China Ta ba da Tallafin Ambaliya, za a Raba Naira Biliyan 1.5 a Jihohin Arewa

China Ta ba da Tallafin Ambaliya, za a Raba Naira Biliyan 1.5 a Jihohin Arewa

  • Gwamnatin Tarayya ta kulla yarjejeniya da kasar China domin bayar da tallafin Dala miliyan 1 ga al’ummomin da ambaliya ta shafa a Arewa
  • Ministan Tsare-tsare da Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, ya bayyana tallafin a matsayin taimakon gaggawa da zai saukaka radadin rayuwa
  • Hukumar SEMA a Jihar Yobe ta fara kwashe iyalai sama da 250 daga Garin Kolo zuwa wasu wurare domin kare su daga sake fadawa cikin ambaliya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Najeriya da kasar China sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tallafawa wa al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa a Arewa.

Wannan yarjejeniya na daga cikin matakan karfafa hadin kai tsakanin kasashen biyu a fannin taimakon jin kai da raya kasa.

China a Najeriya tare da Atiku Bagudu
Jakadan China a Najeriya tare da Atiku Bagudu. Hoto: @YDunhai
Source: Twitter

Legit ta tattaro bayanai kan yarjejeniyar ne a cikin wani sako da jakadan China a Najeriya ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Sarkin da ya 'kunyata' Najeriya a Amurka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan Tsare-tsare da Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, ya bayyana cewa taimakon ya zo a lokacin da ya dace domin rage radadin da dubban iyalai ke fuskanta sakamakon ambaliya.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati tare da ma’aikatanta da hukumomi za su tabbatar da gaskiya, adalci da kuma tabbatar da cewa jama’a sun amfana kai tsaye wajen raba tallafin.

Najeriya ta samo tallafi daga China

Bagudu ya bayyana tallafin Dala miliyan 1 da aka samo a matsayin wata shaida ta dadadden zumunci tsakanin Najeriya da China wanda ya dogara kan mutunta juna da hadin kai.

Ministan ya ce an kafa tsarin hadin gwiwar sa ido tare da ofishin jakadancin China a Najeriya domin tabbatar da amfani da kudin yadda ya kamata.

Ya kara da cewa kudin tallafin zai cike gibi wajen ayyukan jin kai da ake gudanarwa, da dawo da rayuwar al’ummomi da ambaliya ta fi shafa a Arewa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jigawa ta ayyana hutun rana 1 ga ma'aikata saboda 'wani muhimmin biki'

A wani bidiyo da Dada Olusegun ya wallafa a X, an ji ministan ya ce zai kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu a fannoni daban-daban, kamar kasuwanci, noma, fasaha da gine-gine.

Maganar jakadan kasar China a Najeriya

A nasa jawabin, Jakadan kasar China a Najeriya, You Dunhai, ya nuna cewa wannan tallafi alama ce ta jajircewar kasarsa wajen tsayawa tare da Najeriya musamman a lokacin matsaloli.

Ya kuma yi nuni da ci gaban da aka samu a dangantakar kasashen biyu cikin shekara guda da ya kwashe a Najeriya, musamman bayan ziyarar Bola Tinubu China a 2024.

Shugaba Bola Tinubu a kasar China a 2024
Shugaba Bola Tinubu a kasar China a 2024. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Jakadan ya kuma jaddada cewa kasar China za ta ci gaba da mara wa Najeriya baya, musamman bayan sanarwar shugaban kasar, Xi Jinping, da ta ba da damar cire haraji a kayayyakin Afirka.

A wani bangare, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) ta sanar da kwashe akalla iyalai 250 daga Garin Kolo a Karamar Hukumar Nangere sakamakon ambaliyar ruwa.

An yi hasashen ambaliya a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa ma'aikatar muhalli ta tarayya ta fitar da gargadi kan fargabar samun ambaliya a wasu jihohin kasar nan.

Kara karanta wannan

Gwamna ya kara albashi, wasu ma'aikata za su samu rabin miliyan a wata

Rahotanni sun nuna cewa an lissafa jihohin Kano, Yobe, Jigawa Gombe da wasu yankuna sama da 10 a jerin inda ake fargabar ambaliyar.

A karkashin haka, gwamnatin tarayya ta yi kira ga 'yan Najeriya da su rika bin umarnin da hukumomi ke bayarwa game da ambaliyar ruwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng