2027: Jihohin Kudu na Jan Ragamar Rajistar Katin Zabe, na Arewa Sun Biyo Baya

2027: Jihohin Kudu na Jan Ragamar Rajistar Katin Zabe, na Arewa Sun Biyo Baya

  • Hukumar INEC ta ce mutane 1,379,342 ne suka kammala rajistar farko ta yanar gizo a cikin mako guda kacal daga 18 zuwa 24 ga watan Agusta
  • Mata sun fi yawa da kashi 52.04%, yayin da matasa ‘yan shekaru 18 zuwa 34 suka kai sama da kashi 62.3% na masu rajista
  • Osun ta fi sauran jihohi da masu rajista da mutane 393,269, sannan Lagos ta biyo baya da 222,205, yayin da Ebonyi ta fi karanci da mutane 261 kawai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar Zabe ta INEC ta bayyana cewa sama da mutum miliyan 1.3 ne suka kammala rajistar farko ta yanar gizo a cikin mako guda na fara aikin rijistar masu kada kuri’a.

Rahoton hukumar ya nuna cewa tsakanin ranar 18 zuwa 24 ga watan Agusta 2025, an samu sahihan masu rajista 1,379,342.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Sarkin da ya 'kunyata' Najeriya a Amurka

Shugaban hukumar INEC yana magana yayin wani taro a Abuja
Shugaban hukumar INEC yana magana yayin wani taro a Abuja. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

A sakon da ta wallafa a X, INEC ta ce hakan ya nuna sha’awar jama’a wajen shirye-shiryen kada kuri’a a babban zabe mai zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin bayanai da ilimantar da masu kada kuri’a, Sam Olumekun ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Bambancin jinsi da shekarun masu rajista

Cikakken bayani ya nuna cewa daga cikin masu rajistar:

  • 661,846 maza ne (47.96%)
  • 717,856 mata ne (52.04%)

Mafi yawansu matasa ne masu shekaru 18 zuwa 34 da adadinsu ya kai 860,286 (62.37%). Haka kuma, dalibai sun kai 374,534 (27.15%).

INEC ta bayyana cewa adadin mutane masu bukata ta musamman da suka yi rajista sun kai 27,089, wanda ya kai 1.96%.

Osun ta fi kowa yawan masu rajista

A cikin rahoton jihar, Osun ta samu nasarar jan ragamar yawan masu rajista da mutane 393,269, (28.5%), wanda ya sanya ta fi kowa yawan masu rajista a yanzu.

Kara karanta wannan

Kudin fansa: 'Yan bindiga sun dauke mutum 4700, an ji biliyoyin da aka rasa a shekara 1

Jihar da ta biyo baya da Osun, ita ce Lagos da mutane 222,205 (16.1%), sai Ogun da ta zamo ta uku da mutane 132,823 (9.6%). Babban birnin tarayya (FCT) ya zamo na hudu da mutane 107,682.

Jihohin da suka fi mutane kadan wajen rajista su ne Ebonyi (261), Imo (481), Enugu (484), Abia (772) da Taraba (2,395).

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmud Yakubu
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmud Yakubu. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

A Arewa, Kaduna ta samu mutane 61,592, Kogi 58,546 da Kebbi 35,009. A Arewa maso Gabas, Borno ta kai 21,045, yayin da Yobe ta samu 34,888, Kano ta samu mutane 10,166 kacal.

Me ya jawo yawan rajista a Osun?

Masana sun alakanta yawan rajistar da aka samu a Osun da zabukan gwamna da ake sa ran gudanarwa a 2026, wanda ita da Ekiti, ke zama manyan fagen gwagwarmaya kafin 2027.

Hakan na nuna yadda al’ummar jihar ke nuna azama wajen shiryawa domin kada kuri’a a zabe mai zuwa.

Legit ta tattauna da Abdulganiyyi Umar

A tattaunawa da Legit Hausa, Abdulganiyyi Umar ya ce bai samu wata tangarda ba a lokacin da ya yi rajista da INEC.

Ya bayyana cewa:

"Na yi rajista ne domin na kada kuri'a. Kuma ban samu wata tangarda ba a lokacin da na yi rajista."

Kara karanta wannan

INEC: An bayyana jihar da ta fi ko ina kokari, mutane miliyan 1.3 sun yi rajistar katin zabe

"Sai dai da na koma gida muna gwadawa an ce min an samu matsala wajen saka hoto."

An fara rajistar masu kada kuri'a a jihohi

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta fara rajistar masu kada kuri'a a jihohin Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan hukumar INEC ta fara rajistar masu kada kuri'a ta yanar gizo a makon da ya wu ce.

Biyo bayan lamarin, hukumar zaben ta bayyana matakan da 'yan Najeriya ya kamata su dauka domin ganin sun yi rajista cikin sauki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng