Dangote da 'Yan Kasuwa Sun Fitar da Sabon Farashin Man Fetur a Najeriya

Dangote da 'Yan Kasuwa Sun Fitar da Sabon Farashin Man Fetur a Najeriya

  • Kamfanonin Dangote, Aiteo da AA Rano sun daidaita farashin litar man fetur daga N821 zuwa N823 a Najeriya
  • Masana sun bayyana cewa wannan sauyi ya samo asali ne daga hauhawar farashin danyen mai a kasuwar duniya
  • Rahotanni sun nuna cewa farashin gidajen mai bai sauya ba tukuna, amma ana iya ganin karin farashi a makon nan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Sabon sauyi ya bayyana a fannin man fetur a Najeriya bayan da kamfanonin Dangote, Aiteo da AA Rano suka sanar da karin farashi daga N821 zuwa N823.

Bincike ya nuna cewa wannan mataki ya biyo bayan tashi da farashin danyen mai a kasuwar duniya.

Attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote
Attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote. Hoto: Dangote Industries|Getty Images
Source: UGC

Vanguard ta ce hukumar kula da harkokin kasuwar man fetur ta tabbatar da cewa kasuwar cikin gida za ta ci gaba da nuna sauye-sauye bisa ga yadda kasuwannin duniya ke tafiya.

Kara karanta wannan

Kwale kwale ya kife da mutanen da ke tserewa harin 'yan bindiga a Sokoto

Wannan ya nuna cewa farashin man fetur na iya yin tashin gwauron zabo idan yanayin ya ci gaba.

Masana harkar mai sun bayyana cewa sauyin farashin ba zai tsaya ga farashin rumbun ajiya kadai ba, domin ana sa ran nan gaba kadan hakan zai shafi gidajen mai kai tsaye.

Su Dangote sun sauya farashin fetur

Kamfanonin da abin ya shafa sun hada da matatar Dangote, Aiteo da AA Rano wadanda a baya suka rika sayar da lita a kan N821.

Amma yanzu sun koma kan N823 saboda hauhawar farashin gangar danyen mai daga $65 zuwa $67 a kasuwar duniya.

Wannan karin ya bayyana ne a karshen makon da ya wuce, kuma ana sa ran zai iya ci gaba idan farashin danyen mai bai tsaya ba.

Tasirin sauyin farashin man a kasuwa

A cewar wani shugaba a harkokin mai, Olajide Jeremiah, sauyin farashin ya samo asali ne daga gasa tsakanin kamfanonin man fetur da kuma yanayin kasuwar duniya.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Mutane 17 yan gidan sarauta sun fara neman karagar Sarki bayan ya rasu

Ya ce:

“Kasuwar za ta ci gaba da fuskantar daidaito a farashi idan aka samu sauye-sauye a kasuwar duniya. Haka kuma ana sa ran karin zai shafi farashin gidajen mai nan gaba kadan.”

Matsayar masu gidan mai kan lamarin

Shugaban kungiyar masu gidajen mai na kasa, PETROAN, Billy Gillis-Harry, ya bayyana cewa farashin mai a duniya na iya shafar kasuwar cikin gida.

Ya kara da cewa dole ne a kara tabbatar da wadatar mai tare da mayar da matatun gwamnati hannun 'yan kasuwa masu zaman kansu.

Matatar Dangote ta sanar da cewa tana shirin kara karfin tace mai daga ganga 650,000 a rana zuwa ganga 700,000 a rana, karin da ya kai 7.7%.

Hoton matatar Dangote da aka yi a jihar Legas
Hoton matatar Dangote da aka yi a jihar Legas. Hoto: Dangote Industries
Source: UGC

Za a fara hako mai a jihar Kogi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kogi ta bayyana cewa tana shirye shiryen fara hako danyen mai.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan jihar Kogi, Ahmad Usman Ododo ne ya bayyana haka bayan wata ganawa da shugabannin kamfanin NNPCL.

Gwamna Ododo ya ce jihar Kogi ta dade da gano tana da man fetur kuma nasarar hako mai zai inganta tattalin jihar da Najeriya baki daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng