INEC: Abubuwan Sani game da Rijistar Zabe da Aka Fara a Kananan Hukumomi 774

INEC: Abubuwan Sani game da Rijistar Zabe da Aka Fara a Kananan Hukumomi 774

  • An fara rijistar zabe ta zahiri a ofishohin INEC da ke kanann hukumomi 774 a fadin Najeriya daga yau Litinin, 25 ga watan Agusta, 2025
  • A wata sanarwa da INEC ta fitar, ta bayyana abubuwan da ya kamata yan Najeriya su sani game da a rijistar zabe da aka fara wannan karo
  • INEC ta ce tana maraba da wanda ya cika sharuddan kada kuri'a domin yi masa rijista, sannan za a ba da dama gamsu son sauya rumfunan zabe

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bude sabon zangon rijistar masu kada kuri’a a zahiri a fadin ƙasar nan daga yau, Litinin, 25 ga Agusta, 2025.

Wannan mataki ya biyo bayan rijistar ta yanar gizo da aka fara a ranar 18 ga wannan wata na Agusta, 2025.

Kara karanta wannan

Kano: Jami'an NDLEA sun cafke matashi da tramadol 7,000 daga Legas

Shugaban hukumar zabe INEC, Farfesa Mahmud Yakubu.
Hoton shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmud Yakubu da katunan zabe a gefe Hoto: @INECNigeria
Source: Facebook

Hakan dai na kunshe ne a wata sanarwa da hukumar INEC ta wallafa a shafinta na X da safiyar yau Litinin.

Ta bayyana cewa masu rijistar za su rika aiki daga karfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana, daga ranar Litinin zuwa Juma’a na kowane mako a ofisoshin INEC na ƙananan hukumomi.

Bugu da kari, hukumar INEC ta tabbatar da cewa yan Najeriya za su iya zuwa su yi rijista a wasu cibiyoyi da aka ware musamman don wannan aiki.

Legit Hausa ta tattaro maku abubuwan da ya kamata ku sani game da rijistar zabe a Najeriya.

An bude yin sabuwar rijistar zabe

Hukumar INEC ta bayyana cewa ta bude kofar yi wa sababbin masu kada kuri’a da suka kai shekaru 18 da haihuwa rijista, wadanda ba su taba yin rajistar zabe ba

Haka zalika, wadanda suke son maye gurbin katin kada kuri’a (PVC) da ya ɓace ko ya lalace, za su iya zuwa wuraren rijistar domin shigar da bukatunsu.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya kusan 5,000 na kokuwar samun gurbin aiki 98 a Taraba

Canza rumfar zabe a Najeriya

Haka nan, INEC ta ce za a ba da dama ga masu son canza rumfunan zabe zuwa sabon wuri, sabunta bayanansu ko kuma gyara kuskuren da aka samu a PVC dinsu.

INEC ta kuma tunatar da cewa duk wanda ya riga ya fara rajista ta yanar gizo ana bukatar ya ziyarci ofisoshin hukumar na jiha ko ƙaramar hukuma domin kammala rajistarsa.

Katunan zaben yan Najeriya.
Hoton katin zaben da ake baiwa duk wanda ya yi rijista Hoto: INEC Nigeria
Source: Getty Images

INEC ta yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya da suka cancanta da su yi amfani da wannan dama domin tabbatar da cewa sun shiga cikin jerin masu kada kuri’a.

Ta jaddada cewa yin rajista da mallakar katin zabe watau PVC shi ne mataki na farko wajen tabbatar da ana sauraron muryar kowa a tsarin dimokuradiyya.

INEC za ta bar fursunoni su kada kuri'a

A wani labarin, kun ji cewa hukumar INEC ta bayyana kudirinta na bai wa fursunoni damar kada kuri'a kamar kowane dan kasa a zabukan Nanjeriya.

Kara karanta wannan

'Da 'yar matsala,' An fara magana kan bai wa fursunoni damar yin zabe daga magarkama

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hankalinsu ya karkarta wajen tabbatar fursunoni sun yi zabe kamar yadda doka ta tanada.

Ya ce hakkin kada kuri’a hakki ne na ɗan adam wanda bai kamata a hana kowanne ɗan ƙasa ba, ciki har da waɗanda ke cikin gidajen gyaran hali.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262