An Kama Shugaban Falasdinawa a Abuja, Sheikh Makari Ya Yi wa Najeriya Raddi

An Kama Shugaban Falasdinawa a Abuja, Sheikh Makari Ya Yi wa Najeriya Raddi

  • Limamin Babban Masallacin Ƙasa a Abuja, Farfesa Ibrahim Makari, ya yi Allah-wadai da kama shugaban al’ummar Falasɗinawa a Najeriya
  • Rahotanni sun ce jami’an da suka bayyana kansu a matsayin rundunar yaƙi da ta’addanci ne suka yi wannan samame a gidan shugaban a Abuja
  • Har yanzu ba a bayyana dalilin kama shi ko inda aka kai shi ba, lamarin da ya tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin al’ummarsa a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja, – Limamin Babban Masallacin Ƙasa, Farfesa Ibrahim Makari, ya yi magana kan kama shugaban al’ummar Falasɗinawa a Najeriya, Ramzy Abu Ibrahim.

A ranar Juma’a iyalan Abu Ibrahim suka tabbatar da cewa jami’an da suka bayyana kansu a matsayin na rundunar yaƙi da ta’addanci ne suka kama shi.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dauki mataki yayin da masu Mauludi suka fara zagayen gari a Jigawa

Shugaban Falasdinawan Najeriya da Farfesa Ibrahim Makari
Shugaban Falasdinawan Najeriya da Farfesa Ibrahim Makari. Hoto: Prof. Ibrahim Maqari|Abu Jinaan
Source: Facebook

Rahoton Premium Times ya nuna cewa tun bayan faruwar hakan, babu wani bayani daga hukumomin tsaro kan dalilin kama shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya daga ofishin jakadancin Falasɗinawa a Abuja ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa har yanzu suna bin diddigi don samun cikakkun bayanai.

Martanin Farfesa Makar a kan lamarin

Farfesa Ibrahim Makari ya bayyana cewa wannan matakin kama shugaban Falasɗinawa a Najeriya alama ce da ke nuna yiwuwar fara bin manufofin Isra’ila a harkokin tsaron ƙasar.

Malamin ya wallafa a Facebook cewa:

“Kama shi alama ce ta fara bayyana ķudurorin haɗakar biyayya ga manufofin Gwamnatin Isra'ila.
"Kuma mari ne a fuskar Musulman Nigeria da duk masu ƙiyayya da ta'addanci da ake ganawa Falasɗinawa a Gaza.”

Hakan ya ƙara jaddada cewa Musulman Najeriya da sauran masu kishin adalci ba za su yi shiru ba idan ana nuna rashin gaskiya da danniya ga al’ummar Falasɗinawa.

Tarihin Ramzy Abu Ibrahim da aka kama

Kara karanta wannan

Musulunci ya yi rashi, malamin da ya yi limanci a dakin Ka'aba ya rasu

Rahotanni sun nuna cewa Abu Ibrahim ya shafe shekaru da dama yana zaune a Najeriya, inda ake kallonsa a hukumance a matsayin shugaban al’ummar Falasɗinawa a ƙasar.

An sha ganin sa tare da manyan jami’ai da shugabanni a Najeriya, kana ya kasance mai tsayawa tsayin-daka wajen kare muradun Falasɗinawa.

Wasu daga cikin ’yan uwansa sun bayyana zargin cewa kama shi ba zai rasa nasaba da fitowarsa kwanan nan yana sukar hare-haren da ake kai wa ’yan jarida da fararen hula a Gaza ba.

Sai dai duk da haka, wannan ikirari ba a tabbatar da shi daga wata majiya ta hukuma ba a Najeriya.

Rikicin Gaza da tasirinsa a duniya

Lamarin kama Abu Ibrahim na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da samun rahotanni kan hare-haren Isra’ila a Gaza, ciki har da wanda ya rutsa da Asibitin Nasser a Khan Younis.

Rahotanni sun ce aƙalla mutane 15 zuwa 20 ne suka rasu, ciki har da ’yan jarida daga manyan kafafen watsa labarai na duniya.

Har yanzu hukumomin tsaron ƙasa ba su fito da wata sanarwa ba game da kama Abu Ibrahim da aka ce sun yi.

Kara karanta wannan

Makari: An fara ruguza yunkurin hada kai tsakanin malaman Izala da Darika a Najeriya

An yi bore kan alakar Najeriya da Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan Najeriya, musamman Musulmai sun nuna rashin jin dadi kan alakar Najeriya da Isra'ila.

Wasu malaman addinin Musulunci a Kudancin Najeriya sun yi Allah wadai da hakan tare da yin zanga zanga.

A kwanakin baya ne wasu shugabannin Isra'ila suka zo Najeriya tare da ganawa da karamar ministar harkokin wajen kasar da shugabannin Kiristoci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng