Yadda ’Ya’yan Hadimin Ganduje 3 Suka Tsira daga Hatsarin Jirgin Kaduna zuwa Abuja
- Salihu Tanko Yakasai ya bayyana yadda 'ya 'yansa uku da 'yan uwansa guda biyu suka tsallake rijiya ta baya a hatsarin jirgin kasa
- Yakasai ya ce tun farko sun shirya shiga jargin kasan da ya yi hatsari kafin daga bisani su sauya shawara zuwa bin hanyar ta mota
- Tsohon hadimin na Abdullahi Ganduje ya ce an daɗe ana korafi kan matsalolin jirgin kasa Abuja-Kaduna amma ba a dauki mataki ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Tsohon hadimin Abdullahi Umar Ganduje ya magantu bayan afkuwar hatsarin jirgin kasa a Najeriya.
Salihu Tanko Yakasai ya yi magana game da hatsarin da ya faru a yau Talata 26 ga watan Agustan 2025 a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Source: Twitter
Yadda 'ya'yan Dawisu suka tsira daga hatsarin jirgi
Dawisu kamar yadda aka fi saninsa ya yi wani rubutu a X ya bayyana yadda wasu daga cikin iyalansa suka tsallake rijiya da baya bayan fasa tafiya a jirgin kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin rubutunsa, Salihu Tanko Yakasai ya ce akwai yayansa uku da yan uwansa biyu da suka yi niyyar yin tafiya a jirgin da ya yi hatsari.
Dawisu ya ce daga bisani sun yanke shawarar biya musu kudin mota domin su yi tafiyar ta hanyar mota ba ta cikin jirgin kasa ba.
Salihu Tanko Yakasai ya ce:
"Inna Lillahi Wa Inna Ilaihirrajiun.
"Yayana uku da yan uwana sun shirya tafiya ta wannan jirgin kasa, daga baya muka yanke shawarar su bi mota.
"Ana yawan korafi kan wannan jirgin kasa amma har yanzu babu wani abin da aka yi kan haka har ya samu matsala.
"Allah ya kare mu ya sa ka da wata rana irin wannan sakaci na Najeriya ya faru da mutum ya Allah."

Source: UGC
Martanin mutane da dama kan rubutun Dawisu
Wasu daga cikin masu amfani da shafukan sadarwa sun bayyana ra'ayinsu game da abin da ya faru inda suke yi masa barka bayan iyalansa sun tsira.

Kara karanta wannan
'Na yi mulkin gaskiya': Ganduje ya yi zazzafan martani ga Gwamna Abba kan zarge zarge
Mafi yawa sun yi wa Dawisu Allah kiyaye kan abin da faru tare da addu'ar Allah ya kara kiyaye wa da kuma fatan samun lafiya ga wadanda abin ya rutsa da su.
Cars Nation suka ce:
"Wannan gaskiya ne oga, komai na Arewa ba shi da inganci."
Ahmed Abubakar:
"Alhamdulillah ga iyalanka, muna addu'ar samun lafiya da kariya ga duk wadanda lamarin ya rutsa da su."
Abdulhalim Danmaliki:
"Subhanallah, Allah ya kara tsare mu baki daya."
Sapientocracy:
"Bari yan Kudu su kula muku da lamarin."
Abu Ammar:
"Dan uwana, Allah shi kara kiyayewa, babu wani dan uwanmu da ya kamata ya sake shiga wannan jirgin, bin hanyar mota ya fi."
Ganduje: Dawisu ya caccaki gwamnatin Tinubu
Kun ji cewa tsohon hadimin Abdullahi Umar Ganduje, Salihu Tanko Yakasai, ya yi magana kan adalci da rabon dukiya a jihohi.
Yakasai ya yi zargin cewa an ware biliyoyin Naira domin ayyuka a jihar Legas cikin shekaru biyu na mulkin Bola Tinubu.
Hakan na zuwa ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan zargin nuna bambanci tsakanin yankunan Najeriya wajen yin ayyuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
