Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani game da Sarkin da Ya Bata Sunan Najeriya a Amurka

Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani game da Sarkin da Ya Bata Sunan Najeriya a Amurka

Jihar Osun - A jiya Talata ne aka yanke wa Sarkin Ipetumodu daga jihar Osun, Oba Joseph Oloyede, hukuncin daurin fiye da shekaru hudu a gidan yari a kasar Amurka.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kotun Amurka ta daure basaraken mai martaba bayan kama shi da laifin cinye kudin tallafin COVID-19 da ya kai Naira biliyan 6.4 a kudin Najeriya.

Oba Joseph Oloyede.
Hoton Sarkin gargajiya a Osun wanda kotu ta daure a Amurka Hoto: Bright Sunday
Source: Twitter

Kotun Amurka ta daure Sarki daga jihar Osun

A rahoton da Vanguard ta kawo, Sarkin ya karbi wadannan kudi ne ta hanyar amfani da bayanan bogi, da kuma kauncewa biyan haraji, lamarin da ya kara jawo zargi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wata sanarwa daga Ofishin Lauyan Gwamnatin Amurka a Arewacin Ohio a ranar Talata, za a tsare Sarkin na shekaru uku bisa kulawar jami'an tsaro bayan ya gama zaman gidan yari.

Kara karanta wannan

Gwamna ya samu gagarumin goyon baya, ana so ya nemi takarar shugaban kasa a 2027

Bugu da kari, kotun ta umarci ya biya $4,408,543.38 a matsayin diyya, sannan za a kwace duka kadarorin da ya mallaka ta hanyar da doka ta haramta.

Abubuwa 5 game da Sarkin da aka daure

A cikin wannan rahoto, Tribune Online ta kawo muhimman abubuwa guda biyar da ya kamata a sani game da shi:

1. Bayanai da shaidar zama dan kasa

Oba Joseph Oloyede shi ne sarkin gargajiya na masarautar Ipetumodu a jihar Osun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Mai Martaba Sarkin yana da takardun shaidar zama ‘dan kasa har guda biyu, Najeriya da Amurka, inda yake zaune a birnin Ohio.

Bayan mukaminsa na sarauta, yana aiki a matsayin mai kula da harkokin haraji kuma yana da wasu kasuwanci da yake yi a Amurka.

2. Ilimi

Oloyede ya fara karatu a garin Ipetumodu, inda ya halarci makarantar Christ Church II da C & S Modern Commercial Secondary School.

Daga nan ya samu difloma a fannin Lissafin Kudi daga Kwalejin Fasaha ta Ibadan, kafin ya samu digirin MBA daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Enugu.

Kara karanta wannan

Kudin fansa: 'Yan bindiga sun dauke mutum 4700, an ji biliyoyin da aka rasa a shekara 1

Ya kuma yi wani MBA a Jami’ar Sarasota a Florida, Amurka, sannan daga baya ya sami shaidar karatun kasuwanci na Business Administration (DBA) daga jami'ar Argosy, Sarasota.

3. Aiki

Ya fara aikinsa a bangaren harkokin kudi, inda ya yi aiki da bankuna irinsu First Bank of Nigeria da John Holt Financial Merchant Bank.

Bayan ya koma Amurka, ya ci gaba da aiki a banki kafin ya shiga harkar koyarwa a jami’o’i, ya yi aiki a matsayin malami a jami'ar Indiana Wesleyan da jami'ar Phoenix.

Sarkin da aka daure a Amurka.
Hoton Sarki daga jihar Osun wanda ya bai wa Najeriya kunya a Amurka Hoto: Olajide Stave
Source: Twitter

4. Shekaru da hawansa karagar sarauta

Sarkin na jihar Osun yana da shekaru 62 a duniya, kuma ya hau kan karagar mulki a watan Nuwamba 2019.

An nada shi a sarautar Sarkin Ipetumodu bayan rasuwar wanda ya gada, Oba James Adedokun Adegoke, a watan Nuwamba 2017.

5. Masarautar da yake mulki

Masarautar Ipetumodu da ke cikin karamar hukumar Ife ta Arewa a jihar Osun, ta shahara a tarihi a matsayin daya daga cikin muhimman masarautu a jihar.

Har ila yau, garin Ipetumodu shi ne hedikwatar karamar hukumar Ife ta Arewa.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Gwamna ya shirya tsige Sarki Mai Martaba a Najeriya

Gwamna Adeleke na shirin tsige Sarkin

A baya, kun ji cewa Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun na shirin tsige Mai Martaba Sarkin Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede biyo bayan hukuncin kotun Amurka.

Kotun Amurka ta kama Sarkin Ipetumodu daga jihar Osun da laifin cinye kudin tallafin COVID-19 da ya karba da bayanan bogi.

Rahotanni sun nuna cewa matukar ba a samu wani sauyi daga baya ba, Gwamna Adeleke zai tube wa Sarkin rawani sakamakon laifin da ya aikata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262