Makari: An Fara Ruguza Yunkurin Hada kai tsakanin Malaman Izala da Darika a Najeriya

Makari: An Fara Ruguza Yunkurin Hada kai tsakanin Malaman Izala da Darika a Najeriya

  • Dr Aliyu Muhammad Sani ya ce haɗin kan Musulmi nau’i biyu ne kawai da shari’a ta yarda da su, babu wani na uku da ya wuce su
  • Ya yi suka kan sabon kiran da ake yi na a daina kafirta masu aikata bidi’a, shirka da kalaman kafirci a Najeriya
  • Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya ce wannan kira na haɗin kan yaudara ce domin aƙalla yana nufin dakile ci gaban tafarkin Sunna

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Malaman Musulunci a Najeriya sun fara nuna rashin jituwa kan wani sabon shiri na haɗa kan Musulmi da Farfesa Ibrahim Makari ya fito da shi.

Shirin dai na neman kawo ƙarshen rikice-rikicen da ake samu tsakanin kungiyoyin Musulunci musamman kan batun kafirta wasu mutane masu ra’ayi dabam.

Kara karanta wannan

An nemi Amurka da Isra'ila su sa baki a 'tsaron' Najeriya domin sakin Nnamdi Kanu

Farfesa Makari yayin ganawa da Sheikh Gumi, wasu malamai yayin taron hada kan Musulmi
Farfesa Makari yayin ganawa da Sheikh Gumi, wasu malamai yayin taron hada kan Musulmi. Hoto: Prof. Ibrahim Makari
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a Facebook, Farfesa Masur Sokoto ya bayyana wannan yunƙuri a matsayin barazana ga tafarkin Sunna da kuma ingantacciyar fahimtar addini.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sukar batun hadin kan Musulmin Najeriya

A cewar Dr Aliyu Muhammad Sani, Shari’a ta fayyace nau’ukan haɗin kan Musulmi guda biyu kacal.

Malamin ya wallafa a Facebook cewa na farko shi ne ƙarƙashin shugabanci na Musulmi mai mulki, ko dai shugaban ƙasa ne ko kuma shugaban daular Musulunci.

Na biyu kuwa shi ne haɗin kai a bisa igiyar Allah da tafarkin Annabi Muhammad (SAW) tare da Sahabbansa, wato tafarkin Sunna.

Malamin ya ce duk abin da ya wuce waɗannan nau’ukan biyu, to yana iya zama maslaha ta duniya kawai ba ta Shari’a ba.

Hadin kai da ba za su karbu a musulunci ba

Malamin ya ce kiran da ake yi yanzu na cewa a daina kafirta masu zuwa kaburburan waliyyai, masu yin addu’a ga imamai ko shehuna ba zai yi wu ba.

Kara karanta wannan

An kama shugaban Falasdinawa a Abuja, Sheikh Makari ya yi wa Najeriya raddi

Ya kara da cewa haduwa da masu yin fassarori marasa daidaito ga hadisai, tamkar hanyar ba da kariya ga kafirai ne a cikin rigar Musulunci.

Ya ce hakan zai iya zama wata dabara ta amfani da kalmar gaskiya domin ɓata tafarkin addini da kuma rusa tushe na yakar shirka da bidi’a.

Martanin Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto

A nasa bangaren, Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya bayyana cewa wannan yunƙurin haɗin kan da ake tallatawa ba komai ba ne illa yaudara ga malamai da mabiyan tafarkin Sunna.

Ya ce Najeriya na cikin wani zamani na fitina inda ake ƙoƙarin dakatar da ci gaba da nasarorin da Allah ke baiwa tafarkin Sunna.

Don haka Farfesa ya yi gargaɗi cewa kar malamai su amince da abin da zai iya cutar da akidar Musulunci.

Legit ta tattauna da Malam Manga

Malam Manga Adamu Hamza ya bayyanawa Legit cewa akwai bukatar sake nazari kan maganar hadin kai da ake tattaunawa a kansa.

Ya ce:

"Akwai bukatar a fahimci hakikanin batun da ake so a hadu a kan shi. A kan akida za a hadu ko a kan wani lamari na duniya ko na kasa kamar rashin tsaro?"

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: NNPCL ya gano hannun kungiyoyin kasashen waje a satar man Najeriya

"Waye ke jagorantar kungiyar malamai da ke son hadin kan? Dama akwai kungiyar ne ko yanzu aka kawo ta?"

Malam Manga ya ce samun gamsasshen bayani kan tafiyar hadin kan zai taimaka wajen fahimtar manufarta.

Farfesa Mansur Sokoto da ya soki yunkurin hada kai na Makari
Farfesa Mansur Sokoto da ya soki yunkurin hada kai na Makari. Hoto: Mansur Sokoto
Source: Facebook

Izala ta kare Sheikh Sani Jingir

A wani rahoton, kun ji cewa jami'in yada labaran kungiyar Izala, Ibrahim Maina Muhammad ya musa cewa an yi wa Sheikh Sani Yahaya Jingir ihu a Abuja.

Ibrahim Maina ya yi magana ne bayan yada jita jitar cewa masu sauraro sun yi wa malamin ihu a lokacin da ya ke wa'azi.

Izala ta ce babu kamshin gaskiya a cikin labarin kwata kwata, kuma an yada shi ne domin bata suna ga shugaban malamanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng