"Ku Yafe Mani," An Ji Wanda Ya 'Jawo' Hatsarin Jirgin Kasan Kaduna zuwa Abuja da
- Hatsarin da jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya yi a jiya Talata, 26 ga watan Agusta, 2025 ya ja hankalin yan Najeriya
- Hukumar NRC ta dakatar da harkokin sufurin jiragen kasa a layin dogon Abuja zuwa Kaduna, ta fara bincike don gano abin da ya jawo hatsarin
- Shugaban NRC na kasa, Kayode Opeifa ya dauki alhakin abin da ya faru tare da tabbatar wa yan Najeriya cewa hakan ba za ta sake aukuwa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban hukumar kula da harkokin sufurin jiragen kasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa, ya dauki duka laifin hatsarin da ya faru a layin dogon Abuja zuwa Kaduna.
Kayode Opeifa ya kuma nemi afuwar yan Najeriya kan hatsarin da jirgin kasan ya yi a hanyarsa ta zuwa Kaduna ranar Talata, lamarin da ya jikkata fasinjoji shida.

Source: Twitter
Mista Opeifa ya bayyana hakan ne a lokacin da ya halarci shirin The Morning Brief na tashar Channels Television a ranar Laraba, 27 ga watan Agusta, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma tabbatar da cewa tuni aka fara gudanar da bincike kan lamarin kuma ba za a boye wa jama'a komai ba.
Idan ba ku manta ba, jirgin kasa ya gamu da hatsari yayin da ya sauka daga kan layin dogo a hanyarsa ta zuwa Kaduna bayan ya baro Abuja jiya Talata.
Shugaban NRC ya dauki alhakin hatsarin jirgi
Da yake martani kan hatsarin jirgin kasan, shugaban NRC ya ce:
“Ba ya ga neman afuwar ‘yan Najeriya, ina so in bayyana cewa a matsayina na darakta kuma shugaban hukumar NRC, na dauki alhakin abin da ya faru. Idan abu ya shafi tsaro, babu sakaci.
“Da zarar abu ya faru, shugaba ne ya kamata ya dauki alhaki. A wannan yanayin, ni na dauki alhaki."

Kara karanta wannan
Ta faru ta ƙare: Hukumar jiragen ƙasa ta dakatar da zirga zirga daga Kaduna zuwa Abuja
Wane mataki hukumar NRC ta dauka?
Sai dai ya kara da cewa, duk da tun farko bai kamata lamarin ya faru ba, amma hukumar NRC za ta tabbatar irin wannna hatsarin bai sake faruwa ba, rahoton Tribune.
“Ba mu yi tsammanin afkuwar irin wannan lamari ba, ba mu fatan ya faru, bai kamata ya faru ba, amma idan ya faru, ya ba mu damar mu nuna kwarewarmu.
“Kuma ina tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa kamar yadda muke yi a layin dogon Warri-Itakpe, wadda kuka ji ya ambata, mun rufe hanyar kimanin makonni uku da suka gabata.
“Na bayar da umarnin rufe ta saboda dalilan tsaro, kuma idan kuka ga irin aikin da ma’aikata ke yi a kan layin dogon, suna cire karafan titin su na canza sababbi, duk domin tabbatar da irin wannan abu bai sake faruwa ba."
- Kayode Opeifa.

Source: Twitter
Fasinjoji 6 sun ji rauni a hatsarin jirgin Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa an tabbatar da cewa fasinjoji shida sun ji raunuka sakamakon hatsarin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja.
Hukumar NSIB ce ta tabbatar hakan, amma ta bayyana cewa babu wanda ya rasa ransa sakamakon hatsarin jirgin kasan.
NSIB ta tabbatar da cewa ta tura tawagar bincike zuwa wurin da lamarin ya faru domin tattara shaidu da tattaunawa da masu ruwa da tsaki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

