Sheikh Yakubu Musa: Yadda Jagoran Izala Ya Yi Mu'amala da Ibrahim Inyass

Sheikh Yakubu Musa: Yadda Jagoran Izala Ya Yi Mu'amala da Ibrahim Inyass

  • Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina ya bayyana cewa ya gana da Sheikh Ibrahim Inyass a Najeriya fiye da sau daya
  • Malamin ya bayyana cewa ya taba ba da tarihin alakarsa da Sheikh Ibrahim Inyass ga wani Shehin Darika a can baya
  • Yakubu Musa ya kasance dan Darikar Tijjaniyya kafin daga bisani ya koma tafiyar kungiyar Izala a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Daya daga cikin manyan malaman Izala a Najeriya, Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina ya bayyana irin kusancin da ke tsakaninsa da jagoran Tijjaniyya, Sheikh Ibrahim Inyass.

A yayin da yake bayani, Sheikh Yakubu Musa ya ce ya hadu da Sheikh Inyass fiye da sau daya a Najeriya, inda suka tattauna tare da gaisawa da juna.

Kara karanta wannan

Da gaske an yi wa Sheikh Jingir ihu a Abuja? Izala ta fadi abin da ya faru

Malam Yakubu Musa da Sheikh Ibrahim Inyass
Malam Yakubu Musa da Sheikh Ibrahim Inyass. Hoto: Jibwis Nigeria|Adamu Babayayi
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da Sheikh Yakubu Musa ya yi ne a wani bidiyo da shafin Jibwis Nigeria TV ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya yi hirar ne da fitaccen 'dan jaridar nan Malam Sani Musa Matankari Magawata.

Alakar malamin Izala da Sheikh Inyass

A yayin wata hira da aka yi da Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina, ya nuna cewa ya yi alaka da Sheikh Ibrahim Inyass, inda ya ce:

“Mutuminmu ne.”

Ya kara da cewa ko a lokacin da wani babban Shehin Darika ya ziyarce shi, ya ba shi labarin alakarsa da jagoransu, sai ya ce ya ba shi amsa da cewa:

"Ai wallahi da a cikinsu na ke, da ziyara za a ta kawo mani ana diban albarka.

Tarihin Sheikh Yakubu Musa Hassan

A wata hira da aka yi da shi da BBC Hausa, Sheikh Yakubu Musa, wanda aka fi sani da Sautus Sunnah, ya ce ya fito ne daga garin Gwaram a Jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

Tsakanin Assadus Sunnah, Asada waye mai gaskiya? Dan Sadiya ya magantu kan sulhu

Ya ce ya fara karatun addini tun daga wajen mahaifinsa, kafin daga bisani ya karanci Alkur’ani da ilimin Musulunci a jihar Kano.

Bayan haka ya ci gaba da zurfafa karatu a garin Jos, inda ya kara kwarewa a fannoni daban-daban na ilimi.

Shehin malamin yana daga cikin manyan jagororin Izala kuma shi ne shugaban kwamitin amintattu na JIBWIS.

Shugaban kungiyar Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau
Shugaban kungiyar Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau. Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

BBC ta wallafa cewa Sheikh Yakubu Musa ya shiga jerin musulmai 500 mafi tasiri a duniya a mujallar Muslim 500, wanda ya kara bayyana irin matsayinsa a duniya baki daya.

Yakubu Musa ya taba yin Darika

A baya, Sheikh Yakubu Musa ya kasance cikin Darikar Tijjaniyya, inda ya koyi ilimi da koyarwar sufanci.

Sai dai daga bisani ya yi hijira zuwa tafarkin Izala bisa tasirin koyarwar malaman da ya hadu da su.

Ya bayyana cewa sauya matsayi daga Darika zuwa Izala ya ba shi nutsuwa da farin ciki, domin ya koma tsantsar koyarwar Alkur’ani da Sunnah.

Wanene Sheikh Ibrahim Inyass?

Sheikh Ibrahim Inyass ya kasance babban malamin Musulunci kuma jagoran Darikar Tijjaniyya da ya fito daga Afrika.

Kara karanta wannan

Tsohon ministan Buhari ya yi magana game da mulki, 'yan adawa da halin da APC take ciki

An haife shi a Senegal, inda ya yi karatu karkashin mahaifinsa Sheikh Abdoulaye Niass, wanda shi ma shahararren malami ne.

Malaman Darika sun gana da Buni

A wani rahoton, kun ji cewa tawagar Darikar Tijjaniyya ta gana da gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe.

A yayin ziyarar, Sheikh Ibrahim Shehu Dahiru Bauchi ya ce sun ziyarci Yobe ne domin yin wani bikin Mauludi.

Ya kara da cewa tawagar ta hada da manyan jagororin Darikar Tijjaniyya daga Najeriya da wasu kasashen Afrika.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng