Ta Faru Ta Ƙare: Hukumar Jiragen Ƙasa Ta Dakatar da Zirga Zirga daga Abuja zuwa Kaduna
- Hukumar jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta dauki mataki kan zirga-zirgar jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna bayan hatsari
- Shugaban hukumar NRC ya tabbatar ana bincike tare da tabbatar daukar tsauraran matakai gane da iftila'in da ya faru
- Kayode Opeifa ya bayyana cewa fasinjoji shida sun samu raunuka amma an ba su kulawa kuma ya ce za a mayar da kudin tikiti
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hatsarin jirgin kasa da ya faru a hanyar Abuja zuwa Kaduna ya daga hankalin al'ummar Najeriya.
Wasu na zargin lamarin ya faru ne sakamakon satar karafunan dogon a wasu wurare daban-daban.

Source: Twitter
An dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa
Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a hanyar Abuja-Kaduna har zuwa wani lokaci, bayan hatsarin da ya faru, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan
NSIB ta gano wasu bayanai kan hatsarin jirgin Kaduna, an ji halin da fasinjoji 6 ke ciki
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manajan Daraktan NRC, Kayode Opeifa, ya sanar da hakan yayin taron manema labarai a Abuja, sa’o’i bayan hatsarin, inda ya ce bincike na gudana.
Opeifa ya bayyana cewa ma’aikatan fasaha na hukumar tare da hukumar NSIB da wasu hukumomi suna gudanar da bincike a wurin hatsarin domin gano matsalar.
Ya karyata jita-jitar cewa jiragen kasan ba su da inganci, ya kuma ce an fara mayar da kudin tikiti ga dukkan fasinjojin da abin ya shafa.
Shugaban NRC ya ce an karɓi wasu daga cikin fasinjojin a tashar Asham da Idu, Abuja, yayin da ake basu kulawa.
A cewarsa, fasinjoji shida sun samu raunuka kadan amma an ba su kulawar da ta dace, ya kara da cewa adadin fasinjojin bai tabbata ba tukuna.

Source: Twitter
Binciken da ake yi kan hatsarin jirgin kasar
Hukumar NSIB ta tabbatar da cewa ta fara bincike kan lamarin, kuma ta ce rahoton farko ya nuna mutane shida ne suka jikkata.
Daraktan Hulda da Jama’a na NSIB, Bimbo Oladeji, ya ce an tura tawaga zuwa wurin hatsarin domin tattara shaidu da tattaunawa da hukumomi.
Hukumar ta ruwaito Darakta Janar, Alex Badeh Jr., yana mika ta’aziyya ga wadanda abin ya shafa, yana mai cewa za a gudanar da binciken gaskiya.
Sanarwar ta ce:
“Ina mika ta’aziyya ga duk wanda ya jikkata. Mun tura masu bincike domin gano ainihin dalilin hatsarin."
Hukumar ta ce binciken zai yi nazari kan abubuwan da suka haddasa hatsarin, tare da ba da shawarwari domin hana faruwar irin haka a nan gaba, cewar Daily Post.
NSIB ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da bayar da bayanai kan cigaban binciken, tare da tallafa wa dukkan fasinjojin da abin ya shafa.
An samu hatsarin jirgin kasan Kaduna-Abuja
Mun ba ku labarin cewa an shiga jimami bayan jirgin kasa da ya taso daga tashar jirgi ta Rigasa, a jihar Kaduna ya yi hatsari a kan hanyar zuwa Abuja.
Wannan na zuwa ne mako guda bayan wani jirgin AKTS dauke da fasinjoji ya samu matsala lokacin da ya baro tashar Kaduna.
A hatsarin na yau Talata, 26 ga Agusta, wani fasinja ya bayyana irin halin da fasinjoji suka shiga lokacin da taragon jirgin suka kife.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
