Mutane Za Su Gwabza da 'Yan Bindiga a Katsina, 'Dan Majalisa Ya Saye Makamai

Mutane Za Su Gwabza da 'Yan Bindiga a Katsina, 'Dan Majalisa Ya Saye Makamai

  • Ɗan majalisar Katsina, Abubakar Muhammad Total, ya ce ya sayawa mazabarsa makamai domin kare kansu daga hare-hare
  • Ya bayyana cewa an kaddamar da shirin a Funtua, inda ya haɗa mazauna yankin da ‘yan sa-kai domin samun horo
  • 'Dan majalisar ya ce matakin ba wai cin mutuncin jami’an tsaro ba ne, illa dai taimakawa kafin isowarsu a lokutan hari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina – Ɗan majalisar jihar Katsina mai wakiltar mazabar Funtua, Abubakar Muhammad Total, ya dauki matakin sayawa mutanensa makamai.

Rahotanni sun nuna cewa ya saye makaman ne domin su kare kansu daga hare-haren ‘yan ta’adda da suka addabi yankin.

Hon. Abubakar Muhammad Total da ke wakiltar Funtua a Katsina
Hon. Abubakar Muhammad Total da ke wakiltar Funtua a Katsina. Hoto: Funtua Oline Reporters
Source: Facebook

A hirar da ya yi da RFI Hausa, ya ce mataki wani ɓangare ne na aikin raya mazaba, inda jama’a su ka nemi agajinsa bayan shafe lokaci suna fafatawa da ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: NNPCL ya gano hannun kungiyoyin kasashen waje a satar man Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An saya wa mutane makamai a Katsina

'Dan majalisar ya ce makaman da ya saya an raba su ne ga kowace gunduma domin kare kanta, kuma an kaddamar da shirin ne a Funtua.

Ya ƙara da cewa, ya haɗa mazauna yankin da ‘yan sa-kai domin samun horo da dabarun yaki kafin jami’an tsaro su isa wajen.

Ya jaddada cewa ba wai yana nuna gazawar jami’an tsaro ba ne, sai dai domin ‘yan ta’adda su kan shigo daga waje cikin gaggawa, su hallaka mutane kafin jami’an tsaro su iso.

Don haka ya ce wannan mataki zai taimaka wajen tsaida hare-haren kafin isowar jami’an tsaro zuwa yakunan Funtua.

Batun sulhu da ‘yan ta’adda a Funtua

Game da yiwuwar sasanci, Abubakar Total ya ce mutanensa ba su da adawa da sulhu muddin hakan zai kawo zaman lafiya.

Amma ya nuna shakku kan dorewar yarjejeniya, ganin yadda sau da dama aka samu rikicewa bayan tattaunawa.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya kara rubuta littafi, ya fallasa aika aikar alkalai a Najeriya

Sai dai ya bayyana cewa sayen makamai ba zai haifar da wata matsala ba, domin an yarda da mutanen da aka bai wa makaman kuma an tsara tsari na kare kai ne kawai.

Ya ce mutanen yankin ba su yi wa ‘yan ta’adda wani laifi ba, don haka babu wani laifi idan sun kare kansu da makamai.

Mutane suna gwada bindigogin da aka saya musu a Funtua
Mutane suna gwada bindigogin da aka saya musu a Funtua. Hoto: Funtua Online Media Reporters
Source: Facebook

Jama'ar Funtua sun yi murna

Ɗan majalisar ya bayyana cewa jama’ar Funtua sun karɓi wannan mataki cikin murna da godiya, inda ya bayyana shi a matsayin “somin tabi” ga abin da zai biyo baya.

Ya ce zai ci gaba da sayen makamai domin tabbatar da cewa ‘yan ta’adda sun fahimci cewa jama’a ba za su sake zama shiru ba.

Total ya kara da cewa yana shiga damuwa a duk lokacin da ya samu labarin an kai hari a mazabarsa.

Ya bukaci jama’a da su dage da addu’a tare da goyon bayan shirin domin a samu nasarar shawo kan matsalar tsaro a jihar Katsina.

An kama mai safarar makamai a Anambra

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta kama wani tsoho mai bisa zarginsa da hannu a safarar makamai.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Shugaban Boko Haram, Bakura ya karyata labarin kashe shi

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa mutumin ya amsa laifin cewa yana da hannu a laifin da ake zarginsa da shi.

Rundunar ta jaddada cewa za ta cigaba da bincike domin gano sauran mutanen da ya ke alaka da su a jihar Anambra.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng