NiMet Ta Yi Hasashen Ruwan Sama da Guguwa na Kwana 3 a Kano da Sassan Najeriya

NiMet Ta Yi Hasashen Ruwan Sama da Guguwa na Kwana 3 a Kano da Sassan Najeriya

  • Hukumar NiMet ta sanar da cewa daga Litinin zuwa Laraba ana sa ran ruwan sama mai ɗauke da guguwa a wasu sassan Najeriya
  • Jihohi kamar Jigawa, Zamfara, Kano, Kaduna, Bauchi, Yobe da Katsina na daga cikin wuraren da ruwan zai fara sauka tun da safe
  • Hukumar ta yi gargadin yiwuwar ambaliya a wasu jihohi tare da shawarwari ga jama’a da hukumomi su ɗauki matakan kariya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar hasashen yanayi ta kasa (NiMet) ta sanar da cewa za a samu ruwan sama tare da guguwa a sassa daban-daban na Najeriya daga ranar Litinin zuwa ranar Laraba mai zuwa.

NiMet ta bayyana cewa tun daga safiyar Litinin, za a fara ganin ruwan sama mai ɗauke da guguwa a wasu jihohi na Arewa, sannan daga baya ruwan ya bazu zuwa sauran sassa na ƙasa.

Kara karanta wannan

‘Ku ƙaura,’ Gwamnati ta gargaɗi mazauna Gombe da jihohi 6 kan mummunar ambaliya

Mutane suna tafiya a abubuwan hawa yayin da ake ruwa.
Mutane suna tafiya a abubuwan hawa yayin da ake ruwa. Hoto: Getty Images
Source: UGC

A sakon da ta wallafa a shafinta na X, hukumar ta ce hasashen ya shafi jihohin Arewa da Kudancin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga haka, hukumar ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar ambaliyar ruwa musamman a wasu jihohin Arewa.

Bugu da ƙari, NiMet ta bayar da shawarwari ga al’umma da hukumomi su dauki matakan kariya daga illolin ruwan sama da guguwar da za ta biyo baya.

Jihohin da ruwan saman zai shafa

A cewar NiMet, daga safiyar Litinin za a samu guguwa mai ɗauke da ruwan sama a jihohin Jigawa, Zamfara, Kano, Kaduna, Bauchi, Yobe da Katsina.

Jaridar Business Day ta wallafa cewa bayan haka, hukumar ta ce ruwan zai bazu zuwa Kebbi, Adamawa da Taraba da rana.

Hukumar ta yi gargadin cewa jihohin Bauchi, Jigawa, Katsina, Kaduna da Kano na cikin wuraren da ake iya fuskantar ambaliya.

A Niger, Benue, FCT, Plateau da Nasarawa, NiMet ta ce za a fara da hadari da ruwan sama matsakaici, duk da haka, ta ce akwai fargabar ambaliya a wasu sassan Plateau.

Kara karanta wannan

'An bar Arewa a baya,' Remi Tinubu za ta bude kamfani a Legas, an fara korafi

Hasashen yanayi a Kudancin Najeriya

A Kudu, ana sa ran samun ruwan sama matsakaici a jihohin Ondo, Imo, Abia, Enugu, Ebonyi, Anambra, Edo, Delta, Bayelsa, Rivers, Cross River da Akwa Ibom.

Rahotanni sun bayyana cewa ana hasashen ruwan zai fara da safe sannan zai karu da rana zuwa yamma.

Hasashen yanayi a sauran kwanaki

Hukumar hasashen yanayin ta ce ranar Talata Arewa za ta fara da hasken rana mai ɗan haɗe da gajimare.

Sai dai ta ce ruwan sama da guguwa za su ci gaba a sassan Adamawa, Taraba da jihohin da ke makwabtaka da su.

A ranar Laraba, wasu jihohin Arewa ta Yamma za su fara da rana, daga baya kuma a samu ruwan sama mai ɗauke da guguwa.

Arewa ta Tsakiya za ta kasance da gajimare da ruwan sama matsakaici, yayin da Kudancin ƙasar, musamman Ebonyi, Akwa Ibom, Rivers da Cross River za su fuskanci ruwan sama tun da safe.

Kara karanta wannan

NEMA ta nemi 'yan jihohin Arewa 3 su kaura kan fargabar mummunar ambaliya

Gargadin hukumar NiMet ga jama’a

NiMet ta yi gargadi ga jama’a musamman mazauna wuraren da ake fama da ambaliya su ɗauki matakan gaggawa.

Ta bukaci jama'a su guji yin tuki a lokacin ruwan sama mai ƙarfi, su kwashe kayan da iska za ta iya jefawa ruwa.

Yanayin sararin samaniya yayin da ake tsawa.
Yanayin sararin samaniya yayin da ake tsawa. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Hukumar ta kuma ba da shawarar a cire na’urorin lantarki daga wuta yayin guguwar, sannan a guji neman mafaka a ƙarƙashin manyan bishiyoyi.

Haka kuma ta bukaci kamfanonin jiragen sama su karɓi rahotannin yanayi na filayen sauka da tashin jirage don tabbatar da tsaron fasinjoji.

NiMet ta yi hasashen ambaliya a jihohi

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar hasashen yanayi ta kasa, NiMet ta ce za a iya samun ambaliyar ruwa a jihohi uku.

Rahoton Legit Hausa ya nuna cewa hukumar ta ce akwai fargabar ambaliya a jihohin Kebbi, Kwara da Neja.

Ta bayyana cewa ana fargabar ambaliyar ne saboda kusancin su da kogin Niger da kuma hasashen kwararar ruwa daga kasar Benin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng