ASUU: Malaman Jami'a Sun Fara Yi wa Gwamnatin Tinubu Zanga Zanga a Fadin Najeriya
- Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta gudanar da zanga-zanga a yau Talata 26 ga watan Agusta, a dukkan jami’o’in kasar
- Malaman jami'ar ta ce tana nuna gagarumin rashin jin daɗinta da sakacin gwamnati wajen aiwatar da bukatun su manyan makarantu
- ASUU ta jaddada cewa tilas gwamnati ta mutunta yarjejeniyar 2009 da sauran alƙawura idan ana son kaucewa sake fadawa cikin yajin aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A yau Talata, 26 ga watan Agusta, 2025, kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta gudanar da zanga-zanga a dukkan jami’o’in kasar.
Rahoto ya nuna cewa an yi zanga zangar ne domin nuna rashin amincewa da yadda gwamnati ke ci gaba da watsi bukatun kungiyar.

Source: Facebook
Wani malami a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Abdelghaffar A. Amoka ya wallafa yadda suka fito zanga zangar a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
'Lokaci ya yi da za a dauki mataki,' ACF ta shiga takaicin yadda ake zubar da jinin 'yan Arewa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun da farko dama ASUU ta bayyana cewa matakin ya nuna gazawar gwamnati wajen daukar matsalolin malaman a matsayin abin da ya dace da muhimmanci.
Magana kan yarjejeniya ASUU ta 2009
ASUU ta jaddada cewa tun daga shekarar 2012 zuwa yau, rikice-rikice tsakanin gwamnati da kungiyar kan samo asali ne daga rashin aiwatar da yarjejeniyar 2009.
The Cable ta rahoto cewa ASUU ta ce yarjejeniyar ta kunshi sharuddan aiki, ‘yancin gudanar da harkoki, kudin gudanarwa da kuma ‘yancin malamai.
Kungiyar ta ce gwamnatin Najeriya na nuna bambanci wajen aiwatar da bangarorin yarjejeniyar, tana barin batutuwa masu mahimmanci ga malamai ba tare da kulawa ba.
Wannan, a cewar ASUU, yana kashe kwarin gwiwa da jajircewar malamai wajen gudanar da aiki a jami’o’in kasar.
Matsalolin malaman jami’a a Najeriya
Kungiyar ASUU ta ce yanayin jami’o’i daban-daban sun nuna cewa malamai suna gudanar da ayyukansu cikin tsananin wahala.
Ta ce ana koyarwa ba tare da albashi mai kyau ba, ana gudanar da bincike a dakunan karatu da dakunan gwaje-gwaje marasa isassun kayan aiki.
ASUU ta yi gargadi cewa wannan rashin dattaku da aka yi wa malamai zai ci gaba da lalata tsarin ilimi da kuma sanya kwararrun malamai hijira zuwa kasashen waje.
Ta bayyana cewa lamarin da zai raunana burin Najeriya na gina tattalin arzikin da ya dogara da ilimi da bincike.

Source: Facebook
ASUU ta yi wa Tinubu zanga zanga
Farfesa Abdelghaffar Amoka ya wallafa hotunan malamai suna gudanar da zanga-zangar yau a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
Malamin da yake sashen kimiyya na jami'ar yana cikin jagororin kungiyar ta ASUU a yau.
Legit Hausa ta hango wasu malaman jami'a na zanga zangar dauke da alluna da ke nuna cewa ba su bukatar bashin da gwamnatin ke son ba su.
An rufe kwalejin ilimi 22 a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta sanar da rufe manyan makaratu har guda 22 a fadin kasar.
Hakan na zuwa ne bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan yaki da takardun bogi a Najeriya.
Wani rahoto da Legit Hausa ta samu ya tabbatar da cewa an rufe kwalejoji 22 ne da ba su cika ka'idojin aiki ba.
Asali: Legit.ng
