Da Dumi-Dumi: Kotun Amurka Ta Bada Umurnin a Kamo Mata DCP Abba Kyari

Da Dumi-Dumi: Kotun Amurka Ta Bada Umurnin a Kamo Mata DCP Abba Kyari

  • Wata kotu da ke kasar Amurka ta bada umurnin a kamo mata dan sandan Nigeria Abba Kyari
  • Kotun ta umurci FBI su nemo Abba Kyari su gabatar da shi gabanta bisa zarginsa da hada baki da Hushpuppi wurin aikata laifi
  • Takardan kotun ta ce Hushpuppi ya yi amfani da Abba Kyari don kama tsohon abokin laifinsa da rikici ya hada su

Wata kotu da ke Amurka ta bada umurnin a kamo mataimakin kwamishinan yan sanda a Nigeria, DCP Abba Kyari, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

A cewar takardan kotun da Peoples Gazette ta gani, Otis Wright na kotun Amurka na jihar California ta umurci Hukumar Bincike na FBI ta kamo Kyari ta kawo shi Amurka don ya amsa tambayoyi kan rawar da ya taka game da laifin da Ramon Abbbas (Hushpuppi) da abokansa suka yi.

Da Dumi-Dumi: Kotun Amurka Ta Bada Umurnin a Kamo Mata DCP Abba Kyari
Ramon Abbas (Hushpuppi) da Abba Kyari. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

The Punch ta ruwaito cewa Hushpuppi ya ce ya yi amfani da Kyari wurin kama da daure abokin laifinsa, Chibuzor Vincent, bayan Vincent ya yi barazanar fallasa zamba da suka yi wa wani dan kasuwan Qatari.

Kara karanta wannan

Taimakonsa nayi, ban karbi ko sisi ba: Abba Kyari ya kare kansa kan zargin da Hushpuppi yayi masa

A cewar takardan kotun, Hushpuppi ya hada baki da wasu mutane biyar - don damfarar dan kasuwan (aka sakaya sunansa) ta hanyar ikirarin cewa su kwararru ne da ma'aikatan baki da ke neman bashi don gina makaranta a Qatar.

Sai dai, Hushpuppi ya fara farautar Vincent bayan sun samu rashin jituwa kuma ya yi barazanar cewa zai tona damfarar da suka yi wa dan kasuwar na Qatari.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"A cewar takardan kotun, Kyari wanda fitaccen mataimakin kwamishinan yan sandan Nigeria ne, an ce ya shirya yadda aka kama Vincent kuma aka tura shi gidan yari bisa umurnin Abbas, kuma ya aike wa Abbas hotunan kama Vincent. Kyari ya kuma aikawa Abbas lambar asusun banki inda tura masa kudin kama Vincent da daure shi."

Amma, wani shugaba a tawagar yan sanda na sufeta janar, ya yi bayani a shafin Facebook cewa Hushpuppi ya kira ofishinsa ne ya yi korafin cewa wani ya yi barazanar zai kashe shi shekaru biyu da suka gabata.

Kara karanta wannan

DCP Abba Kyari na cikin wadanda na baiwa kudin cin hanci, Shahrarren madamfari Huspuppi

Dan sandan ya ce wanda ake zargi da barazanar shine Vincent, an kuma kama shi amma daga bisani an sake shi bayan an gano tsaffin abokai ne kuma matsalar kudi ta shiga tsakaninsu.

Kyari ya kuma ce bai karbi kudi daga Hushpuppi ba.

Hushpuppi, mai shekaru 37, a cikin takardan kotun da ya rattaba hannu a kai, ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da suka hada da karkatar da kudade, damfara, zamba da sauransu.

Akwai yiwuwar za a iya yanke masa hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari idan kotu ta tabbatar da laifinsa.

Taimakonsa nayi, ban karbi ko sisi ba: Abba Kyari ya kare kansa kan zargin da Hushpuppi yayi masa

A baya, mun ruwaito muku cewa DCP Abba Kyari, ya karyata rahoton cewa ya karbi cin hanci hannun shahrarren dan damfara, Abbas Ramon, wanda aka fi sani da Huspuppi wanda ke kurkukun Amurka yanzu.

Kara karanta wannan

Shahararren ‘Dan 419 a Duniya, Hushpuppi ya amsa laifinsa a kotu, zai tafi gidan yari

Jawabi daga gwamnatin Amurka ya nuna cewa Huspuppi ya lissafa Abba Kyari cikin jerin mutane shida da ya baiwa kudin cin hanci.

Amma a martani kan wannan tuhuma, Abba Kyari da safiyar Alhamis a shafinsa na IG ya ce bai taba tambayar Hushpuppi kudi ba kuma bai karbi kudi hannunsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164