Sarkin Kano, Sanusi II Ya Jagoranci Wasu Shugabannin Duniya zuwa Gidan Buhari
- Ana ci gaba da zuwa yi wa iyalan marigayi Muhammadu Buhari ta'aziyya tun bayan rasuwar tsohon shugaban kasar a watan Yuli, 2025
- Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya jagoranci tawagar shugabannin Fulani na duniya zuwa gidan Buhari a Kaduna
- Wannan ne karo na biyu da Sanusi II ya je gidan Buhari yin ta'aziyya tun bayan dawowarsa Najeriya saboda bai halarci jana'iza ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya sake komawa karo na biyu gidan marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ke Kaduna.
Sarki Sanusi II, Khalifan Tijjaniyya a Najeriya ya raka shugabannin kungiyar Fulani ta duniya zuwa gidan Buhari domin yi wa iyalansa ta'aziyya.

Source: Twitter
Masarautar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ta tabbatar da hakan a wata gajeruwar sanarwa tare da hotuna da ta wallafa a shafin X yau Talata, 26 ga watan Agusta, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rasuwar Buhari da abin da ya biyo baya
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan cikar shugaba Buhari kwanaki 40 da rasuwa, inda aka yi taron addu'o'in sake nema masa gafara da rahamar Allah.
Idan ba ku manta ba, tsohon shugaban kasar ya rasu ne a ranar 13 ga watan Yuli, 2025 a wani asibiti da ke birnin Landan na kasar Birtaniya.
Rasuwar Muhammadu Buhari ta girgiza 'yan Najeriya da shugabanni, inda Gwamnatin Tarayya ta shirya masa jana'izar girmamawa a mahaifarsa, Daura.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da kusan duka mukarrabansa, gwamnoni, yan Majalisa, sarakuna, 'yan kasuwa da dubban yan kasa sun halarci jana'izar Buhari.
Sarki Sanusi II bai je jana'izar Buhari ba
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II na cikin manyan Arewa da ba a gani a wurin jana'izar Buhari ba.
Hakan ta faru ne saboda basaraken ba ya gida Najeriya lokacin da Buhari ya rasu kuma har aka yi maaa sutura aka birne shi bai dawo ba.
Bayan ya dawo Najeriya, Sanusi II ya sa an sauke tutar masarauta domin girmama marigayin, sannan kuma ya je gidansa na Kaduna ya yi wa iyalansa ta'aziyya.

Source: Twitter
Sarkin Kano ya sake komawa gidan Buhari
A karo na biyu Sanusi II ya koma gidan Buhari, inda ya je tare da shugabannin kungiyar Fulani ta duniya da suka zo don jajantawa iyalan tsohon shugaban kasar.
Masarautar Kano ta ce:
"Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, CON, ya jagoranci tawagar Ƙungiyar Fulani ta Duniya zuwa Kaduna don yin ta’aziyya ga iyalan marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, yau Talata, 26 ga Agusta, 2025."
Sarki Sanusi II ya gana da Obasanjo a Legas
A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ziyarci jihar Lagos kuma ya gana da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
An tabbatar da cewa basaraken ya samu rakiyar wasu manya a masarautar ciki har da Waziri, Galadima da Magajin Garin Kano.
Sarki Muhammadu Sanusi II da Obasanjo sun tattauna kan muhimman batutuwa a ganawar da suka yi amma ba a fitar da cikakken bayani ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

