Wata Sabuwa Gwamna Ya Kirkiro Sababbin Sarakuna 3, Ya Dawo da Sarki kan Mulki
- Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo ya kudiri aniyar inganta ayyukan sarakunan gargajiya domin kawo ci gaba ga al'umma
- Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu na Kogi, Barista Salami Ozigi Deedat ne ya sanar da hakan a Lokoja
- Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Kogi ta dawo da Onu Ife na Omala, Mai Martaba Boniface Musa wanda aka dakatar a kwanakin baya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Gwamnatin Kogi karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Usman Ododo ta kirkiro sababbin sarakuna uku a fadin jihar da ke Arewa ta Tsakiya.
Gwamnatin ta Kogi ta ɗauki wannan matakin da nufin ƙarfafa masarautun gargajiya da kuma fadada harkokin mulki ta yadda zai isa ga jama'a.

Source: Twitter
Wannan na daga cikin manufofin gwamnatin Gwamna Usman Ododo na kawo sauyi a tsarin shugabancin al’umma, kamar yadda The Nation ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, Barista Salami Ozigi Deedat, ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Lokoja.
Ya ce an amince da kirkiro sababbin sarakunan ne a taron majalisar zartarwa ta jihar da aka gudanar a Lokoja, babban birnin jihar, a ranar Juma’a.
Gwamnatin Kogi ta kafa sababbin masarautu 3
Ya ce sababbin sarakunan sun haɗa da Ohiekura na Osara, Ohireba Anebira na Lokoja, da kuma Ohi na Eganyi wanda daga yanzu za a kira shi Ohi na Ajaokuta.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa Ohi na Ajaokuta shi ne zai rike matsayin Shugaban Majalisar Sarakunan Karamar Hukumar Ajaokuta.
Ya ce matakin na cikin shirin gwamnati na ƙarfafa tsarin mulki, kare al’adun gargajiya, da ba sarakuna damar taka rawa wajen samar da ci gaba da zaman lafiya a ƙananan hukumomi.
Gwamna Ododo ya dawo da Sarkin Omala
A wani lamari mai alaƙa, Majalisar Zartarwa ta jihar Kogi ta sanar da dawo da Onu Ife na Omala, Mai Martaba Boniface Musa, wanda a baya aka dakatar da shi.

Kara karanta wannan
Jima: An tunawa gwamnoni 19 hanyar da za su samu 'makudan kudi' a Arewacin Najeirya
An ce dawo da shi ya biyo bayan nadamar da ya nuna da kuma neman afuwa kan wasu ayyukan da suka sabawa ka’ida da suka kai ga dakatarwa da shi.
Basaraken shi ne shugaban majalisar sarakunan gargajiya na karamar hukumar Omala a jihar Kogi, cewar rahoton The Guardian.
Barista Deedat ya yi kira ga sauran sarakuna da su yi aiki tare da gwamnatin jihar Kogi don kawo ci gaba mai amfani a yankinsu.

Source: Facebook
Kudirin gwamnatin Kogi kan sarakuna
Ya bayyana cewa gwamnatin Ododo na da kudurin ganin an ba sarakuna matsayin da ya dace wajen gudanar da harkokin mulki da kuma kawo ci gaba a cikin al’ummomi.
“Wannan gwamnati za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen kare martabar masarautun gargajiya, kawo ci gaba, da tabbatar da zaman lafiya a jihar Kogi," in ji Deedat.
Tsohon gwamnan Kogi ya gana da 'yan Majalisa
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya umarci yan Majalisar dokokin jihar su bi Gwamna Ahmed Ododo sau da kafa.
Yahaya Bello ya jaddada bukatar majalisar ta goyi bayan duk wasu kudurori da gwamnatin Ododo za ta kawo gaban majalisar jihar Kogi.
A wani faifan bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, Bello ya umarci yan Majalisar su zauna ƙasa a lokacin da suka kai masa ziyara, hakan ya jawo sukar jama'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
