Bayan Zargin Gwamna da Rike Kuɗin Jama'a, An Dakatar da Ɗan Majalisa na Wata 3

Bayan Zargin Gwamna da Rike Kuɗin Jama'a, An Dakatar da Ɗan Majalisa na Wata 3

  • Majalisar dokokin jihar Anambra ta dakatar da wani dan majalisa da ke shiga intante yana fallasa badakalar kudin mazabun jihar
  • 'Dan majalisar dai ya kasance yana wallafa bayanan kudin da FAAC ke aikawa kananan hukumomi da tambayar inda aka kai su
  • Saboda tone-tonen da yake yi, tare da zarge-zargen da yake yi wa gwamnan jihar, aka cire shi daga dandalin majalisar na WhatsApp

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - Kokarin bankado badakalar kudin mazabu ya jefa dan majalisar mazabar Ayamelum, Hon. Bernard Udemezue a babbar matsala.

A ranar Talata, 26 ga watan Agusta 2025, majalisar dokokin jihar Anambra ta dakatar da Hon. Udemezue na tsawon watanni uku.

Majalisar Anambra ta dakatar da dan majalisa, Bernard Udemezue na watanni 3
Dan majalisar Anambra, Bernard Udemezue yana gabatar da jawabi a zauren majalisa. Hoto: Isi Enyi
Source: Facebook

An dakatar da dan majalisa a Anambra

Jaridar Punch ta rahoto cewa kakakin majalisar Anambra, Somtochukwu Udeze ya sanar da dakatar da Udemezue a zaman majalisar na yau.

Kara karanta wannan

Makinde: Gwamna zai mika ragamar mulki ga mataimakinsa, an ji dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An dakatar da dan majalisar Ayamelum, Hon. Udemezue ne bayan da majalisar dokokin ta kada kuri'a kan bukatar hakan.

Majalisar Anambra na zargin dan majalisar da wallafa wasu bayanai a shafukansa na sada zumunta, wadanda suka kira da "bayanan bata suna."

An zabi Hon. Bernard Udemezue a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Ayamelum a majalisar dokokin Anambra karkashin jam'iyyar PDP.

Laifin me dan majalisar ya aikata?

Rahoto ya bayyana cewa, dan majalisar ya kasance yana bankado wasu bayanai da suka shafi kudin mazabun jihar da ake tura wa daga asusun FAAC.

Hon. Udemezue ya zargi gwamnan jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo da cinye wani kaso na mazabar Ayamelum.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram a yau Talata, dan majalisar ya ce:

"Mazabar Ayamelum tana bin Soludo Naira biliyan 18. Ana tura mana akalla N500m a kowanne wata."

Hade da wannan sako, dan majalisar ya wallafa hoto wanda ya nuna kudin da asusun FAAC ya tura wa kananan hukumomi 21 na jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Duk da ya yi murabus, an dakatar da tsohon shugaban majalisar dokokin Benue

Sakamakon fallasar da ya dade yana yi game da kudaden mazabarsa da yadda yake zargin gwamnati na sama da fadi da su, aka cire Udemezue daga dandalin 'yan majalisar Anambra na WhatsApp.

Udemezue ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa:

"Sun cire ni daga dandalin 'yan majalisar dokoki na WhatsApp. Lallai na cancanci hakan saboda na riga na gama fallasa su."
Dan majalisa ya zargi gwamnan Anambra, Charles Soludo da cinye kudin mazabarsa
Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo yana jawabi a wajen wani taro a Awka. Hoto: @CCSoludo
Source: Facebook

Majalisa ta dauki mataki kan Hon. Udemezue

Bayan abubuwan da ya rika wallafawa, majalisar dokokin Anambra ta yanke shawarar gayyatar Udemezue a zamnta na ranar Talatar makon jiya.

'Dan majalisa, Tony Muobike da ke wakiltar mazabar Aguata 2 ne ya gabatar da kudurin, wandan bulalar majalisa, kuma mai wakiltar Ihiala 1, Jude Ngobili ya goyi baya.

Kakakin majalisa, Udeze, wanda ya jagoranci zaman na ranar Talaya, ya mika lamarin ga kwamitin majalisar kan dokoki, ladabtarwa da alfarma domin yin bincike tare da ba da rahoto a zaman majalisar na yau Talata.

A zaman majalisar na yau Talata ne, majalisar ta yanke shawarar dakatar da Hon. Udemezue na tsawon watanni uku.

'Yan bindiga sun sace 'dan majalisa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu ƴan bindiga dauke da makamai sun sace ɗan majalisar dokokin jihar Anambra, Justice Azuka a Onitsha.

Kara karanta wannan

APC ta dakatar da babban jami'in gwamnati saboda aikata zunubai masu girma

Wani makusancinsa ya ce har yanzu babu wani labari game da inda ɗan majalisar yake tun bayan sace shi yayin da suke jiran kiran 'yan bindigar.

Rundunar ƴan sanda reshen jihar Anambra ta ce tuni dakarunta suka bazama domin ceto shi da kamo waɗanda suka sace ɗan majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com