Tura Ta Kai Bango: 'Yan Majalisar PDP Sun Taso Tinubu a Gaba kan Tsadar Rayuwa

Tura Ta Kai Bango: 'Yan Majalisar PDP Sun Taso Tinubu a Gaba kan Tsadar Rayuwa

  • Matsalar tsadar rayuwa da rashin tsaro na daga cikin abubuwan da suke cin tuwo a kwaryar 'yan Najeriya da dama
  • Kungiyar 'yan majalisar wakilai na jam'iyyar PDP, sun bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya farka daga barcin da yake yi don magance matsalolin
  • 'Yan majalisar sun nuna cewa al'amura sun tabarbare fiye da yadda ake tunani a kasar nan, domin mutane sun shiga cikin wani mawuyacin hali

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kungiyar ‘yan majalisar wakilai na PDP ta yi kira da babbar murya ga Shugaba Bola Tinubu.

'Yan majalisun na PDP sun bukaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta ɗaukar matakan magance matsanancin ƙuncin tattalin arziki da ya addabi ‘yan Najeriya.

'Yan majalisar PDP sun ba Tinubu shawara
Hoton 'yan majalisar wakilai za zauren majalisa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: @HouseNGR, @DOlusegun
Source: Twitter

'Yan majalisun sun bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da suka gudanar a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

Dele Momodu: 'Yadda Wike da Tinubu su ka kawo tsarin miƙa mulki Kudu a PDP'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar, Fred Agbedi, wanda ya samu rakiyar takwarorinsa, ya ce ‘yan Najeriya na kashe kansu saboda tsadar rayuwa da ke kara tsananta a kullum, jaridar Daily Trust ta tabbatar da batun.

'Yan majalisar PDP sun aika sako ga Tinubu

Ya yi tir da kashe-kashen da ake yi a kasar nan, yana mai cewa Shugaba Tinubu yana ta yawo a kasashen waje maimakon ziyartar iyalan da suka rasa ‘yan uwa a waɗannan hare-haren.

"Muna kuma kira ga gwamnati mai ci ta tabbatar da tsaro ga ‘yan Najeriya daga Imo, Katsina, Plateau, Benue, Zamfara, har zuwa Borno."
"Akwai kunci mai tsanani a wannan kasa, kuma ‘yan Najeriya na kuka da ciwo a kullum. Mutane suna kashe kansu saboda gwamnati ba ta kula da su."
"‘Yan Najeriya na cikin tsananin wahala, shugaban kasa ka tabbatar ka kula da halin da ‘yan kasa ke ciki."
"Ta ya za a ce ana kashe ‘yan Najeriya, amma shugaban kasa yana can a Brazil da sauran kasashe."

Kara karanta wannan

PDP ta koka, ta zargi EFCC da garkame manyan 'ya 'yanta 2 a Kaduna

"Mun tuna lokacin da lamarin Chibok ya faru, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yana waje, amma ya katse tafiyarsa nan take, ya dawo Najeriya, ya nuna goyon baya ga ‘yan kasa."

- Fres Agbedi

Fred Agbed ya yi ikirarin cewa sama da mutane 10,000 aka kashe cikin shekaru biyu da suka gabata, abin da ya bayyana a matsayin abin tayar da hankali.

Ana kiraye-kiraye ga Tinubu kan tsadar rayuwa
Hoton shugaban kasan Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

An bukaci Tinubu ya sa baki a rikicin Osun

Haka kuma, ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya bayar da umarnin sakin kuɗaɗen kananan hukumomi na jihar Osun.

Kudaden kananan hukumomin jihar Osun dai an rike su ne sakamakon rigimar da ake yi kan zaben ciyamomi da kansiloli da aka gudanar.

An wanke Tinubu kan matsaloli a Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya dora alhakin matsalolin da ke faruwa a Najeriya kan gwamnoni.

Farfesa Usman Yusuf ya bayyana cewa gwamnonin Najeriya ne ke boye gaskiyar hakikanin halin matsin rayuwa da kuncin da ake ciki a kasar nan.

Tsohon shugaban na NHIS ya bayyana cewa gwamnoni ba su tabuka komai duk kuwa da irin makudan kudin da suke karba daga wajen gwamnatin tarayya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng