Babu Ruwan Tinubu, Tsohon Shugaban NHIS Ya Fallasa Masu Jawo Matsaloli a Najeriya

Babu Ruwan Tinubu, Tsohon Shugaban NHIS Ya Fallasa Masu Jawo Matsaloli a Najeriya

  • Tsohon shugaban hukumar hukumar NHIS, Farfesa Usman Yusuf ya ce gwamnoni ne kashi 80 cikin 100 na matsalolin Najeriya
  • Farfesa Usman ya ce gwamnoni na karɓar kuɗi mai yawa daga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu amma ba sa yin aikin a zo a gani
  • Yayin da Yusuf ya zargi gwamnoni da karkatar da kuɗin jama’a, Usman ya tabo batun N419bn da aka ce an raba wa talakawa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon shugaban hukumar inshorar lafiyar ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya zargi gwamnoni da jawo matsaloli a Najeriya.

Farfesa Usman Yusuf ya ce gwamnoni na boye wa Shugaba Bola Tinubu gaskiya game da halin tsananin wahalar da ake ciki a Najeriya.

Farfesa Usman Yusuf ya fada wa Tinubu cewa gwamnoni ne ke jawo mafi yawan matsalolin Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu zaune a wajen taro a Abuja, da tsohon shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf a farfajiyar kotu. Hoto: Daniel Bwala
Source: Facebook

"Gwamnoni ne matsalar Najeriya" - Usman Yusuf

Tsohon shugaban NHIS din ya yi sabuwar bankada game da halin da ake ciki a Najeriya a wata hira da aka yi da shi a Trust TV a Abuja.

Kara karanta wannan

'Na yi mulkin gaskiya': Ganduje ya yi zazzafan martani ga Gwamna Abba kan zarge zarge

Farfesa Usman ya ce duk da cewa gwamnoni na karɓar kuɗaɗe masu yawa a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, ba a ga wani abin a zo a gani da suke yi da kuɗin ba.

Ya ce sama da kashi 80 cikin 100 na matsalolin ƙasar gwamnoni ne ke jawo su, saboda sun gaza amfani da albarkatun da aka tanadar wa jama’arsu

“Mai girma shugaban ƙasa, idan su ba za su gaya maka gaskiya ba, to ni ka saurare ni, ni zan fada maka gaskiya cewa yunwa ta addabi 'yan Najeriya
“Duk abin da suke gaya maka ba gaskiya ba ne, kuma gwamnatinka ba ta ɗaukar komai don magance wannan bala’i da ya afka wa mutanenmu a ƙasar da take da yalwar arziki.”

- Farfesa Usman Yusuf.

'Su wa aka raba wa N419bn?" - Farfesa Usman

Yusuf ya kuma yi tambaya kan shirin gwamnatin tarayya na raba kuɗi ga talakawa (CCT), inda ya ce babu wata shaida da ke nuna cewa Naira biliyan 419 da aka ce an raba ta isa ga jama’a.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: NNPCL ya gano hannun kungiyoyin kasashen waje a satar man Najeriya

“Na ji wani minista yana cewa sun raba N419bn a matsayin tallafin kuɗi. Haba, wannan adadi bai kamata ya ba ka mamaki ba? Su waye aka ba?” Farfesa Usman ya tambaya.

Ya ƙara da cewa:

“Shugaba, bayan cire tallafin mai, kowa ya yaba maka. Amma kai kana riƙe da kuɗi a aljihunka, kana jefawa wasu gwamnoni. Sun karɓi kuɗi masu yawa amma babu abin da ake gani a ƙasa.
"Abin da kawai muka shaida suna yi shi ne gantali a duniya, suna gina gadoji da gidaje a ko ina yayin da yunwa ta ke kashe mutanenmu.
Farfesa Usman Yusuf ya ce gwmanoni na karbar kudi daga gwamnatin Tinubu amma ba sa aikin komai.
Shugaba Bola Tinubu (a tsakiya) tare da gwamnonin Najeriya a fadar shugaban kasa, Abuja. Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Usman ya soki gwamnoni kan rike kudin jama'a

Farfesa Yusuf ya jaddada cewa ba shugaban ƙasa ba ne ke da alhakin samar da ayyukan yi, gina makarantu da inganta kiwon lafiya, illa gwamnoni.

Jaridar The Cable ta rahoto Farfesan ya ce:

“Har ma a lokacin Buhari na faɗa cewa gwamnoni ne sama da kashi 80 cikin 100 na matsalolin Najeriya.
"Ba gwamnatin tarayya ba ce za ta samar wa mutane aiki a ƙananan hukumomi, domin gwamnoni ne suka danne haƙƙokin ƙananan hukumomi. Ba fadar shugaban ƙasa ba ce za ta gina makarantu ko asibitoci."

Kara karanta wannan

Makari: An fara ruguza yunkurin hada kai tsakanin malaman Izala da Darika a Najeriya

Tsohon shugaban NHIS din ya ce kokarin Tinubu na ’yantar da kuɗaɗen ƙananan hukumomi daga hannun gwamnoni bai yi wani tasiri ba, domin har yanzu suna riƙe da su.

Kalaman Usman game da kama shi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban hukumar NHIS, Farfesa Usman Yusuf ya yi magana kan kamun da hukumar EFCC ta yi masa.

Farfesa Usman Yusuf ya yi ikirarin cewa hukumar EFCC ta kama shi ne kawai a wani ƙoƙari na gwamnatin Bola Tinubu na rufe bakin masu sukarta.

Sai dai, tsohon shugaban na NHIS ya bayyana cewa ba zai ji tsoro ba domin shi ba irin mutanen da ake rufewa baki ba ne, musamman ta hanyar barazana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com