Jima: An Tunawa Gwamnoni 19 Hanyar da Za Su Samu 'Makudan Kudi' a Arewacin Najeirya

Jima: An Tunawa Gwamnoni 19 Hanyar da Za Su Samu 'Makudan Kudi' a Arewacin Najeirya

  • Jihar Legas na neman shiga gaban Arewa kan harkokin sarrafa fata watau jima bayan kaddamar da wata masa'anta a yankin Mushin
  • Tsohon shugaban NILEST ta kasa, Farfesa Mohammed Kabir Yakubu ya bukaci gwamnonin jihohin Arewa su tashi tsaye su farfado sana'ar jima
  • A cewarsa, Arewa na da dumbin arzikin dabbobi wanda zai iya taimaka mata wajen samar da kudaden shiga ta hanyar bunkasa harkokin fata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Tsohon Shugaban Cibiyar Nazarin Fata da Kimiyyar Fasaha ta Najeriya (NILEST), Farfesa Mohammed Kabir Yakubu, ya yi kira ga gwamnonin Arewa da su tashi tsaye wajen bunkasa harkar sarrafa fatar dabbobi.

Ya ce Najeriya na iya asarar biliyoyin daloli a kudin shiga idan ba a dauki matakin da ya dace game da kasuwancin fata da sarrafa ta ba.

Kara karanta wannan

'Sama da kungiyoyi 1,000,' Gambari ya tono tarin 'yan ta'ddan da ke cikin Afrika

Sana'ar jima.
Hoton sabuwar masana'antar fata da gwamnatin Legas ta bude Hoto: Mustapha Sani Abdullahi
Source: Facebook

Leadership ta ce Yakubu, wanda ya jagoranci kwamitin tsara manufar harkar fata ta kasa, ya bayyana haka ne a cikin wata takarda mai taken: “Dumbin Arzikin Fatar Arewa, Mafarkin Fatar Legas.”

Wannan kalamai nasa na zuwa ne bayan gwamnatin Legas ta kaddamar da masana'antar sarrafa fata, wacce za a rika kera takalma, jakunkuna da sauran kayan da ake yi da fata.

Tsohon shugaban NILEST ya ja hankalin Arewa

Farfesa Mohammed ya ce duk da cewa Legas ba ta kiwon dabbobi, ta bude masana’antar fata a Mushin kuma ana kiyasin za ta samar da kudin shiga har Naira biliyan 387.5 a kowace shekara.

“Arewa na da dabbobi amma babu hangen nesa. Legas ba ta da dabbobi amma tana da jagoranci,” in ji shi.

Ya bukaci shugabannin Arewa musamman gwamnonin jihohi 19 su yi koyi da Legas, yana mai cewa darajar masana’antar fata a duniya ta kai Dala biliyan 400.

Kara karanta wannan

Babu zama: Kwankwaso ya dura Legas bayan ruguza kasuwar Hausawa

Sai dai a cewarsa, nahiyar Afirka tana samar da kashi 30% na fata, amma tana da kashi 6% kacal a bangaren fitar da fatar da aka sarrafa.

Yadda Arewa ke samar da fatar dabbobi

Farfesa Yakubu ya bayyana cewa Morocco na samun fiye da dala miliyan 500 duk shekara daga harkar fata kuma yawancin wannan fata na fitowa ne daga Sokoto.

Yakubu ya tuna cewa a lokacin da yake shugabantar NILEST, ya kafa cibiyoyin koyarwa 23 a fadin kasa kuma ya yi shirin farfado da masana’antun fata da hada kai da kasashen waje.

Ya ce sama da kashi 90% na fatocin da ake samar wa a Najeriya ana fitar da su a danyu ba tare an sarrafa su zuwa wani abin daban ba, rahoton Bussiness Day.

Gwamnonin Arewa.
Hoton gwamnonin Arewaa taron da suka yi a Kaduna Hoto: @GovKaduna
Source: Twitter

Kudin da Najeriya za ta samu daga jima

Ya bukaci a hana fitar da danyar fata, a sabunta wuraren yanka da masana’antun fata, a kafa cibiyoyin masana’antu, kuma a jawo mata da matasa a cikin sana’ar fata.

Yakubu ya yi hasashen cewa Najeriya na iya samun kudaden shiga har zuwa Dala biliyan 4 a shekara nan da 2030.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamna ya kirkiro sababbin sarakuna 3, ya dawo da Sarki kan mulki

"Hakan zai samar da ayyukan yi sama da miliyan biyu. Saboda haka dole Arewa ta tashi daga barci idan har muna son zama jagora a harkar fata a duniya.”

Ruguza kasuwar Hausawa a Legas ta tada kura

A wani labarin, kun ji cewa ruguza kasuwar Hausawa da gwamnatin jihar Legas ta yi ya fara jawo hankalin manyan Arewa.

Jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara jihar Legas, inda ya gana sa shugabannin kaauwar don tattauna matsalar da ta taso da yadda za a magance ta.

Kasuwar, wacce aka kafa tun a shekarar 1979 ta kasance cibiyar kasuwanci ta Hausawa a Kudancin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262