'Allah Cire Ni a Gadon Sarauta': Sarki a Najeriya Ya Ƙaryata Zargin Yana Shan Wiwi

'Allah Cire Ni a Gadon Sarauta': Sarki a Najeriya Ya Ƙaryata Zargin Yana Shan Wiwi

  • Mutane da dama sun yi yada cewa wani babban Sarki na shan wiwi duba da yadda yake magana da mu'amalantar mutane
  • Sai dai Sarkin Iwo, Oba Abdulrosheed Akanbi, ya yi Allah wadai da masu yada jita-jitar cewa yana shan tabar wiwi
  • A cikin wani faifan bidiyo da ya bazu, ya ce idan yana shan wiwi Allah ya sauke shi daga gadon sarauta, amma ya musanta zargin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Iwo, Osun - An yi ta yada jita-jitar cewa fitaccen Sarki a yankin Yarbawa yana ta'ammali da tabar wiwi lamarin da ya fusata shi.

Sarkin Iwo, Oba Abdulrosheed Adewale Akanbi, ya yi martani kan zargin da ake yi masa wai yana shan wiwi a rayuwarsa.

Sarki ya rantse da Allah bai shan wiwi
Sarkin Iwo kenan a jihar Osun, Oba Abdulrosheed Akanbi. Hoto: Emperor Abdulrasheed Adewale Akanbi Telu 1.
Source: Facebook

Sarkin ya karyata zargin cewa yana shan tabar wiwi, inda ya ce wannan magana karya ce daga makiya, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

'Na yi mulkin gaskiya': Ganduje ya yi zazzafan martani ga Gwamna Abba kan zarge zarge

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarki Akanbi ya yi nasara a kotu

Martanin barasaken ya zo ne bayan kotun daukaka kara ta tabbatar da nadinsa a matsayin Sarkin Iwo, wanda ya ce nasara ce daga Allah.

An yi ta kai ruwa rana kan kujerar sarautar Iwo inda ake kalubalantar Mai Martaba Akanbi da zargin nadinsa bai cika ka'ida ba.

Bayan hukuncin, Mai Martaba Akanbi ya bayyana farin ciki tare da jaddada cewa mulkinsa na Allah ne, kuma babu wanda zai iya rusa shi.

Ya kuma ce zai kare al’adun gargajiyar Iwo tare da kawo sauye-sauye na zamani, yana mai cewa mulkinsa ya kawo daukakar gwamnati da inganta ta.

Sarkin ya bayyana masu kalubalantarsa a kotu a matsayin masu bata lokaci, yana cewa korafe-korafensu kawai sun kara karfafa matsayin mulkinsa a kan gadon sarauta.

Sarki ya ƙaryata zargin cewa yana shan wiwi
Mai Martaba Sarkin Iwo kenan, Oba A wurin taro. Hoto: Emperor Abdulrasheed Adewale Akanbi Telu 1.
Source: Twitter

Sarki ya ƙaryata cewa yana shan wiwi

A wani bidiyo da Adeniji Alabi ya wallafa a Facebook, Oba Akanbi ya bayyana cewa wadanda suka kirkiri wannan magana marasa kunya ne kuma Allah zai hukunta su.

Kara karanta wannan

JIBWIS ta ƙalubanci masu cewa an yi wa Jingir ihu a Abuja, ta sanya kyautar kuɗi

Ya yi ikirari cewa idan yana shan wiwi, Allah ya sauke shi daga gadon sarauta, amma ya dage cewa zargin babu tushe.

Ya ce:

“Suna yi mani karya, su marasa kunya ne, sai dai idan ina shan wiwi, Allah ya cire ni daga wannan gadon sarauta, ku masu zargin, Allah zai hukunta ku.”

Bararaken ya sha tayar da kura musamman a kafofin sadarwa inda yake fadin abin da ke cikin ransa ko da kuwa ba zai yi wa mutane dadi ba.

A yanzu haka basaraken yana Canada inda yake hutawa tare da wallafa faya-fayen bidiyo da ke nuna jin dadi wanda hakan ke jawo maganganu da yabo daga wasu mutane.

An bukaci gwamna ya tube Sarki daga sarauta

Mun ba ku labarin cewa an bukaci gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke da ya tuge sarkin Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi daga sarautar garin.

Malamin addinin gargadiya, Satguru Maharaj Ji shi ya bukaci hakan daga gwamnan saboda yadda Sarkin ke zubarwa masarauta mutunci.

Maharaj ya bukaci Gwamna Adeleke ya yi gaggawar daukar mataki kan Akanbi saboda barinsa kan kujerar hatsari ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.