Ranar Hausa: Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani yayin da Bikin 2025 Ya Kankama a Daura
Daura, jihar Katsina - Yau Talata, 26 ga watan Agusta, ita ce ta ranar da ake bikin ranar Hausa ta duniya a kowace shekara.
An fara bikin wannan rana ne a shekara 2015 domin tunawa da al'adun Hausa, ci gaban harshen da kuma zamantakewar Bahaushe.

Source: Facebook
Wanene ya kirkiro ranar Hausa ta duniya?
Tsohon ma'aikacin Legit Hausa da BBC Hausa wanda yanzu haka yake aiki da TRT Hausa, Abdulbaki Aliyu Jari ne ya kirkiro ranar Hausa ta duniya a 2025.
Abdulbaki Jari ya fara fafatukar ranar Hausa ta duniya tare da hadin gwiwar wasu abokansa a shafukan sada zumunta, rahoton Daily Trust.
An kirkiro wannan rana ne domin hada duk masu magana da harshen Hausa wuri guda a tattauna kan ci gaban harshen da kuma kalubalen da yake fuskanta a karni na 21.
A cikin shekaru biyu da suka gabata, ana gudanar da bikin Ranar Hausa ta Duniya a fiye da kasashe 20, ciki har da Faransa da Saudiyya.
Bunkasar harshen Hausa a duniya
Abdulbaki Jari ya ce bisa ga binciken baya-bayan nan, harshen Hausa shi ne na 11 a jerin harsunan da aka fi amfani da su a duniya, kuma ana hasashen zai hau matsayi na biyar nan da 2050.
Masu fafutukar wannan rana suna fatan cewa nan gaba za a amince da yaren Hausa a hukumance a ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) da kuma ƙungiyar raya ƙasashen yammacin Afrika (ECOWAS).
A baya-bayan nan sai da hukumar Lafiya ta Duniya watau WHO ta sanya Hausa a cikin harsuna guda uku da ta zaɓa domin yaki da annobar korona a nahiyar Afirka
Ana kallon al'ummar Hausawa a matsayin ɗaya daga cikin ƙabilu masu muhimmanci a yammacin Afirka, da al’adunsu na musamman a faɗin nahiyar da ma sauran ƙasashen duniya.

Source: Facebook
Manufar kirkiro ranar Hausa ta duniya
A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, tsohon editan na Legit Hausa kuma wanda ya kirkiro ranar Hausa, Abdulbaki Jari ya ce za a yi bikin bana a garin Daura.
Abdulbaki, wanda ya dauki bidiyon a gaban fadar sarkin Daura, ya ce ana shirya bikin ranar Hausa ne domin tunatar da muhimmanci harshen Hausa, al'adu da uwa uba hadin kai.
"Rana ba ta karya, yau Talata, 26 ga watan Agusta, 2025 ita ce ranar Hausa ta duniya, kuma ga mu a fadar Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar, CON, fadar Hausa.
"A nan fadar mai martaba za a gudanar da bikin ranar Hausa ta duniya, taro ne da ake yi domin tunatar da mu muhimmancim harshenmu, al'adarmu da uwa uba hadin kan al'ummar mu."
"Ku zo Daura domin ganin tantagaryar al'adar Hausawa da kuma baiwar da Allah ya yiwa Malam Bahaushe daga al'adunsa, harshensa da kuma yanayin zamantakewa.
- Abdulbaki Jari.
Bikin ranar Hausa ya kankama a Daura
A bana an shirya bikin wannan rana a garin Daura da ke jihar Katsina a Arewa maso Yammacin Najeriya. Ana ganin Daura a matsayin tushen Hausa.
Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka bikin ranar Hausa ya kankama a Daura, jihar Katsina, inda manyan mutane daga ciki da wajen Najeriya suka halarta.

Kara karanta wannan
'Lokaci ya yi da za a dauki mataki,' ACF ta shiga takaicin yadda ake zubar da jinin 'yan Arewa

Source: Twitter
Aminiya ta rahoto yadda makada da mawaka ke nuna bajintarsu da kayatar da mahalarta taron da al'adun Hausa iri daban-daban.
Manyan baki daga ciki wda wajen Najeirya sun hallara a kofar fadar Sarkin Daura albarkacin wannan rana mai matukar muhimmanci ga Hausawa.
Daga cikin wadanda suka halarci bikin ranar Hausa a Daura akwai gwamnan Damagaran, Kanar Yosouf Labo da kuma Sarkin Damagaram, Aboubacar Sanda Oumarou.
Bikin ranar Hausa a jami'o'in Najeriya
Haka kuma bikin wannan rana za ta gudana a jami'o'i musamman wadanda ake karantar da harshen Hausa irinsu jami'ar Ahmadu Bello a Zariya.
A bikin wannan shekara, za a karrama Farfesa Dalhatu Muhammad wanda ya bada gagarumar gudumuwa wajen bunkasar harshen a Najeriya.
Sarkin Daura ya koka kan sare itatuwa
A wani labarin, kun ji cewa mai martaba Sarkin Daura ya nuna damuwarsa kan yadda mutane ke sare itatuwaba bisa ka'ida ba a jihar Katsina.
Sarkin ya ce sare itatuwa ba tare da bin ka’idojin da ya kamata ba ya fi ta’addanci saboda barazanar da yake wa muhallin da al'umma ke rayuwa a ciki.
A cewar Mai Martaba Umar Farouk Umar, majalisar masarautar ta dauki sare itatuwa a yankin a matsayin babban laifi saboda hadarinsa ga al’umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


