Abin Kunya: Amurka Ta Daure Sarkin Najeriya da Ya Sace Naira Biliyan 6.4 na COVID 19

Abin Kunya: Amurka Ta Daure Sarkin Najeriya da Ya Sace Naira Biliyan 6.4 na COVID 19

  • Sarkin Ipetumodu a Osun, Oba Joseph Oloyede, ya samu hukuncin fiye da shekara hudu a kurkukun Amurka saboda laifin karkatar tallafin COVID-19
  • Kotun Amurka da ke Ohio ta kuma umurce shi ya dawo da kudi kimanin Dala miliyan 4.4 tare da kwace wani katafaren gidan da ya mallaka
  • Oloyede ya jagoranci wata makarkashiya da ta yi amfani da sunayen kamfanoni da jama’a wajen satar kudin tallafi da gwamnatin Amurka ta ware

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Kotun Amurka ya yanke wa Sarkin gargajiya daga jihar Osun, Oba Joseph Oloyede, wanda ake kira Apetu na Ipetumodu, hukunci bayan kama shi da sata.

Hukuncin ya biyo bayan shigar da karar da ofishin lauyan gwamnatin Amurka a Ohio ya yi, inda aka tabbatar da cewa ya jagoranci aikace-aikacen bogi domin karɓar tallafi.

Kara karanta wannan

Gwamna ya kara albashi, wasu ma'aikata za su samu rabin miliyan a wata

Sarkin Najeriya da Amurka ta daure.
Sarkin Najeriya da kotun Amurka ta daure. Hoto: Osun Defenders
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa gwamnatin Amurka ta ware tallafin da ya karkatar ne ga ‘yan kasuwa da kungiyoyi a lokacin annobar cutar Corona.

Amurka ta gano satar Sarkin Najeriya

Rahoton ofishin lauyan Amurka ya ce tsakanin Afrilun 2020 zuwa Fabrairun 2022, Sarkin da abokinsa Edward Oluwasanmi suka tura buƙatun bogi don samun rancen tallafin Corona.

An gano cewa Oloyede ya mallaki kamfanoni guda biyar da wata ƙungiya, sannan ya yi amfani da su wajen tura bayanan ƙarya.

A gefe guda, abokinsa Oluwasanmi ya mallaki kamfanoni guda uku da aka yi amfani da su wajen karɓar kuɗin.

Daga cikin abin da suka karɓa, kusan Dala miliyan 1.7 aka samu ta hannun Oloyede, yayin da Oluwasanmi ya samu Dala miliyan 1.2, wanda gabaɗaya ya kai Dala miliyan 4.2 (N6.4bn).

Yadda Sarkin ya kashe kudin Amurka

Tribune ta rahoto cewa bincike ya nuna cewa Oloyede ya yi amfani da wasu daga cikin kudin wajen sayen fili, gina gida da kuma mallakar wata mota mai tsada.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Gwamna ya shirya tsige Sarki Mai Martaba a Najeriya

Haka kuma, ya yi amfani da sunayen wasu abokan cinikinsa wajen neman rance, inda shi kuma ya riƙa karɓar kaso tsakanin kashi 15 zuwa 20 daga abin da suka samu.

Bayan karbar kudin, bai bayyana su ba ga hukumar haraji ta Amurka (IRS) ba, lamarin da ya kara tsananta masa tuhumar zamba da karya a haraji.

Kotun ta tabbatar da cewa Oloyede ya jagoranci aikace-aikacen bogi har guda 38, wanda hakan ya sa aka amince da rancen da ya kai jimillar Dala miliyan 4.2.

Shugaban Amurka, Donald Trump a wani taro
Shugaban Amurka, Donald Trump a wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hukuncin da kotun Amurka ta yankewa Sarki

Abokin hadin gwiwarsa, Edward Oluwasanmi, wanda shi ma ke da shekaru 62 daga garin Willoughby, an yanke masa hukuncin shekara biyu da watanni bakwai a kurkuku a watan Yuli.

An kuma umarce shi ya dawo da fiye da dala miliyan 1.2 da kuma mika kadarorin da ya mallaka daga kudin damfara.

Baya masa daurin sama da shekara hudu, kotun ta umarci Sarkin ya biya fiye da Dala miliyan 4.4, sannan ya sallama gidansa da sauran kadarorin da ya samu daga haramtacciyar hanya.

Hukumomin FBI, IRS da ofishin binciken sufuri ne suka jagoranci binciken tare da kwamitin yaki da damfarar tallafin annobar COVID-19.

Kara karanta wannan

"Ba zai yiwu ba": Minista ya fadi kuskuren da Tinubu zai yi da bai cire tallafin fetur ba

Amurka ta magantu kan albashin Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta yi magana kan wasu matsalolin tattali da suka shafi Najeriya.

Rahoton da kasar ta fitar ya nuna cewa sabon mafi karancin albashin Najeriya na N70,000 ba zai tabuka komai ba.

Amurka ta koka kan yadda lamuran shari'a ke tafiyar hawainiya a Najeriya, inda ta yi zargin cewa ana gaza yanke hukunci a kan lokaci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng