Gwamna Radda Ya Tona Sakacin Jami'an Tsaro har Aka Hallaka Musulmai a Masallaci

Gwamna Radda Ya Tona Sakacin Jami'an Tsaro har Aka Hallaka Musulmai a Masallaci

  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya yi magana kan matsalolin tsaro da ke kara kamari a wasu garuruwa
  • Radda ya shawarci jama’a su nemi hanyoyin kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga da ke jawo asarar rayuka
  • Ya koka cewa gwamnoni ba su da iko kan sojoji ko ’yan sanda, inda ya ce a Gidan Mantau an samu bayanan sirri kafin hari

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Gwamna Dikko Umaru Radda ya yi magana kan matsalolin tsaron da suka addabi jihar Katsina a Arewacin Najeriya.

Mai girma Radda ya shawarci mutane kan yadda za su kare kansu duba da yadda lamarin ke sake rincabewa a jihar.

Gwamna Radda ya shawarci al'umma kan hare-haren yan bindiga
Gwamna Dikki Umaru Radda yayin taro da jami'an tsaro a Katsina. Hoto: Dikki Umaru Radda.
Source: Facebook

Gwamna Radda ya koka kan matsalolin tsaro

Gwamnan ya bayyana haka a cikin wani faifan bidiyo yayin hira da DCL Hausa da aka wallafa a manhajar Facebook.

Kara karanta wannan

'Yan Katsina na gunaguni, Gwamna Radda ya dawo Najeriya amma ya tsaya a makwabta

Gwamna Radda ya kuma koka game da tabarbarewar tsaro musamman yadda ake samun matsala daga jami'an tsaro.

Ya bayyana cewa a matsayinsu na gwamnoni ba su da ikon tilasta sojoji ko 'yan sanda zuwa filin daga.

Radda ya bayyana yadda aka samu bayanan sirri awa 15 kafin a kai farmaki a Gidan Mantau wanda ya yi ajalin mutane da dama.

Ya bayyana cewa:

"Muna matsayin shugabannin tsaro a jihar amma ba mu isa mu tilastawa sojoji su je wurin da aka tura su ba.
"Ba mu isa mu tilasta dan sanda zuwa inda aka tura shi ba, iyaka dai mu ba da umarni kuma ba dole ba ne a amshi wannan umarnin ba.
"Zan ba ka misali kan hari Gidan Mantau, awa 15 kafin a kai harin mun samu bayanan sirri, mun fadawa duk wata hukumar tsaro cewa za a kai hari."
Gwamna Radda ya tona yadda jami'an tsaro ke sakaci
Gwamnan jihar Katsina da ke fama da matsalolin tsaro. Hoto: Dikko Umaru Radda.
Source: Facebook

Gwamna Radda ya koka kan matsalar tsaro

Kara karanta wannan

Gwamna ya samu gagarumin goyon baya, ana so ya nemi takarar shugaban kasa a 2027

Gwamna Radda ya ce jami'an tsaro ba su dauki matakin da ya dace ba har aka kai farmakin wanda hakan abin takaici ne.

Ya ce:

"Amma babu abin da aka yi har kuma aka yi abin da aka yi, har saura awa uku an tabbatar da cewa maharan ga su nan za su kai hari."

Dalilin irin wannan matsalolin Gwamna Radda ya ce lallai ya kamata a samar da yan sanda na jihohi.

Ya ce hakan ne zai ba su dama suna saya musu makamai da kuma ba su umarni domin kawo karshen matsalolin tsaro.

Gwamna Radda ya magantu game da lafiyarsa

Game da batun lafiyarsa, Gwamna Radda ya ce ya dawo lafiya kuma yana jinsa garau a yanzu ba tare da matsala ba.

Ya kara da cewa:

"Garas nake, garas nake, jikina ya dawo garas, wanda bai son ya ji haka sai dai ya toshe kunnuwansa."

Katsina da jihohi da ke fama da matsalar tsaro

Kun ji cewa an fitar da wani rahoto yayin da Najeriya ke ci gaba da fama da rashin tsaro musamman a Arewacin kasar.

Kara karanta wannan

Kudin fansa: 'Yan bindiga sun dauke mutum 4700, an ji biliyoyin da aka rasa a shekara 1

Matsalolin sun kama daga garkuwa da mutane da ta'adin 'yan Boko Haram wanda ya daidaita yankin Arewacin Najeriya.

Wani rahoton bincike ya bayyana cewa, a cikin shekara guda, ‘yan Najeriya sun biya biliyoyin kudi a matsayin kudin fansa ga masu garkuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.