'Yan Katsina Na Gunaguni, Gwamna Radda Ya Dawo Najeriya amma Ya Tsaya a Makwabta
- Gwamna Dikko Radda ya dawo gida Najeriya daga hutun da ya tafi a kasar waje, amma an rahoto cewa ya yada zango a Kaduna
- Yayin da ya sauka Kaduna, an ce ’yan majalisar dokokin Katsina sun kai wa gwamnan ziyara domin yi masa maraba da kuma jaje
- Ganawa tsakanin Radda da ’yan majalisar a Kaduna ta jawo ce-ce-ku-ce, inda mutane ke sukar gwamnan kan kin wuce wa Katsina
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - 'Yan Katsina sun fara guna guni a soshiyal midiya da suka samu labarin cewa gwamnansu, Dikko Radda ya dawo Najeriya amma ya yada zango a Kaduna.
Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta ruwaito cewa Gwamna Dikko Radda ya dauki hutun jinya na makonni uku daga ranar 18 ga Agusta, 2025.

Source: Facebook
Gwamna Radda ya yada zango a Kaduna
Sai dai, wani rahoto da jaridar Katsina Post ta fitar, an ji cewa Gwamna Radda ya karbi bakuncin 'yan majalisar dokokin Katsina a wani gida a Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar ta rahoto cewa 'yan majalisar dokokin Katsina sun je Kaduna ne domin yi wa Dikko Radda maraba da dawowa, da kuma jajanta masa kisan masallatan da aka yi a Malumfashi.
Tawagar 'yan majalisar dokokin jihar Katsina na karkashin jagorancin kakakin majalisar, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura.
Wasu 'yan majalisar da ba su samu kujerun zama ba, sun zauna a kasa, yayin da Hon. Nasir Daura ke zaune a kusa da gwamnan.
'Yan majalisa suna tare da Gwamna Radda
Gidan talabijin mallakin Katsina, watau KTTV ya rahoto cewa ganawar gwamnan da 'yan majalisar ta faru ne a jiya Talata, 26 ga Agusta, 2027.
Rahoton ya ce 'yan majalisar sun kuma nuna goyon bayansu ga tsarin mulkin Gwamna Radda yayin da yake ci gaba da jan ragamar Katsina zuwa Tudun-Mun-Tsira.
An wallafa hotunan gwamnan tare da 'yan majalisar a cikin falon wani gida suna tattaunawa, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.
Wasu 'yan Katsina sun fara guna-guni
Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin 'yan Katsina kan wannan lamari.
Bello Bello:
"Ta tabbata dai ba ta talaka ake yi ba, ya dawo amma bai da lokacin zuwa jajantawa al'umma, sai su ke zuwa jajanta mai a wanin garin da ba jihar shi ba."
Salmanu Dahiru Iyatawa:
"Allah wadaran naka ya lalace, inda abin ya dame su, dunguma za su yi su je garin su jajanta wa mutanen."
Sa'eed Musa Sa'eed:
"Mu Katsinawa in dai mu na da hakki a kan ku, ku ka tauye mana, Allah ya bi mana hakkin mu."
Ahmad Rabiu:
"Allah ya isa tsakanin mu da ku, taron munafukai, azzalumai, mayaudara, maƙaryata!
"In sha Allahu, buƙatar ku ba za ta biya ba, tunda kun kasa tsare jinanen al'umma, duk kuma wanda yake ganin ba zai iya ba to ya aje kujerarsa, sai mu gane cewa shi mutumin kirki ne da gaske."
Abubakar Usman Dtm:
"Shin yaushe ne su mutanen da suka yi hadarin tare da mai girma gwamna za'a kai su ko da Abuja ne domin duba lafiyarsu? Kai ana mulkin jama'a a kasar nan."

Source: Facebook
Wasu mazauna jihar Katsinan sun ci gaba da cewa:
Ameer Mansur Sani:
"Allah ya isa tsakaninmu da ku walllahi. Kun ki zuwa Garin Mantau din yi masu jaje, shi kuma ya dawo yawan shi, ya kafe Kaduna, amma can za ku je mashi jaje. Lokaci ne."
Naziru Hamisu:
"To abin tambaya, me ya keyi Kaduna, ita ma fa jiha ce kamar jaharshi, me ya sa ba zai wuto garin shi, su taru su tafi Garin Mantau su yi masu jaje, kuma su basu kwarin gwiwa?"
Abubakar Mahdy Funtua:
"Wai ita Garin Mantau din, inda aka kashe ma gwamna yan uwa, shi ma na ji an ce da kyar ya sha, dama a Kaduna take?"
Sameenu Ice:
"Wai ba ma Katsina ya sauka ba kenan, ko gidan Buhari na Kaduna ya kara komawa ne!?"
Mustapha Yaro Tsigah
"Allah ya sa wannan ziyarar ta zama sanadiyar faduwarsu zabe gaba dayansu, Allah ya bamu masu kishin mu, kauyen ya dace ku je ba gurin wannan ba."
Gwamna Radda ya yi sababbin nade-nade
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya sanar da nadin sababbin mataimaka na musamman guda 15.
Wadanda aka nada suna da kwarewa a fannoni daban-daban, kuma za su taimaka wajen aiwatar da shirin “Gina makomarka.”
Gwamna Dikko Radda ya bukaci sababbin jami’an da su nuna ƙwazo da jajircewa wajen yi wa jama’ar Katsina aiki cikin gaskiya da amana.
Asali: Legit.ng



