cewa tsoron Allah ne ya sa ta mayar da kuɗin duk da halin ƙuncin da take ciki.
A kalamanta:
"Wallahi haka na mayar fa, haka na ce miki zuciyata a tsinke haka da kudin nan ya shiga. Ya kira ni, ya ce ke ce Fa'iza AbdulKadir? Na ce e."

Source: Original
Ta ce ya ɗauki kwanaki uku kafin ta kammala aikin banki da ya ba ta damar mayar da kuɗin ga wanda ya turo daga Jihar Kebbi.
"Washegari ya sake kira na ya ce kudin bai tafi ba, na ce baba na ka ji ni, ba ka ganni da ido ba, amma kana ji na da kunne."
"In na ci kudinka na ci haram, ni halal na ke nema ba haram ba." "Ni ina neman wurin kwanciya ba na duniya na ke so ba."
Ta bayyana cewa jama'a da dama sun gwangwaje ta da kyaututtuka bayan labari ya fantsama cewa ta mayar da kudin.
Fa'iza ta mayar da N4.8m a Borno
A baya, kun ji cewa yadda wannan mata mai aikin shara a cibiyar kiwon lafiya, Faiza Abdulkadir, ta sake tabbatar wa duniya cewa har yanzu akwai sauran masu gaskiya a Najeriya.
Faiza, wadda ke samun albashin N30,000 a wata, ta mayar da Naira miliyan 4.8 da aka tura cikin asusun bankinta a kuskure a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Dan uwanta, Ibrahim Muhammad AbdulRahman, shi ne ya tabbatar da wannan al’amari a inda ya bayyana cewa duk da ƙuncin rayuwar da Faiza ke ciki, ta ki rike kudin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

