Shugaba Tinubu Ya Kara Kawo Sabon Shiri, Za a Taimaki Matasa Miliyan 7 a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta kawo sabon shirin da za a dauki matasa miliyan bakwai domin horar da su kan fasahar zamani a fadin Najeriya
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya bayyana hakan a wurin taron matasa da aka shirya a kwalejin tsaron kasa da ke Abuja
- Ministan matasa, Ayodele Olawande, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu a taron, ya ce za a ba matasan horo ta yadda za su amfana da shirin a rayuwarsu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana shirin horas da matasa miliyan bakwai a fannin fasahar zamani a fadin jihohin Najeriya da Abuja.
Matasa miliyan uku daga ciki za su samu horo da gogewa a fannoni kamar fasahar AI, tsaro na yanar gizo da kuma kirkiro manhajar kwamfuta.

Kara karanta wannan
Jima: An tunawa gwamnoni 19 hanyar da za su samu 'makudan kudi' a Arewacin Najeirya

Source: Twitter
Leadership ta ce an bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja yayin taron matasa na 2025 mai taken: “Matasa da jagoranci, gina tushen shugabanci mai dorewa.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasa za su amfana da shirye-shiryen Tinubu
Wakilin shugaban kasa, Ministan Harkokin Matasa, Ayodele Olawande, ya ce an shirya wannan taron ne domin fara koyawa matasa harkokin shugabanci.
Ya jero wasu tsare-tsaren gwamnati da ake aiwatarwa ciki har da Nigerian Youth Academy, wadda aka tsara don horas da matasan miliyan bakwai a fadin kasar nan.
Olawande ya ce matasa suna taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban kasa kuma wajibi ne a ba su horon abubuwan zamani, dabi’u da tunani domin su ne shugabannin gobe.
Shirin da Tinubu ya kawo don taimakon matasa
Ya sake nanata kudirin gwamnatin tarayya na ƙarfafa matasa da da kawo ci gaban ta hanyar gina shugabanci mai nagarta.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, ministan ya ce:
“Gwamnatin Tarayya na kokarin ganin matasa da sauran yan Najeriya sun samu ilimi kan fasahohin zamani, kuma ta kuduri aniyar cimma kashi 70% daga nan zuwa 2027.
Sauran shirye-shirye da ministan ya ce gwamnatin Tinubu na kokarin aiwatarwa sun hada da kirkirar ayyukan yi sama da miliyan biyu da shirin bayar da lamunin karatu don ba kowa damar neman samun ilimi.
Haka nan Olawande ya ambaci shirin noma da ke tallafawa dubban matasa ‘yan kasuwa, da kuma shirin National Youth Fellowship na haɓaka fannin lafiya da hidimar jama’a a matakin ƙananan hukumomi.

Source: Twitter
Dalilin shirya taron matasa a Abuja
A jawabinsa na maraba, Kwamandan Kwalejin Tsaron Kasa, Rear Admiral James Okosun, ya ce an shirya wannan domin wayar da kan matasa kan harkokin shugabanci.
Sauran masu jawabi sun bukaci mahalarta da su yi amfani da abin da suka koya a cikin al’ummominsu, wuraren aiki da cibiyoyi domin gina kyakkyawan makomar kasar.
Bola Tinubu ya dawo da shirin GEEP
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta dawo da shirin GEEP wanda ke bai wa kananan yan kasuwa rancen kudi da kuma tallafi a Najeriya.
An sauya sunan shirin zuwa Renewed Hope GEEP (RHGEEP 3.0), tare da burin tallafawa yan Najeriya masu ka nan an san'o'i miliyan biyar daga nan zuwa 2027.
Tun farko an kirkiro shirin GEEP ne a ƙarƙashin hukumar (NSIP) da nufin samar da ƙaramin bashi da tallafin kuɗi ga miliyoyin ‘yan Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

