Babu Zama: Kwankwaso Ya Dura Legas bayan Ruguza Kasuwar Hausawa
- Gwamnatin Jihar Legas ta rusa kasuwar Alaba Rago tare da masallatai sama da 40 da shaguna 3,000, abin da ’yan Arewa suka ce ya janyo musu asarar mai yawa
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da shugabannin ’yan Arewa a Legas domin jin korafinsu da kuma neman hanyoyin magance matsalolin da suka taso
- A daya bangaren, wasu 'yan gwagwarmaya a Arewa sun ce za su tafi Legas da lauyoyi da masana domin bin diddigin lamarin tare da kare muradun al’ummarsu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas - Rusau da aka yi wa kasuwar Alaba Rago a Legas ta tayar da kura mai yawa tsakanin ’yan Arewa da gwamnati.
Kasuwar aka kafa tun a shekarar 1979 ta kasance cibiyar kasuwanci ta Hausawa a Kudancin Najeriya.

Source: Facebook
Rahoton Aminiya ya nuna cewa lamarin ya shafi dubban shaguna da masallatai da dama kuma ya jefa al’ummomin Arewa cikin babbar damuwa da kuma neman diyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar shugabannin kasuwar, hasarar da al’ummar Hausawa suka tafka ta kai sama da Naira biliyan 20, lamarin da suka ce ya shafi rayuwar dubban iyalai da ke rayuwa a jihar.
Domin fahimtar matsalolin da suke fuskanta, jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya gana da shugabannin kasuwar a Legas.
An rusa kasuwar Hausawa a Legas
’Yan kasuwar sun bayyana cewa an rusa shaguna 3,000 da suka gina tsawon shekaru cikin kankanin lokaci.
Bugu da ƙari, sama da masallatai 40 da suka kasance wuraren ibada na al’umma sun lalace a sanadiyyar rushe-rushen. A cewarsu, hakan ya haifar da asara ta fiye da Naira biliyan 20.
Sun ce tun bayan rusau din, dubban iyalai sun rasa wuraren samun abincin yau da kullum, abin da ya haddasa talauci da rudani a cikin al’umma.

Kara karanta wannan
'Ka dawo gida da gaggawa: An buƙaci Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci a jihohin Arewa 2
Shugabannin kasuwar sun yi kira da a ba su wuraren kasuwanci domin komawa harkokinsu ba tare da tsangwama ba.

Source: Facebook
Kwankwaso ya gana da 'yan kasuwar
Legit Hausa ta ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya karɓi tawagar shugabannin kasuwar karkashin jagorancin Alhaji Hussaini a masaukinsa da ke Legas.
A yayin taron, ya ce yana sane da irin matsalolin da al’ummar Hausawa ke fuskanta a Legas, kuma ya jaddada cewa zai yi iya ƙoƙarinsa wajen ganin an samu sauƙi.
Hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a X cewa tattaunawar ta mayar da hankali kan gano matsalolin da suka taso da kuma neman hanyoyin magance su.
Lauyoyin Arewa za su kai ziyara Legas
Lauya Hamza Nuhu Dantani ya bayyana cewa tawagar ’yan Arewa za ta je Jihar Legas domin bin diddigin lamarin tare da gano sahihin abin da ya faru.
Ya wallafa a Facebook cewa za su yi tafiya tare da Abba Hikima da Dan Bello domin kare mutanen Arewa da suka yi asara.
An koka kan kafa kamfani a Legas
A wani rahoton, kun ji cewa hadimin tsohon shugaban APC na kasa, Salihu Tanko Yakasai ya yi magana yayin da za aka kafa kamfani a Legas.
Rahotanni sun nuna cewa matar shugaban kasa ce ta ziyarci jihar domin kaddamar da kamfanin hada takalma, jakunkuna da sauransu.
Salihu Tanko Yakasai ya koka da cewa a Arewa ne ya kamata a samu irin kamfanin domin a yankin ake samar da fata mai yawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

